← Book details Auren Raba Gardama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 9

Sashe 2

Auren Raba Gardama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sister Sai ina haka, d'ago da kanta tayi a ta'kaice tace shopping,

To waye zai kaiki?

Driver,
To why not kizomuje ni inkaiki tunda kinga dama fita zanyi,
no Kabarshi kawai,

Haba dai sister guda zata fita inkasa kaita please kizo muje,

Mamakinsa ne yakamata ganin yadda yake ro'konta yakai ta unguwa,
Kawar da tunanin tayi tace OK to bara Siyama tafito........
Bata 'karasa ba saiga siyamar tafito,

Park yakaisu suka sha ice cream, Sai faman janta wasa yake a 'kokarinsa nason cusa kansa,

Sunje shopping mall tayi siyayya itama siyam tad'au abunda takeso, duk zubair ne yayita biya,

Basu dawo gida ba Sai guraren magrib, dan haka nema bai shiga dasu ba, ya ajesu a bakin gate,

Dan yanaso yatsaya masallaci, Siyama ce ta kwaso musu kayan ,

Itakuwa wata yr leda kawai tari'ko wacce chocolate ce acikinta,

Tura 'karamar 'kofar gate d'in tayi kanta a 'kasa,

Daidai lokacin zaifita zuwa masallaci, yana gyara hannun rigarsa da ya nad'e dazaiyi al'wala,

Aikuwa karo sukayi wanda yasa ta kusa fad'uwa sabida takalmanta, da suka lan'kwashe,

Baya tayi zata fad'i da azama ya kamota madadin ta fad'i Sai tafad'a a hannunsa,

Idanuwanta a rufe dn tad'auka tafad'i jin ta jingina da abune yasa tabud'e idonta,

Ganin mutumin da takejin haushinsa tun ranarda tadawo ne yasa tayi saurin bari hannunsa,

Had'i da nunasa da d'an yatsa,

Kai baka da hankaline zaka fito baka sanin inda kake saka 'kafarka tsabar dabbanci,

Mts next time kasake bari mukayi,kwatankwacin wannan had'uwar,

Saida takad'a yn yatsunta sukai 'kara tace Sai nayi sanadin barinka gidannan,

U trashed

A zafafe tawuce cikin gidan,ko ledarta bata tsaya d'auka ba Sai Siyama ce tad'auka, wacce duk abunda yafaru gaban idonta,

Tunda tafara magana yake kallonta yana mamakin yadda ta ta'kar 'kare tana masa rashin kunya,

Kayi ha'kuri yaseer...

Maganar Siyama ce ta dawo dashi daga tunanin d yake, girgiza kai kawai yayi yafita,

Jin anyi ruku'i

M&Z
[18/01, 22:53] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕AUREN RABA
GARDAMA🌕🌕

Na

MAMUH GEE🌕
And
ZINNIE SMART👌

_Bismillahi'rahmanirraheem_

16~20

Tana shiga d'aki tashiga cire kayanta, towel tad'auka had'i da fad'awa bathroom,

Dan acewarta yau dole ta dirji jikinta kodan wannan matsiyacin da yatabata,

Al'wala tad'auro bayan tayi wankan, tana fitowa ta janyo wata doguwar Riga tasaka, sannan ta shimfid'a prayer Mart ta kabbarta sallah,

Bayan ta sallame tayi azkar d'inta,
Saime kawai hoton abunda yafaru d'azunne yari'ka dawo mata,

Wani irin haushinsa d tsanarsa taji, mts tasaki tsaki dn bata son take tunanin useless man d'innan kamar yadda tarad'a masa suna,

Wayarta ce tayi 'kara dubawa tayi dn taga waye mai kiran,
New number tagani,tsaki takoma ja dn ita ba kasafai take son kira da new number ba,

Cigaba akayi da kira saida takusa katsewa sannan tad'auka had'i da cewa,
Hello who is on the line,
Sister taji anfad'a Wanda koba a fad'amata ba tasan shine dn muryarsa da taji,

A ranta tace nifa bnka number naba dnka ri'ka disturbing d'ina ba.............

