← Book details Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 14

Sashe 11

Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

miƙewa tayi tare da fara yunƙurin guduwa, Kanshi ya fara jujjuyawa yana mai miƙa hannunsa ya kashe wutan ɗakin.
A take duhun daren da ya tsala ya mamaye ɗakin gaba ɗaya.
Cike da tsoro ta fara kiciniyar sauƙowa daga kan gadon.
Tana sauƙowo, shi kuwa yana isa gab da ita, haka yasa bayanta ya manna da ƙirjinsa, da sauri yasa hannunsa duka biyu ya ruggume da ƙarfi jin yadda take mutsu-mutsun kwace kanta ne, yasa cikin cool voice dinshi yace "Sadiyyerh!", ya furta cikin sanyayyiyar murya mai nuna zallar fushi, wanda hakan ya tilasta mata zama kan kafarshu cike da fargaba.

sakinta yy ya koma kan bed din ya kwanta, da kanta ta gangara gareshi, tare da shigewa cikin jikinshi ,a hankali tace "Afwan Yaa Zauj.!", ta furta a hankali, banza yy da ita, tasan halinshi, dama ba lallai he ya mata mgn ba , amma ita da wannan shirun nashi gwara ma in dukanta zai yi ya duketa, dan ta tsani shirunshi, hannunta ta sanya cikin tattausan gemunshi ta dan shafa, tare da sanya yatsunta biyu tana dan jaaa a hankali, cikin sigar shagwaɓa tace "ina fa Zauj bana son shirunka , na gwamma ce in ma duka na ne kayi . da kayi shiru", ta fada tana cuno baki gaba.

banza ya kuma yi da ita, dan bai ma san ta in da zai fara ba, ace matar Malam gudu, Shehi, Alaramma, Sheikh amma tana abubuwan da basu dace ba, "don Allah..! " ta fada cikin marairaicewa.

Ajiyar zuciya ya jaa tare da cewa "Uhmmm..!", "Uhuum uhummmm", ta fada tana tirza kafafu a jikinshi, zameta yy daga jikinshi ya juya mata baya, riƙe bakinta tayi kafin tace "Laaaa'ilah Abun ya ƙaura har haka, innalillahi don Allah Yaa Shehi ko faɗa kamin in ta kama da duka, Allah kuwa bazan iya fuskantar fushin nan naka ba, domin ban san mai yake nufi ba, fushinka a gareni babban bala'i ne, don Allah ka sauko " ta fada tana haɗa hannayenta tare da komawa dayan side din da ya mayar da fuskarshi.

Numfashi ya ja kafin cikin harshen Fulatanci yaren da yasan zata fi fuskanta fiye da ko wame Yare a duniya, Yaren Uwa da Uba, yaren duk Ahlinta ya fara cewa " D'un wod'a gorko me ma debbo mo tegal nasti shaka ma66e e dow andal, bo d'un gotun e memuki don nanki beldun e bo memuki nontan.

Sai dai to wodi larura nyawu, a d'on gorko wa wai mema debbo to wodi koltan a shaka, ko b'awo waduki god'd'un iri ba majun.

Ko e d'un warti dole sai d'un wad'ama, ko ittiku d'er diyam, da dun watta gam non d'un mema 6andu ko d'un nyid'u ko dun nyid'a.

Ko yidaki tinaki, to wala wakkati te fuki koltal koo d'un hendirta shaka

bo to memuki kin warti na der shiri ko andal, ko majjuki heftiki dina, to wala god'd'un e dow do'o.....

Gam non, har joni memuki bandu na dow jawu dun wod'a, d'un dole bo d'un tubana dun, sannan dun hotana jomirawo tagud'o tagu .
(Haramun ne taɓa jikin juna a tsakanin mace da namijin da ba Muharraman juna ba bisa sani, kuma duk ɗaya ne taɓawar da nufin jin daɗi ne ko kuwa ba da wannan ƙudurin ne ba. Amman a cikin yanayin larura kamar Magani da Jiyya babu makawa sai ya zamo wannan taɓawar da tufafi a Tsakani, ko kuma bayan sanya safar hannu ta roba da ire-irenta, in banda a yanayin da yake keɓantacce idan ya kasance maganin ko jiyyar ko kuɓutar da wanda ya dulmiya a cikin ruwa ba zai taɓa yiwuwa baya tabbata ba sai an taba jikin kai tsaye, ko kuma ta lalurar gaggawa zuwa maganin ko kuɓutarwar ta fuskar gaggawa da rashin lokacin da za a sami safar hannun ta robar da ire-irenta nan kusa".

