← Book details Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direct Hanyar Garin Gombe suka nufa, idanunshi na lumshe bakinshi bai gushe da Ambaton Allah ba har suka yi nisa sosai suka raba dai-dai tsakanin Abuja da Gombe, A hankali ya fara bude Royal Eyes dinshi, tare da kallon wayar da take gefenshi wadda take ta vibrating , ga kuma haske da take kawowa.

a hankali ya kai zara-zaran fararen yatsun hannunshi, ya dauki wayar tare da yin Receiving call din, a hankali ya kara wayar a kunnenshi ba tare da sanin mai kira ba, Wata Muryar ce mai sanyi da dadi ta daki dodon kunnenshi wadda tasa ya dan lumshe ido, yarda ya dan saki jikinshu ne kawai zai fahimtar da kai wanda yake kiran nashi yana da matuƙar muhimmanci a gareshi,a hankali cikin halin rashin son magana yace "l'll call you late ",yana fadar haka ya kashe wayar .

ko Ajiyeta a in da take bai yi ba, wani call din ya ƙara shigowa cikin wayar tashi, ```Jaddi``` sunan Mai kiran nashi ya bayyana a kan screen din wayar, sai da ya lumshe idanunshi kafin ya dauki kiran, A hankali yace "Assalamu alaika", daga cikin wayar muryar wani tsoho ta fara magana cikin harshen turanci , sai da na ƙarewa fuskar wayar kallo kafin na gane ashe number bata Nigeria bace, number ƙasar waje ce.

shi din ma da ya dauka ba wata maganar kirki ce ta haɗashi da shi ba, daga uhmm sai uhumm, shi kenan abun da yake ce mishi, har suka yi Sallama.

4hours ne ya kai su Gombe daga Abuja, direct titin Abdul-azeez Arman-Maleeek Sarki roaud suka nufa, basu tsaya ko ina ba, sai gaban wani tankameman get din gidan Sarauta wanda gaba daya gidan fenti ne irin na daɗɗiyar masarauta, fentin da ba'a samunshi a ko wace Masarauta sai masarautar da ta Haura shekara ɗari biyu da wani abu, tsarin gini da shigar mutan gidan ma ya isa kara tabbatar maka da dadewar Masarautar, a hankali ya bude idanunshi da suka dan zurma sa boda wahalar tafiya, dan tunda ya shigo ƙasar bai samu ya huta ba.

Get din gidan aka bude, in da motacin suka fara shiga a hankali, suna shiga ƙaramin get wanda zai sadaka da cikin gidan in da mutane suke, aka saki wani Algaita da busa wanda ba ko wace Masarauta ake yinshi ba, sai Masarautar da suke da Kambun Sarauta, sanan Algaitar nan da Busar ba wani ne yake yinsu ba, suna busa kansu ne a duk lokacin da wani wanda yake da Haƙƙin Mulkar Sarauta idan ya biyo ta ƙofar wanda bama kowa ne ake budewa ita ba.

matse idanunshi yy sosai, dan baya son busar nan da Algaitar dan a duk lokacin da za'ayisu to gaba daya tsikar jikinshi na zubuwa ne, sai ya rasa Natsuwarshi har sai yata Addu'o'i, yanzun ma hakan ce ta kasance, har suka ƙarasa parking space aka bude mishi mota bai bude idanunshu ba, kuma bai yi wani abu da zai nuna cewar zai fito daga motar ba.

kusan 10 minutes da bude mishi ƙofar motar kafin ya fito, A hankali, cikin kamala da cikar Zati yake tafiya, yana babbazar Alƙyabbar da take jikinshi, hannun na rike da wani dan sada irin na sarakai ko kuma wani gawurtacce a cikin gidan Sarauta.

Ƙofar Fada da ta fi ko ina tsaruwa da shan Ado a cikin gidan Sarautar ya nufa a hankali, kafin ma ya iso, har an shiga An mishi iso da Sarki, yana zuwa ya shige, duk sauran mutanan da yake tare da su , suka tsaya a waje.

Laɓɓansa dauke da Tasbhi da Addu'o'i ya shiga, yana mai yin Sallama ciki-ciki, wata sanyayyiyar murya ce ta Amsa mishi Sallamar daga ciki , a hankali ta ci gaba da tafiya zuwa ciki, Kishingiɗe ya samu Sarki akan kujerarshi, yana shiga ya tashi ya zauna, har ya ƙaraso cikin Fadar idanunshi na cikin kanshi, shi kuwa idanunshi na ƙasa dan baya kallon mutane, kullum idanunshi a ƙasa........
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼

*DAGA ALƘALAMIN*

SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️.

SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR )

```WANDA YAKE SON A TALLATA MISHI HAJARSHI. ZAI IYA TUNTUƁATA TA NUMBER NA KAMAR HAKA.

07033371851

ZAMU TALLATA MAKA HAJAR KA CIKIN SAUƘI DA RANGWAME```

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

PAGE 2.

A hankali ya ƙarasa gurin kujerar da yake zama a kullum da ko Yaushe in ya shigo cikin Masarautar, zama yy tare da dan Zamowa with full respect yace "Sannu da hutawa Lamurɗe", ya fada a hankali cikin natsuwar da ta zame mishi jiki, dan murmushin da ya tsaya mishi iya kan fuskarshi yy tare da cewa "Sannu da sauka Arɗo", jinjinw kanshi yy bai ƙara cewa komai ba,sai da suka nisa kusan 5 minutes kafin Ahmad Arman Maleeq(Ƙanin Mahaifin Arman Maleeq), yace "Ya Barkindo da jiki ?", ya fada maganar na tsaya mishi iya laɓɓanshi.

a hankali cikin natsuwa da kamala ya bude laɓɓansa tare da cewa "Alhamdulillah", ya fada tare da mayar da idanunshi ya lumshe, tsureshi yy da ido na dan wani lokaci kafin ya juya idanunshi, ya dade sosai a gurin Ahmad Sarki kafin ya miƙe, A hankali yace "zan shige", bai ji Amsar da Allaraini ya bashi ba ya fice a binshi.

har ya shige ta gaban wani side mai kyau da tsari, sai kuma ya dawo baya, a hankali ya doshi cikin palon sashen, tura ƙofa yy a hankali yy Sallama, cikin palon yana tura kanshi ciki.

cikin Kaɗuwa da razani Hamshaƙiyar tsohuwar matar da take zaune nannaɗe cikin wata ƙasaitacciyar shiga, mai kyau irin ta Masu fada a ji, ƙarasowa yy cikin palon, ya zauna fuskarshi bb walwala ko kaɗan, fuskarta ta haɗe fiye da Yarda take baya, kyakyawa ce fara tasss da ita, tana da manya idanu, da hanci har baka, sai dan ƙaramin bakinta, yana yin kallon da take bin Sheikh Arman maleeq kawai zai gamsar da cewa akawai wani abu mai kama sa ƙiyayyaeshi a cikin ranta.

Cikin Yar isa da taƙama tare da jin kanta a Sama tace "sannun Isasshe Saukar yaushe ?, yau kuma daga wata duniyar ?, Ya Ubanka yaji da jiki?", ta fada cikin gatsali , idanunshi ya bude ya watsasu akan fuskarta a ƙaro na farko tun da ya shigo cikin palon.

Harshen shi ya taune kafin cikin ƙarfafa harshenshi da kumbura bakinshi, ya ce "Uhmmmm", abun da ya furta kenan bai ƙara kallon in da take ba, ita ma din bata damu da maganar tashi ba, bata kuma damu da lafiyar Mahaifin nashi ba.

a Hankali ta miƙe tayi cikin bedroom dinta ba tare da ta ko kalleshi ba, Sheikh kuwa haka ya gaji da zama ya miƙe tare da barin palon, zuwa sashenshi da bayan na Sarki da Sayya(Mahaifiyar Ahmad Sarki , tsohuwar da ya fita daga sashenta) bb sashen da ya kai shi kyau a cikin Masarautar.

Fadawan da suke a ƙofar shiga cikin sashen ne suka bude mishi, ya shiga cikin palon bakinshi dauke da Kamilalliya kuma cikakkar Sallama kamar yarda Addini ya tanadar, bb kowa cikin palon, sai dai hakan bai hana komai da yake cikin palon yin aiki ba kama daga kan Fankokin da suke kunne da AC har kan hasken da ya mamaye gaba daya palon , wadda ya haska ko ina tanwar kamar rana.

kuma ko ina ƙal-ƙal bb alamar ƙazanta ko wani najasa, a hankali ya fara taka ƙafarshi tsakiyar palon, idanunshi a dan janye, har ya ƙarasa kan kujera 2 siter ya zauna , a hankali ya ƙarasa jaanye idanunshi gaba daya ya lumshesu, yana sauke numfashi a hankali cikin natsuwar da ta zame mishi jiki, a hankali ya dan sanya hannunshi ya fara zare half cover din da suke ƙafarsa, yana sauke numfashi a hankali,har ya gama zarewa a hankali yajaa numfashi tare da furta "Subhnallah wal-hamdulillah waa laaa'illaha'illalahu wallahu Akbar, Suhbanallah", ya furta yana ƙara rumtse idanunshi.

nauyin da ya ji kanshi ya fara mishi sakamakon ciwon kan da ya riskeshi, yasa ya sa hannunshi tare da fara zare farin rawanin da yake kanshi ,bakinshi na kiran sunan Allah har ya gama zareshi.

kyakyawar sumar kanshi da take a barzaze mai kala biyu, ƙasa baƙiƙƙirin irin sumar Asalin Fulani, sai kuma Sama Brown kalar sumar turawa, wadda ta kasance kamar an rinata, sai dai ba rinatan akayi ba, zallar sumar kanshi ce a haka , a hankali ya dago kanshi, tsura mishi idanu nayi , sai dai na kasa ganin fuskar tashi, wadda sumar kanshi ta sauko ta rufe mishi gaba daya fuskarshi, sai dai kyakyawan cute lips dinshi da suka ƙasance pink irin na mata ake iya gani, da kyakywan sajenshi wanda ya haɗe da gumenshi, mai mugun yawa, san har kusan kirjinshi , baƙi sosai irin gemun larabawa.

a hankali yasa hannunshi ya fara zame gashin kanshi da ya zubo mishi akan fuskarshi, da sauri na matsa dan na mugun firgita da yana yin zubin tsarin fuskarshi, dan kallo daya in ka mishi baza ka gamsu cewae mutum bane, abu na farko da Zuciyarka zata fara raya maka shine ba mutum Bane Aljani ne, dan sam baya kama da mutane, sa boda tsananin kyanshi.

yana da kyan da ba kowa ne ya taɓa ganin irin kyan ba, kyanshi Ainahin kyau ne marar Algus , fari ne sosai wanda farin nashi ya sirka da jaa - jaa wanda ba'a cika ganin irin wannan farin a mutanan Nigeria din mu ba,sai dai mutanan waje, yana da yar faffaɗar fuska da bata cika fadi ba, sannan bata cika tsayi ba dai-dai misali.
Chapter 2 · 0% Book details