← Book details Auren Raba Gardama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 9

Sashe 5

Auren Raba Gardama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nutsuwa yashigo palon tuni qamshinsa yacika palon,abinda yakeba kowa mamaki da yaseer din shine fitinannan qamshinsa da Kwarjininsa.

Dauke kai tayi tana 6ata fuska.

Shikuwa gaida dady yayi cikin girmamawa.

Lpia kalau yaseer,
Bismillah zauna muyi breakfast.

Ba musu yaja kujera cikin wayewa ya zauna tareda gaida Anty basma.

Cikin salon yaudara yace,
Lailah kintashi lpia?

Sosai ita kanta tayi mamaki sbd tafi kowa sanin girman kansa duk da yana maigadi.

Murmushin jin dadi dady ya yana cewa,
Lailah kece yakamata ki gaidasa bashi yakamata ya gaidakiba.

Toh. Kawai tace tana turo baki.

Coffee ya kur6a yana wani irin murmushin qeta.
Sbd yasan duk wannan iskancin takusa dainasa.

Dady dan Allah kaje dani naganosu mum dasu afra nayi missing dinsu sosai kuma banaso tasan da wani zancen aure sbd ranta zai 6aci.

Miqewa dad yayi yana cewa,
Baxaki ko inaba sbd yawo baikacekiba yanxu
Kaikuma yaseer mutafi ko.

Kallon Anty basma tayi alamar tambaya.
Antyn tayi saurin cewa,
Yes tareda yaseer zashi Lagos sbd yanaso yafara koya masa business.

Dan qaramin tsaki taja kafin ta miqe tayi hanyar hayewa stairs tana cewa,
Nidai dady bara na shiryo kobaka tafi dani America ba saiku barni Kaduna nayiwa hajiya babba kwana biyu.

Kallon yaseer dady yayi zaiyi magana
Yaseer yayi saurin cewa,
Ba komai zata iya zuwa idan nadawo daga Lagos saina biya nataho da ita.
To shikenan tunda ka amince.

Motar dady suka tafi da ita Kuma yaseer ne ke tuqin
Lailah na gefensa dady na baya.

Suna isa Kaduna kai tsaye gidan haj babba suka nufa.
Suna pakawa maigadi yataso da sauri yana musu barka da zuwa kafin yasanar dasu yau dinnan hajiya babba tayi tafiya gidan bakowa arufe yake.

Shiru dady yayi kafin yace,
Lailah kinga rashin jinki abinda yaja tunda dakinyi zamanki dashikenan gashi yanxu bamusan yazamuyi dakeba kuma lokacin tashin flight dinmu yakusa.

Yi hakuri dady bansan bazamu sameta bane.,amma ai ba matsala muje airport din Ku wuce zan iya kai kaina abuja tunda ba dare neba.
Wat". Kina tunani xanbarki kija mota ke kadai daganan har abuja.
Daddy Allah zan I......
Just shutup lailah.

Yaseer muje airport pls kafin murasa flight.

Suna isa yaseer yafice motar yanajin takaicin lailah sbd tanason 6ata masa plans dan yaso ya huta a Lagos din idan dady ya wuce,afterall yaso ya gana da wasu baqinsa daya bawa appointmnt.

Ticket yasiyo guda uku yadawo tareda Wanda zai karbi motarsu ya aje.
Kallonsa dady yayi yace,
Yaseer yakuma haka naganka da tickets kuma harguda uku.
Zaiyi magana aka fara sanarwar passengers na girjin Lagos su hanzarto.

Murna tafarayi dan tasan shikenan dady zatabi america dasunje lagos din.
Qudurtawa tayi idan tasamu ta tafi ba Inda zata dawo.

Mamuh & zinnie
[18/01, 22:55] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕

Na

MAMUH GEEE🌕
And

ZINNIE SMART

56~60

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.

Yaseer ina tsananin jin kunyar cewama kayi hkr sbd yau 'da ne ka haifesa amma baka haifi halinsaba,
Nayi baqin cikin ganin abinda lailah tayimaka yanxu a bainar jama'a,
Haka zalika tun ba yauba ina lure da sane da rashin mutuncin datake tafka maka.

Qara kallon yaseer din yayi cikin wani nazari daya shigesa yanxun yace,

Yaseer kadaka damu insha Allah zanyi maganin abin nasan matakin dazan 'dauka.

