← Book details Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 14

Sashe 6

Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sauri Abdul_maleeq ya fiddo wayarshi da take cikin pocket din shi, ya fara kiran Number Yaaa Shehi, kira daya ,biyu, a na ukkun Shehi Arman ya dauki Wayarshi, a hankali ya dan yi jim kafin yy Sallama.

bai amsa Sallamar cikin ba, a ruɗe Abdul_maleeq ya fara magana cikin ruɗu ya ce "Yaaa Shehi Zayn! Zayn!! Zayn_maleeq Yaa shehi ", ya fada kamar zai yi kuka,cikin rashin fahimta yace "mai yake damunsa ...?", cikin sauri yace '" gamu a part din Jadda baya hayyacinshi, wani abu yake makamar wanda zai mutu, Yaaa Shehi ka taho", ya fada cikin wani yana yi.

cikin sauri Yaaa Shehi ya fara daga ƙafarshi zuwa sashen Jadda, yana zuwa ya samesu, suna kan Zayn_maleeq Jadda kuwa tana zaune kan kujerarta . sai tauba chewing gum take kamar wata budurwa, da sauri Sayyid ya nufeshi yana cewa "Abin ci Jadda ta bashi yana cikin ci ya fara haka", ya fada yana nuna shi.

kallon Jadda da take zaune yy, wadda ganinshi yy mugu-mugun razanata,nunawa ne kawai bata yi ba .

takawa ya fara yi zuwa gareta, da sauri ta miƙe , tana jin wani futsari na ƙulle mararta, tana tafiya yana bin bayanta, har sai da ta kai karshe gurin bango, ta fara zazzare idanu take.

idannunshi da suka yu jaaazir tsabar ɓacin rai ya watsasu akan fuskarta, cikin wata kakkasar murya yace "ke..! , ke !!, ke!!! ki roƙi Allsh kar wani abu mummuna ya faru da Zayn, in kuwa ya faru da shi uhmmmm...", cije lips dinshi na ƙasa yy da karfi Alamar, koma mai zai aika ba zai mata kyau ba, sosai ta tsorata wanda tsoratar tayi sanadiyar zubowar Futsari daga mararta..

Wannan littafin na kuɗi, game buƙata ya tuntuɓi number ta kamar haka .

07033371851.

DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼

*DAGA ALƘALAMIN*

ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️.

SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA,SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR🌹🌹
)

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

*P. 5*

Hannunshi ya juya mata, kafin ya juya gurin Ƙannanshi, idanunshi jaaazir, Umarni yy musu da su daukeshi, Part dinshi, suka nufa da shi.

Kan kujera suka ajiyeshi, Umarni ya ƙara musu da su dauko mishi Madara peak da cup a fridge, da sauri suka dauko suka dawo, karɓar madarar yy,ya ɓula bakinta da Key din mota , gaba daya madarar ya juye cikin cup din, Sayyid-maleeq ya kalla kafin yace "Zuma and Spoon", ya fada yana daura tafin hannunshi a goshin Zayn_maleeq , da ta dauki wani mugun zafi sosai.

da sauri Sayyid ya je yy abun da Shehi ya Umarceshi da yy, bayan ya kawo ya haɗa Zumar, ya jujjuya , tare da tallafar kan Zayn ya fara zuba mishi haɗaɗɗiyar madarar da Zuma , a bakinshi cikin ikon Allah yake shiga cikinshi, har ya shanye tasss.

tafin hannunshi, ya kama ya matsa, zazzafan numfashi ya sauke, tare da ƙaƙarin Amai, dagoshi Shehi yy ya ƙarashi da jikinshi,amai ya shiga kwararawa baƙiƙƙirin .

shafa mishi bayanshi ya shiga yi , yana fesar da iska mai zafi, sai da Zayn ya amai gaba daya abun da ya ci kafin ya koma jikin Shehi, yana sauke numfashi, cikin kakkausar murya da gargadi yace "kai kunnen kashe ne da kai ko ??,ba na haneka da karɓar wani abu ba hannun yan cikin masarautar nan?,ka ci gaba da shishige musu kana karɓar abu a hannunsu kana ci, ba mutuwa ake tsoro ba wahalar da zaka sha ita de abun gudu", dafe kanshi yy yana jin yana wani mugun sara mishi.