Hakanan idan ya kasance taɓawar ba cikin shiri ne ba kuma ba cikin sani ba, ko kuma ya kasance bisa jahiltar hukuncin shari'a ne to babu komai a cikin hakan. Duk da haka dai ita taɓawar juna bisa sani ba bisa lalura ba Haramun ce, kuma wajibe ne yin istigfari daga aikatawa da yin Tuba zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki.

cikin sanyin harshe ya kai karshen mgnr tashi, numfashi ya jaa dan ya manta rabon da yy mgn mai tsawo haka, ita kuwa shiru tayi tana saurararshi ,chan tace "Astagfiroullah wa atubu ilai..! ³ Astagfiroullah.!³", ta furta a hankali tana ƙara maƙaleshi, tare da sauke ajiyar zuciya mai sanyi , tana jin natsuwa na saukar mata cikin ruhi da gangar jikinta, tana Alfahari da samunshi a cikin rayuwarta dan a duk lokacin da ratuwarta zata shiga tangal² shi yake tarota.ya mayar da ita kan hanya mai-daiciya.

"Jazaqallahu bil khair Yaa Zaujilkhair", ta fada tana hug nashi very tight har sai da ya dan yi nishi kafin ta sassauta riƙon da ta mishi, a hankali ya fara biya mata karatun Al-qur'ani mai girma cikim zazzaka sanyayyiya lallausar muryarshi, haka ya ringa mata karatun a kunnenta, har sai da ya ga barci ya dauketa , dan yasan a irin wannan lokacin har idan ba haka ya mata ba, to haka zata yi ta surutu har lokaci yazo ya ƙure bata yi barci ba.

sai da ya tabbatar da yin nisan barcinta kafin ya zameta a jikinshi a hankali, sai da ya jaa mata blanket tare da sanya mata pillow a ganta ya runguma mata,kafin ta miƙe ya nufi bathroom,wanka ya yo kafin ya fito, da Jallabiyarshi Ash colour wadda tayi Asalin fito da kalar fatar jikinshi da take ta walƙiya , ya mannu a jikinshi ta lafe, sai hularshi wadda ta rufe mishi gaba daya kanshi, wanda hakan yy sanadiyar zubowar sumar kanshi da take ɗigar da ruwa, "Fa Tabaraqallahu Ahsanul khaliqin ", bb abun da za'ace da ya wuce wannan .

duk in da ake neman cikakken namiji mai haiba da kamala, kwarjini da kasaita , mulki da dukiya, to duk ya wuce yanan, ilimi Allah ya bashi both Arabi da Boko, duƙiya yana da ita wadda har bai san iyakarta ba, ƙarewae mulki shine kanshi Sarkin gobe wanda mulkin Yau din ma yake karkashin ikonshi, shi dai bb abun da zai ce da Allah sai godiya, dan irinsu ne ake cewa 1 in world ma town ba.