Cikin qoqarin danne 6acin ransa yace,
Alh basai ka mata komaiba sbd ni ban dauki abin da mahimmanciba.

Girgiza kai yayi cikin qara tabbatar da tunanin da yayi ya wuce.

Cikin tsananin 6acin rai da wani irin tiririn zuciya ya shige dakinsa na gate din yana fidda wani irin huci.

Rigarsa ya farke daga jikinsa yayi wurgi da ita tareda kaiwa bango duka,
Duk baimasaba saida yasa qafa yayi ball da laptop dinsa dake charging.

I hate her,
I hate her so very much,
I despise her,
Infact I hate this house and every one in it.

Wayarsa yaciro yana huci ya danna kira.
Ringing biyu aka dauka tareda cewa,
Barka da yini sir.

Bar tsaya amsawaba yace,
Lawal ka sanar da isowata office gobe sbd na rufe case din binciken alh naseer modibo,
Sannan kayimin booking ticket gobe zan wuce Miami.

Cikin son cika umarnin ogansa yace,
Yes sir but.....
No buts just did wat I said.
OK sir.

Wurgi yayi da wayar tareda fadawa toilet din dakinsa.

******************

WASHE GARI

Qarfe goma za'a daura aure dan haka tuni gida ya kaure da hayaniyar jama'a.
Kowa ka gani ya shirya sai shirin daura aure ake.

Qarfe Tara da Rabi kowa ya shirya banda lailah dan har lokacin barci take bata tashiba
Hattasu maryam da siyama harda amarya ayshat sungama shiryawa cikin ado na musamman.

Anty kubra ce tashigo dakin da kaya a hannunta tana cewa,
A'a maryam harkun shirya Baku tada mutuniyar takuba ta shiryaba har an fara daurin auren.

Janye bargon da lailar ke ciki tayi tana cewa,
Daughter maza tashi kiyi wanka ga kaya na musamman nakawo miki.

Tashi tayi tana duba agogo kafin ta kalli su siyama dake faman daura dankwali ayshat kuwa turare take fesawa taci ado sai qyallin amare takeyi.

Lallaima 'yan Matan nan shine kuka shirya Baku tadani ba.
Tura toilet Anty tayi tana cewa,
Bari anjima kya musu wannan.

Tana fitowa wanka tahau shiri.
Dark blue lace ne Anty basma takawo mata Wanda daddynta ya siyo matasu cikin tsadadden lefen dayayo mata kasancewar alh tsoho ya sanar dashi wazai aura mata.

Mai makeup na gama mata makeup ta suka sauko qasa gaba dayansu.

Palon cike yake da mutane anata hidima.

A gurin daurin aure kuwa ba qaramin tashin hankali da mamaki jama'a sukayiba jin an daura auren LAILAH ALI MODIBO da YASEER.
Iya kaduwa su zubair da jabeer sun shiga sai dai sunsan akwai rigima da tashin hankali gurin lailah.

Ana gamawa batareda kowa yashigo gidanba aka 'dunguma zuwa gurin 'dauro nasu jabeer da zubair gidan matayensu.

Ana watsewa bilal yakirata yace,
Bby gani nazo daurin aure amma ba kowa har an watse inaga nayi latti.
Ok Ai ba damuwa bari nazo ko fira muyi kaga adon danayi.

Ko gyale bata yafaba sbd rigar jikinta fitted gown ce data kar6i jikinta ta zauna mata sosai gashi rigar Nada tsawo sosai amma heels din qafarta sun taimaka gurin rage tsawon rigar.

Tun daga nesa ya kafeta da ido yana hade yawu da qyar yana ayyana kota halin qaqa sai ya mallaki lailarsa.

You luk fabulous.
Thank you my.....
Bata qarasaba taji qarar wurgi da kaya tareda wani irin hucin 6acin rai mara misaltuwa na tasowa daga 'dakin yaseer.

Gabantane ya buga da qarfi haka kawai amma saita daure zata kuma magana motocinsu dadynta dasu alh tsoho dasu abbah tareda angwaye suka parker.

Qarar lasifikar maroqi ce tasayi firgifit amma ga babban tashin hankalinta saita taji yana fadin,

Yau dai min shaida 'daurin auren 'yayan gata da aka 'daura na,
JABEER DA SALMA,,,
ZUBAIR DA KHULSUM,,,
AYSHATU DA ANGONTA AHMAD,, SAINA GIMBIYA LAILAH ALI MODIBO DA ANGONTA YASEER.

