← Book details Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 14

Sashe 3

Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana da siririn hanci da ya dace da kyakyawar fuskarshi, uwa uba bakinshi da Idanunshi, wanda su zaka kalla ka tabbatar da cewar ba Asalin dan ƙasar bane, sa boda yarda suke, idanunshi ba za'a kirashi da blue ba ba za'a kirasu da light blue ba sai da ace musu royal , wanda suka ƙarawa fuskarshi kyau, bakinshu kuwa dan mitsitsi mai dauke da pink lips , a hankali ya bude bakinshi, jerarrun fararen haƙoranshi farare tas masu kyau da daukar ido wanda har fuskarka kana hange ta cikinsu ne ta bude , kafin a hankali yace "Alhamdulillah", wanda na lura da cewar hakan ya riga ya zame mishi jiki, dan duk motsawar da zai yi sai ya kira sunan Allah.

Wayarshi da take ring yasa hannu ya dauja ba tare da ya duba wanda yake kiran ba, a hankali ya ƙara wayar a kunnenshi, daga chan ɓangaren aka ce "Assalamu alaika Yah Sheikh", a hankali ya Amsa Sallamar har lokacin bai shaida wanda ya kirashi ba, sai dai yana ji a jikinshi kamar ya san muryar ko kuma ya taɓa jinta a wani guri.

Cikin sauke Ajiyar zuciya Dr din yace "Ranka ya dade Yah Sheikh ", ya fada a ƙasalance yana gyara amanshu kan kujerar da yake zaune,a hankali ya furta "Uhmmm!", wanda shi din ma na lura ya zamar mishi jiki, ya fi ganewa yy hakan da yy magana.

A hankali yace " ni ne Dr din da ka bawa Marar lpy Ɗazun", a hankali yace "hope everything is fine", ya haɗa yana lumshe idanunshi da sauke numfashi, jinjina kai Dr din yy tare da cewa "to lpy ba lau ba, dan gaskiya ta samu babbar matsala ga kuma dama matsalar da take fama da ita, sai abun ya haɗu ya ƙara dagula lissafin jikinta", gyara zama yy tare da sauke numfashi, kafin yace, "ina bukatar duk wani information a kan ta, send me"ya fada yana kashe wayar.

A hankali ya mike ya shige ciki , wata ƙofa ya nufa, yana budewa wani kyakyawan bedroom mai dauke da bed da wadrobe sai carpet , bedside drower , sai wata doguwa kujera 3siter wadda za'a iya kwanciya kai, gefe kuma wani dan lugun ne mai dan faɗi, wanda yake dauke da table wanda litattafan Addini ne kawai a kai, sai wata Yar kujerar zama, wadda da alama ita ce wadda ake zama ayi karatu, Sallayarshi da Chasbharshi Agefe a ajiye .

A hankali ya ƙarasa gefen babban bed din da ya mamaye kusan rabin bedroom din, bai zauna ba, sai ta nufi wani ƙofa in da anan wani kyakyawan bathroom mai tsaro irin na wayyayu ya bayyana, wani katon mirror da yake ajiye a gefen bathroom din ya dan tura, wanda take wata ƙofa ta bayyana , da mamakina naga ya murɗa hannun ƙofar ya shiga ciki, wani rantsatsen bedroom da ya fi na baya haɗuwa ne ya bayyana.

gaba daya kayan bedroom din green ne da white, wanda kalar tayi mugun fito da bedroom din, gefen bed din da ya sha shimfiɗa da green and white bed sheet ya nufa, bai zauna ba daga tsaye Shehi ya fara warware igiyoyin Alƙyabbar jiknshi, sai da ya kunce kafin ya zameta daga jikinshu a hankali, cikn natsuwa ya ajiyeta a gefen bed din, lokacin kuma na ƙare mishi kallo, babban mutum ne sosai dan a kalla in bai yi 33 years ba zai iya yy 29 to 30 years, yana d dan faɗi ba sosai ba yana da tsawo da faffadan kirji, ba za'a kirashi mai jiki ba ba kuma za'a kirashi marar jiki ba,bashi da ƙiba yana tsaka tsakiyar jiki, irin na Jarumai ko in ce sadaukai.