zameshi yy daga jikinshi ya wucewarshi Upstairs. dai-dai nan Umma Jakadiya ta shigo palon a tsorace, da sauri ta isa gurin Zayn , tana tattaɓashi a firgice take cewa "fatan dai bb abun da ya sameke ko ?" ta fada a firgice, idanunshi da suka kasance irin na Shehi ya dan bude tare da yin luuuu da su irin dai yarda Shehi yake yi, idan baya son hayaniya ko baya jin dadi.

taɓa wuyanshi yy, jikinshi bb zafi, numfashi ta sauke tare da cewa "Alhamdulillah", kallon Sayyid da Abdul tayi, tace "ku kamashi ku kai shi Bedroom ya kwanta, ya huta, kafin na sama mishi abin da zai ci", ta fada tana miƙewa.

Yaa Shehi na shiga bedroom dinshi, ya kwanta kan bed, yana sauke wani wahalalan numfashi,cikin rashin yake ayyana tunda sun gama abun da ya kawosu garin dole su tattara su barshi, kafin ayi Sanadiyar rai abu mafi soyuwa a gareshi.

zazzafan numfashi ya sauke yana jin wani zafi tun daga cikin jikinshi, har saman gashin kanshi,a hankali ya miƙe ya zare Alƙyabbar jikinshi, ya zame rawanin kanshi ya ajiye akan bed din, tare sa nufar bathroom, tsakiyar shower ya tsaya, tare da kunnawa.

ruwan sanyi ne ya fara dukan kanshi, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tura yatsun hannunshi tsakiyar kanshu, yana barbaza gashin kanshi . ta yarda ruwan ya ke shiga dukkan jikinshi.

sai da ya tabbatar da cewar zafin ranshi, har ma da zafin jikimshi yy ƙasa kafin ya fito kashe shower din, ƙaramin towel ya daura a kanshi, yana tsane gashin kanshi da yake lirif da ruwa,a hankali yake takowa . sai da ya zo gurin ƙofa kafin ya zare lallausa kuma tattausar ƙafarshi daga cikin bathroom slippers din, bude kofar yy ya fito, yana fitowa ya daura ƙafarshi akan welcome carpet da yake shimfiɗe a ƙofar fitowa bathroom din.

da Sunan Allah ya fito ya fara shiryawa cikin Arebiyan Jallabiya Back mai kyan gaske, gaban dressing mirror ya tsaya, hand dryer, ya fara busar da gashin kanshi, da har rufe mishi fuska yake, tsabar yawa da sulɓi, a hankali ya tattare gashin ya mayar da shi baya , yana fesar da sanyayyar ajiyar zuciya, turarenshi na Huge boss ya dauka, ga fara feshe jikinshi da shi.

har sai da ya fara hawar mishi kai kafin ya ajiyeshi, yana juyawa daga gaban mirror, gurin Pray mat ya matsa, tare da zama, ya tankwashe ƙafafunshi , Al-qur'ani ya dauka ya fara karantawa.

Yaa Shehi bai fito ba sai gabanin Magrib, a hankali ya fara saukowa, wannan ƙaron yana sanye da Jallabiya Fara ƙarr sai hula fara, ƙafarshi na sanye da wasu tausasan slippers masu kyau da sukawa ƙafarshi ɗas.

A hankali yake saukowa daga Upstair yana cewa "```Allahummaj al fiy kalbiy nu`ran, wa fiylisa niy nu`ran, wafiy basari nu`ran, wamin fauki nu'ran, wamin tahti nu`ran , wa an yami`ni nu`ran , wa an shima`liy nu`ran, wa min ama`mi nuran, wa mankhalfiy, waj al fiy nafsiy nu`ran, wa aazim liy nu`ran , wa azzimliy nu`ran , waj al liy nu`ran , wa nu`ran , Allahumma aadiniy nu`ran , waj alfiy asabiy nu`ran, wafiy lahmiy nu'ran , wafiy damiy nuran , wafiy shaariy nu`ran , wafiy bashariy nu`ran```" , bai ko yi musu magana ba sai nuni da yy musu da su tashi lokacin Sallah yy.