Kasa tantance mezatayi tayi saita qurawa daddynta ido don son tabbatarda abinda taji..
Sunkuyar da kai yayi cikin jin wani irin yanayin tausaya mata.
Yanayinsa ya tabbatar mata da hakan gaskiyane.

Juyawa tayi gurin alh tsoho ta 'daga hannu ta.........

M & Z
[18/01, 22:55] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕

Na

MAMUH GEEE🌕
And

ZINNIE SMART

46~50

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.

Tsit palon yayi bakajin motsin komai sai kukan a.c dake tashi ahankali.

Batareda tsohon ya dagoba yace,

Ayshat jeki ki kiramin lailah.

Miqewa tayi jiki a sanyaye tafice.

Minti uku saigata sundawo tareda lailah.,
Zama sukayi
ayshat a qasa ta zauna
Ita kuwa lailah kusada antynta basma ta zauna.

Rai a tsananin 6ace yafara fadin,

Yau koma bayar takai acikin zuriar nan ana fada harda duka,
Kuma qarin abin haushin harda Ku manyansu duk akan dalili daya.

Nayi baqin ciki sosai akan wannan sabon alamari,
To yau zanyi maganin wannan matsalar
Ke lailah inaso ki zabi daya daga cikinsu yanxu anan gurin.

6ata fuska tayi tareda turo baki tace,

Nifa gaskia banda time din wani soyayya ko aure dan haka ba Wanda nakeso acikinsu.

Umman zubair tayi saurin katseta da cewa,
Lailah kidaina fadar haka mana ki duba kiga yanda zubair ke....

Kunji tsiyar ai
Sbd ke kullum hafsatu ke kike kawo matsalar....

Abba nasir ne ya katsesu cikin 6acin rai yana cewa,

Ku kunzama mutanen banza tunda bazaku iya hana 'yayanku ba sai dai kuma ku hau naku abin kunyar.

6acin ran alh tsoho ya qaru iya matuka ya miqe tsaye tareda basu baya ya fara magana cikin kakkausar murya.

KE LAILAH nabaki nanda sati daya ki fitar da daya daga cikinsu su biyu idan ba hakaba wani satin nakuma zagayowa zan raba gardama na aurar dake ga duk Wanda naga dama.
Yana gama fadar haka yashigewarsa dakinsa yabar baya da qura.

What"
Tace da qarfi cikin rawar murya kafin ta kalli Anty basma cikin wani irin yanayi.

Saurin kama hannun lailar tayi suka bar palon.
Da dai dai suka bar palon cikin zullumin ya zata kaya.

Suna shiga Palo tayi wurgi da wayarta a kujera tana wani fidda numfashi.
Dafata Anty basma tayi tace,

Lailah pls take it easy komai zaiyi daidai.

Anty kinajin abinda tsohon nan yafada,
Wlh ni banason kowa acikinsu in fact ni ban tashi wani aure ba,
Danasan wannan shirmen zan tarar a Nigeria daban dawoba.

Da qarfi ta kwala kiran safiya mai aikinsu
Aiko da sauri tazo dan tasan abu kadan ke hasalta lailar.

Bani ruwa mai sanyi yanxun nan.
To,, tace tareda juyawa da sauri. Lailah Waya ta dauka ta danna kiran daddynta Yana dauka ta fashe masa da kukan shagwaba tana koro masa bayani.

Lallashinta yahauyi tareda tabbatar mata da yananan dawowa jibi.

Suna gamawa ta kira mum dinta itama tana dauka ta fara zuba mata abinda ke faruwa..

Lailahna kwantar da hankalinki ba abinda zai yiyu bane yi miki auren dole,so jst calm ur self okey my love.

Nidai mum dan Allah kizo idan bakaba da dad yadawo zan tahowata america.

Kadaki damu my girl dazarar dad dinki yadawo baice komaiba zanzo nataho dake.
OK mum I love you.
I love u too my girl.

***********
Kwana biyu kenan da faruwar abin Sam lailah bata ko fitowa Palo sbd bata buqatar ganin kowa abincinta ma saidai safiya takawo mata daki.
Chapter 5 · 0% Book details