bayan ya zame Alkyabbar ya ajiye, wani farin boyel ne mai kyau da taushi ya bayyana , ya ji dinkin surfani da ya kasance Golding , sosai dinkin yy kyau kuma ya dace da jikinshi, wata ƙofa naga ya ƙara nufa, nan kuma wani Bathroom din ya ƙara bayyana wanda shima komanshi ya kasance green da white gwanin kyau.

bottom din gaban rigarshi ya shiga ballewa, bayan ta cire rigar wata rigarce ta ƙara bayyana, haka bayan ya cire dogon wandon Boyel din wani wandon mai dan tsayi da ya kusa rufe ƙafarshi ya bayyana, ajiye kayan da ya cire yy a jikin hanger, matsawa yy jikin shower ya sakar wa kanshi ruwa, a hankali ya furta "Subhanallahi", ya fada yana lumshe lu-lu eyes dinshi, wanda hakan yy sanadiyar kwanciyae eyes lashes dinshi, wanda suka kwanta a ƙasan idanunshi suka yi zaro-zaro sakamakon ruwan da take sauka a kanshi wanda yake gangara har cikin jikinshi gaba daya .

gashin kanshi kuwa gaba daya ya rufe mishi fuskarshi ya zamana ba'a iya ganin fuskarshi, sa boda gashin kanshi da ruwa ya jiƙa ya zubo, ya dade sosai ruwan na dukan jikinshi, kafin ya dauki wani soso mai taushi da Sabulun Dove mai gyara fata da sanyata taushi ya fara gogawa jikinshi ba tare da ya cire kayan jikinshi ba, while ruwan da ya kunna yana dukan kanshi.

duk kuwa da ga komin wanka nan amma bai damu da yin wankan ciki ba, domin yana koyawa kanshi rashin jin dadi, domin yana duba wanda basa da dukiya ya suke, shin lokacin da Allah ya yanke maka wani jin dadi ya zaka yi?, hakan yasa wani lokaci yake dan nuna wa jikinshi ba fa kullum ake kwana gado ba dolle wata ranar a kwanta a ƙasa.

har ya gama wankan mai matsa daga ƙasan shower din da take dukan jikinshi ba, sai da a ko wane lokaci yana ƙara rumtse idanunshi da kiran sunan Allah har ya gama wanka.

yana gamawa ya nufi wata Yar kofa ya bude, ya shiga tsarin jararrun kaya ne musu kyau da tsari tare da tsada suka bayyana a cikin gurih, wanda hakan ya tabbatar min da cewar gurin Adana kaya ne.

dan sakaya ƙofar yy..kusan 10 minutes kafin ya turo ƙofar ya fito kamshin turaremshi na Huge boss din da na shaƙa ne ya tabbatar min da fitowarshi, cikin wani shigar ta Ash din Jallabiya har wa yau kanshi na nannaɗe da rawani , a haka ya fito yana ta baza kamshi, kafarshi sanye da wani slippers mai taushi a hankali yale takawa har ya fita dayan bedroom din , zama yy kan bed, tars da daukar wayarshi da take haske alamar shigowar saƙo, a Gmail dinshi ne aka turo mishi saƙon.

hakan yasa ya zauna cikin bawa Saƙon muhimmanci , a hankali ya bude saƙon, Abun da ya gani yy mugun girgiza mishi tunaninshi, tare da sanya duniyarshi cikin wani, firgitaccen yana yi, a hankali yace "Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un, Allahumma Ajrni fiii masibati ", ya fada yana ƙara duba saƙon Dr din .