Maganarsace takatseta
Hello ar u there
Inaji tafad'a a ta'kaice

Am sorry sister natakuraki ko?am really sorry, please,
Dama kira nayi inmiki ya gajiyar fita dn nasan 'kanwar tawa yr hutu ce,

Yadda yayi maganar da zolaya yasa tasaki yr siririyar dariya,had'i da fad'in haba dai yayah zubair,

Ai banyi fitar da zangaji ba d'an zoo road d'in da mukaje??
Ke sister kifad'i gskya kedai kind'an gaji badai da yawa bako??

Dariya tasaki sossai,

Haka sukaci gaba da fira sai janta da surutu yake,

A nufinsa na 'ko'karin cusa kansa gurinta tayadda yakeso tasaki jiki dashi,

Koda yatashi bayyna manufarsa bazai sha wahala ba dn shikam sonta yariga da yayi nisa tayyada bayajin kira,

*************

Haka kuwa akayi wata irin sha'kuwa ta shiga tsakanin zubair da LAILAH a inda zubair yake ganin cewa tuni laila ma ta kamu da cutar da yakamu da ita tunda dad'ewa,

Dan haka shi agurinshi time kawai yake jira yabayyanamata cewa yana sonta

Wanda a ganinsa, itama shi take jira,

Wanda,a 'bangaren laila kwata kwata batamasan wainar da yake toyawa ba,

Dan ita duk abunda ke gudana a tsakaninsu tana kallonsa ne amatsayin yan uwantaka,

Kuma da kowani d'an uwanta zata iya haka shima dalilin da tasa sha'kuwar tafi yawa sabida yana yawan kulawa da ita wanda ba yayiwa yn uwansa,

Sai ta d'auki hakan akan Allah ne yahad'a jininsu,

WANNAN KENAN

************

Yau takama juma'a rana ce da TSOHO yaware domin ganawa da iyalansa baki d'aya,

Bayan ansauko juma'a ne kowwa yanufi sashin tsoho dn sunsan da zaman wannan 'ka'idar,

Kowwa ya hallara mata gurin zamansu daban haka mazan kuma acikin wannan babban falon nasa,

Ake kan kawo abinci da drink's kala2 kowwa yaci ya 'koshi mai abun fad'a yafad'a ko shawara ko 'korafi kodai wata damuwa,

To yauma hakan takasance bayan anci abinci an'koshi,tsoho ne yabude guri d addu'a,

Sannan yayi musu nasiha kamar yadda yasaba,

Nan yabada dama d'aya bayan d'aya kowwa yafad'i abunda ke ransa,

Bayan angamane yace to,

Saura yn mazan yayanku da ynmata dan haka ina so kowwa acikinku yafito da matar aure,

Kuma haka yanuna bangaren da su Laila suke yace duk aurar daku za'ayi,

Nagaji da ganinku kunzama tuzurai tunba mazan ba,

Dariya zubair yayi yace tsoho kwantar da hankalinka nikam nasamu mata saidai ko jabeer, yafad'a yanawa jabeer d'in dariya,

Amma ni dama lokaci nake jira amma mata kam ai tanann nasamu,

Ya'karasa zancen nasa yana kallon Laila wacce akayi sa'a itanma shi takallah,

Wani kallo taga yasakarmata wanda takasa tantance na meye ??kuma ma me hakan ke nufi??

Kai itafa takasa gane kan yaya zubair kwanann wasu irin abubuwa yakemata dayake d'aure kanta to me yake nufi???

Tunanin tane ya tsaya lokacin dataji jabeer nafad'in to ai nima nasamu mata jira nake musasanta kan infad'a,

Dariya tsoho yasaki da iyayensu kowa dariya yayi,tsoho yace,

Ja'iran yara dama jira kuke inyi magana ko to nayi,

To masha'Allah,tunda yn mazan sunsamu mata tofa kuma ynmata kuyi 'ko'kari kufito da mazaje,

Daga haka taron ya watse kasancewar ankira sallar la'asar,

M&Z
[18/01, 22:54] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕

Na

MAMUH GEEE🌕
And

ZINNIE SMART

21~25

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.

Wani irin iska ake kadawa mai dadi Wanda yake hankado labulen windon dakinta yana dukan fuskarta dake kwance kan lallausan pillow dinta.

Jan numfashi tayi a hankali sbd yanayin ya tuna mata da America sosai
Hardai idan tana tareda mate dinta salman Wanda suka rabu suna tsaka dajin dadinsu,,
Mikewa tayi ahankali tazo bakin qaton window din ta tsaya tareda lumshe idanunta iskan na saukar mata ahankali.