har ya kuaa fita Umma Jakadiya tace "Yaa Shehi mai za'a haɗa maka ??.", hannu ya ɗaga mata alamar yana dawowa, Zayn_Maleeq da ya warwarw ne yace "Ummu Tuwan Shinkafa da miyar Kase", yaba fada ya bi bayan Yan uwanshu haka suka fice yana gaba suna binshi a baya, har suka ƙarasa Masjid din bb wanda yy wa wani magana.

ko da suka ƙarasa bakin Masjid din, suka yi Addu'ar shiga Masallaci, lokacin Yaah Shehi har ya shige ciki, kasantuwar lokaci ya tafi da yawa.

kafin su ƙarasa shiga cikin Masjid din har ya ƙwala kiran Sallar Magrib cikin zazzaƙar muryarshi mai dadin Sauraro , cikin yar Azama suka shiga Masjid din, suka tsaya a sahun gaba daga bayanshi.

cikin Zazzaƙar muryarshi ya fara karatun Al_qur'ani mai girma, har ya idar a cikin Suratul Ma'eedah , Ƙarin karatun da ya soma yi musu jiya yy musu ,har lokacin Sallar Isha yy , Bayan ya Jasu Jam'in Sallar Isha, suna idar wa, ya miƙe tare da yin hanyar waje, ganin hakan yasa da sauri Sayyid_Maleeq da Zayn_maleeq da Abdul_Maleeq suka biyo bayanshi.

jerawa suka yi su huɗu a bunsu suna tafiya, ko wane tasbhi yake, haka har suka ƙarasa sashen Matan Sarki da tun zuwansu basu leqa ba, sashen Babbar Matar Sarki Hajiya Lami suka fara shiga,ba laifi ta sakar musu fuska sosai, dan kusan Ƙawar Ammiensu ce kafin ta bar duniya, bayan sun gama gaisheta, suka nufi sauran sassan gidan.

duk in da suka shiga bb wani sakin fuska hakan, yasa basu wani damu ba, san sun saba da yana yon gidan Sarautar nasu,Asalin Sarautar tasu ce, amma gaba ake musu da mugun kwulli a kanta.

su basu ma damu da Sarautar ba kwata-kwata amma an damar musu rayuwarsu, hakan yasa basa jin dadin zama cikin gidan ko kaɗan, wanda har zaman Abroad ya fiye musu zaman gidan , dan ta ko wane ɓangare hari ake kawo musu, duk kuwa da cewar Sarautar ba hannunsu take ba sun riga da sun Miƙata ga Ƙanin Mahaifinsu.

daga nan Ɓangaren Sarki suka nufa, cikin sanyayyiyar muryar Shehi yy Sallama cikim palon Lamurɗe,cikinshi ne yy wani mugun murɗawa, zuciyarshi tayi wani mugun bugawa, tunaninshi ya so gushewa daga cikin jikinshi, dakyar ya tattare gaba daya natsuwarshi guri daya, har suka ƙaraso cikin palon shi bai amsa Sallamarsu ba kuma bai dauke idanunshi daga kallon da yake musu ba.

har suka ƙaraso su Zayn suka zauna ƙasa Yaa Shehi ya zauna saman kujera, amma Lamurɗe bai dauke ganinshi garesu ba, da alama ma baya cikin cikakken natsuwarshi, gyara murya Yaa Shehi yy, tare da cewa "Fatan Lafiya Abba ..?", da sauri ya dauke idanunshu daga garesu yana sakin dan ƙiƙirarran murmushi, tace "Uhmm hhhhmm lpy lau Yaa Shehi", ya fada yana dai-daita natsuwarshi.

Haɗa baki su Zayn suka yi gurin cewa "barka da dare Abba ", dan murmushin da iyakarshi laɓɓa yy tare da cewa ''barka dai Yaran Albarka", jim suka dan yi kafin Yaa Shehi yace "Uhmmm na zo faɗa maka cewar gove zamu koma", ya fada yana dan sauke numfashi. ɓoyayyiyar Ajiyar Zuciya Lamurɗe ya sauke tare da cewa "to..to...to. Madallah Allah shi kai mu goben", ya fada yana dan murmushi.
Chapter 6 · 0% Book details