kafin ya gama banbance halin da Yarinyar take ciki a lokacin Dr y kira, a hankali ya ƙara mishi bayani, "kamar yarda na rubuta maka, gaskiya tana buƙatar ganin Manyan Likitoci domin su dubata da kyau tare da bata duk wani treatment da ya kamata, babbar Jijiyar dai da take riƙe da jinta tare da maganarta ne ta samu matsala domin tama zaro daga in da take sakamakon mumunan haɗarin da sukayi, sannan ta ko ina jikinta raunika ne, gashi kuma tana dauke da Asthma mai karfi sosai, gashi kuma wani sashe daga zuciyarta yana da matsala, kodarta ma daya tana da matsala, wadda in ba'a gaggauta mata aiki ba zata iya rasa Rayuwarta, gaskiya Yarinyar nan tana ciikin haɗari domin ta shiga cikin Critical condition. wanda bayanin shi zai yi wuya, da mugun wahala ta rayu",ya fada cikin wani yana yi.

wani zazzafan breath Shehi ya sauke, cikin kamilalliyar muryarshi mai tattare da gaji yace "Uhmm", yana fadar haka, ya,kadhe wayar dan ya tabbatar da cewar Dr din ya gaɓa duk bayanan da zai mishi.

Agogon bangon da take maqale a jikin bangon bedroom din ya kalla, ganin lokacin Sallar Magrib ya gaba to, ya sashe miƙewa, dan in dai yana nan bb mai Limancin Masallacin Masarautar sai shi.

A hankali ya......

Littafin nan na kuɗi ne #400 ne kuɗinsa,ga mai so zai iya tuntuɓata domin sanin ta yarda zai biya kuɗinsa.

07033371851

DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROYAL STAR🧚‍♂️🧚‍♂️
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼

*DAGA ALƘALAMIN*

SALMAJI YAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️

SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR)

```MASU SON A TALLATA MUSU KASUWANCIN SU ZASU IYA TUNTUƁATA AKAN NUMBER NA KAMAR HAKA.

07033371851```

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Page 3.

A hankali ya miƙe, tare da daura baƙar Alƙyabba mai dan saukin nauyi a jikinshi, tare da ƙara gyara Rawanin kanshi, sai yy fito A Ahmad Sudeis sak.

cikin Kamala da natsuwa yake tafiya, yaba ta ƙara baza kamshin turarem Huge boss da, ya kama mishi jiki sosai dan har ko bai sa ba, to zaki ji kamshi a jikinshi.

yana Zikirin maraice ya fito daga bedroom din, zuwa palo, kasantuwar yana da Alwala yasa bai tsaya yin wata ba, ya nufi hanyar fita, a ƙafarshi yy shiga tattaki zuwa Masallacin da yake faron Masarautar in da anan kowa dan cikin Ahlin masarautar yake gabatar da Sallarshi.

yana tafe yana zikirinshi, har ya ƙarasa Masallacin, gaba daya Jama'ar da suke bakin Masallacin suka miƙe, tare da fara mimmiƙa mishi hannu, suna gaiswa, wani ɗan tsoho ne yace "Yah Shehin Malamin mu ka guji Ƙasarmu , bayan lokaci mai dan tsawo da ka bar nan sai a cikin Talabijin muke ganin ka, fatan dai komai lafiya?, Ya Mai martaba Abdul-azeez Arman Maleeq Sarki da jiki?", ya fada yana dunƙule hannayeshin.

karo na farko da tunda ya shigo cikin Masarautar da yy amfani da tattausar murya mai dadin Sauraro yy tsohon magana a hankali cikin rashin son maganarshi, ganin lokacin Sallah na shigewa Yasa ya nufi cikin Masallaci duk mara mishi baya suka yi suna Addu'ar Samun Sauƙin wa Abdul-azeez Arman Maleeq Sarki
, gurin Liman ya tsaya tare da kabbara Sallah cikin zazzaƙar muryarshi, gaba daya garin sai yy tsitttttt ana saurarar sautin karatunshi.
Chapter 3 · 0% Book details