Lungun da kayan Ibadarshi suke ya nufa, yana zuwa ya dai-daita tsayuwarshi kan pray mat din gurin,tare da Kabbara Sallah, yy nafilfili kamar yarda ya saba, kafin ya fara karatun Al-qur'ani da Hailala tare da salati, a takaice dai haka ya gama raya wannan daren gangar jikinshi da ruhinshi basu samu wani hutu ba, sai bautar Allah da suka nitso a gurin yi,sai ƙarfe 4 saura kafin ya tashi daga gurin da yake, gurin da ake ijiye kayanshi ya nufa, bai wani jima ba ya fito sanye da Jallabiya sai kuma Babbar Alƙyabbarshi haƙa mai golden din zane , irin wadda yake yawan sawa, kafarshi sanye da takalmi Gucci baƙi da yy wa ƙafarshi gwanin kyau, kanshi na nannaɗe da hirami fari, sai siririn glasses din da ya sanyawa kyawawan idanunshi, wanda ya sanya ne sa boda ya tashu baya jin dadin idonshinshi sosai, yana jin kamar zai mishi kyau, amma ba ƙaramin kyau yy mishi ba dan sai ka rantse irin samarin nan ne yan 20 something, Al halin kuwa ya bawa 30 ma baya dan ya fara hararar 40, turarenshu na Huge Boss da ya zauna a jikinshi ya dauka tare da ƙara faffaseww yarda ba zai yi yawa ba, shi bai yi yawa ba shi bai yi kaɗan ba dai-dai misali, ya sanya, sai da ya gama shiryawa kafin ya kalli Haleematou da ta ƙara nannaɗewa cikin blanket sakamakon sanyin Subhi da ya fara busowa kamar za'ayi ruwan sama , dan da wasu ƙasashen ne da ake ruwan ƙanƙara to da ba makawa irin sanyin nan da ake zugawa da sun sa ran ko ruwan dusar kankarar za'ayi.

matsawa gefen bed din yy , yasan idanunta biyu dan a irin wannan lokacin yasan rabi da kwatar mutanan gidan nan idanunsu biyu, sai dai Yara haka suma kuma kiran Sallar fari zasu mafarka.

"tashi..!" yana fadar haka ya ficewarshi hankalinshi kwance bakinshi kuma na fitar da sautin Ambaton Allah, lokacin da zai fito gaba daya Driver din gidan da Escort idanunsu biyu, suna ganinshu suka fara gaisheshi, bai iya amsa musu ba sakamakon Abun da yake bakinshi, sai dai jinjina musu kai da yy ,

mota aka bude mishi da sauri, ganin lokaci na kurewa yasa ya shiga, A hankali Driver dinshi ya fara jaan motar , cike da kwarewa da sanin ya kamata.......

tafiyar da suka yi ba zata wuce ta 5 minutes ba suka ƙaraso Harami, Kofar shiga ta gaba nan motar Shehi ta tsaya, bude mishi aka yi, a hankali ya fito yana raira karatun Al-qur'ani cikin zuciyarshi, shiga yy cikin masallacin , lokacin da zai shiga lokacin Sallah ya cika, bayan saqala Microphone din a jikin rigarshi ya fara ƙwala kiran Sallah, wanda yasa Haleematou tashi zumbur dan, bayan fitarshi wani barci mai masifar dadi ta fara jin ya dauketa, Umma Jakadiya ma da ba barci take ba ta miƙe ta zauna, haka Ayyana da dukan sauran yan cikin gidan, ba cikin gidan kawai ba duka yan cikin garin in da sautin muryarshi zata iya ratsawa,cikin gaggawa maza har ma da wasu matan ƙwala kiran Sallah, wanda yasa Haleematou tashi zumbur dan, bayan fitarshi wani barci mai masifar dadi ta fara jin ya dauketa, Umma Jakadiya ma da ba barci take ba ta miƙe ta zauna, haka Ayyana da dukan sauran yan cikin gidan, ba cikin gidan kawai ba duka yan cikin garin in da sautin muryarshi zata iya ratsawa,cikin gaggawa maza har ma da wasu mataan,cikin natsuwa da kamala tare da tattausan harshe da karyashi yake rero karatun Al-qur'ani mai girma cikim bawa ko wane harafi haƙƙinsa.

gaba daya zuciyoyin masu sauraranshi sun tsumu, sun shiga bege da shauƙin karatun nasa, domin muryarshi na da taushi da dadi ga wani sarewa da yake cikinta, ba zaka karaa jin dadin muryar tashi ba sai ma ka ji yana rairo karatun Al-qur'ani kai girma, anan zaka ƙara sanin cewar Ehhh lallai Allah yy baiwa anan.
Chapter 11 · 0% Book details