I really missed you my salman,
Da nasan maganan aure za'ayimin daban yarda ko kadan nadawoba sbd am not ready for it.,
And I promised you Dana dawo zan cigaba da karatu na anan but I don't know wat came over me...
I dnt knw if I can do this without you but I promise I will try.

Tsaye yake bakin window din dakinsa na bakin gate din gidan yana waya.

Ahankali ta bude idanunta dake lumshe sbd wani irin sanyi dake shigarta sakamakon lovely voice din datake jiyowa tana watsa american English a nutse.,dadi da qari kuma kamar muryan salman dinta.

Alokaci daya idanunwansu suka sauka akan juna,
Ba qaramin mamaki tayiba data ga shine maiyin wannan turanci Wanda zatace yadama ya shanye.

Dauke kansa yayi tareda janyewa daga jikin windon sbd yanayi kayan dake jikinta dan kuwa handless vest ce ajikinta da gajeran wando.

Numfashi tasauke ahankali tareda jingina jikin window sakamakon mutuwa da jikinta yayi..
She just don't know why but sumtin is telling her that sumtin is not right.

Wayarta ta daga ta danna kiran salman ko zataji daidai.

*****************
Fira take da daddynta akan zataje Kaduna gurin kakarta ta gurin mamanta saiga jabeer yashigo palon da sallama.

Dad da Anty basma ne kadai suka amsa ita kuwa dauke kai tayi sbd Sam bata wani shiri da jabeer din dan girman kansa.

Daddy dama Kaduna zani nadawo gobe shine nace bara naxo nayi muku bankwana.

Alhmdulillh kaga kuwa saika tafi da lailah dan yanzuma muke maganar tanaso taje Kaduna gurin hajiya babba.
Kaje da ita goben idan kagama aikinka saika biya ka daukota kudawo ko.
To. Yace yana kallon gefen datake zaune.
Badan tasoba ta miqe ta shiryo.

A hanya tayi mamaki sosai na yanda ya taqarqare yaringa janta da fira.

Sama sama take amsa masa harsuka isa Kaduna.

Da gudunta ta fada jikin tsohuwar tana dariya
Itama dariyar take dan kuwa ba qaramin farinciki tayiba da ganin jikar tata.

Tareda jabeer sukaci abinci dare agidan dan bai bar gidanba sai dare sosai bayan sunsha fira da tsohuwa.

Washe gari sai yamma suka baro Kaduna ana kiran magriba suka iso abuja.

Salloli tayi bayan tayi wanka kai tsaye bangaren tsoho ta nufa

Zaune suke su biyu kadai apalon kan babbar darduma dake shimfide a palon sunacin abinci.

Ruwan black tea yake kurba ahankali cikin kwarewa da iya shansu dan har wani lumshe ido yakeyi.

Maida kallonta tayi ga tsoho taga shi fruit yake ci ahankali.

Siririn tsaki taja Wanda yasa suka lura da shigowarta amma duk da hakashi bai dagoba sbd wani iron masifaffen miskilanci dake cinsa.

Alh tsoho hidima kake haka abun ko gayyata.

Azumi nakeyi duk ranar litinin hakama yaseer shiyasa duk ranar nake gayyatarsa musha ruwa tare.

Ok, tace tana yamutsa fuska dan tuni ta fasa zama ta juyawarta.

*********
Yau tacika wata biyu da dawowa kuma yau ne zata fara zuwa school sbd qarasa karatunta na degree da bata qarasaba acan.

Ado taci na musamman sai zuba qamshi take
Hanbag da wayarta ta dauka ta sauko Palo.

A dining ta Tatar dasu dad dinta tuni taja kujera tazauna tana cewa,
Gud morning papa.

Lailan dady kin tashi lpia?

Lpia klau dad.

OK my girl kinga yau zaki fara zuwa school so be very careful sbd nan da america is not dsame so be smart and intelligence.

Don't worry dad I can handle it.

Kallon Anty basma tayi tace,
Ina kwana Anty.

Lpia klau yar daddy nima INA Jan kunnenki daki lura sosai a school din.

OK, tace tana mikewa cikin sbd tafara latti.

Key dad ya miko mata
Da sauri ta karba cikin murna tace,
I love you dad and thank u so much.
Chapter 2 · 0% Book details