← Book details Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Aslam wanda ya fara daukarta , ya fito yana sharce zufa idanunshi sunyi jaaazir, hatta kayan jikinshi sun jiƙe da zufa, Office dinshi ya shiga, ya zauna ya dafe kanshi...

sai kuma ya ɗago kan tare, da daukar wayarshi. lallatsawa ya shiga yi kafin ya karata a kunnenshi.

sautin ring din Wayar Shehi ne ya fara tashi cikin bedroom din nashi, lokacin 9am ,a hankali ya dan mirgina da Addu'ar tashi daga barci cikin bakinshi, ya miƙa hannunshi, ya dauku wayar, sai da ya duba sunan mai kiran kafin yy picking call din ya ƙara a kunnenshi.

Zallar tashin hankalin da ya ji a cikin muryar Dr din ne yasa ya dan muskuta ya gyara zamanshi,cikin gaggawa yace "Shehi a gaggauta fitar da Yarinyar nan domin yi mata dashen nan,dan jikin gaba daya ya rikice bb sauƙi gaba daya, numfashinta ma baya fita, gaskiya tana cikin hali, in da hali ayi duk abun da za'ayi a yau din nan zuwa gobe a fitar da ita,"sauke numfashi yy .

kafin yace "akwai abokina da yake irin wannan .......

Wannan littafin na kuɗi ne , game buƙata zai iya tuntuɓata ta number na kamar haka.

07033371851

DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼

*DAGA ALƘALAMIN*

ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️

SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR🌹🌹)

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

PAGE 4.

Akwai wani Abokina da yake irin wanna Surgery din a chan garin Madina yake zaune, in kana so zan iya magana da shi sai ya shirya muku duk abun da ake baƙata", Ya fada yana dan sauke numfashi.

dan jaaan ajiyar Zuciya Shehi yy kafin yace "okay..!", yana fada ya kashe wayar, tare da yin baya ya koma in da ya tashi, barcinshi ya koma sai guraren 1pm kafin ya tashi, wanka da Alwala yy ya fito, yana ta baza kamshi, tare da ƙoƙarin sanya agogon Rolex diamond da yake tayi a hannunshi.

kamar kullum yana sanye ne da Turkey Jallabiya fara sol,sai takalminshi da ya kasance half cover, ya lulube gaba daya jikinshi da irin Alƙyabbar Manyan Malamai baƙa mai kwalliyar Golding , ga wani kamshin Huge Boss da yake tashi, yy wsni sihirtaccen kyau, kamar a boyeshu, ƙasumbarshi da sajenshi gaba daya sun kwanta luf,dogon Gemunshi kuwa sai motsawa yake a hankali kyawawan lips dinshi suma suke motsawa,tare da Ambaton Ubangijin Talikai.

Downstairs ya nufa, yana ƙara baza Alƙyabbarshi, da gyara Agogonshi. tun kafin su ƙaraso cikin palon, kamshin turarenshi ya shidawa su Zayn_maleeq da suke zaune cikin palon zuwanshi.

cikin ladabi duk suke kallonshi, har ya ƙaraso cikin palon, duk duƙar da kansu suka yi ƙasa cikin bafa girma suka zube tare da cewa "Barka da fitowa Yaa Shehi", tsantsar kauna da kulawa, ya shafa kawunansu . tare da lumshe ido kafin yace "kuna lpy ?", gaba dayansu suka Amsa da "Alhamdulillah", jinjina kanshi yy kafin ya zauna kujerar da ta kasance ta zamanshi, bayan shi bb mai hawanta sai Zayn_maleeq shima kuma ba ko yaushe ba.

Umma Jakadiya ce ta fito daga wata ƙofa, kallom Shehi tayi tare da dan rausayar da kanta tace "sannu da hutawa Shehi...!", a hankali ya bude jikirtattun idanunshu, akan Umma Jakadiya, kafin ya jinjina kanshi, yace "Alhamdulillah..!", cikim tsananin kula ya mata maganar, wanda yake nuni da Zallar kularshi a kanta.

kallonshi tayi , tare da cewa "Shehi a kawo Abin ci ne ?", dan tsura mata idanu yy na wasu seconds kafin ya jujjuya kanshi, yacr "ah'ah lokacin Sallah...!", yana fadar haka ya miƴe, gaba daya Ƙannenshu suka mara mishu baya izuwa Masallaci.

ko da suka je Shi yana gurin Liman su kuma suna Sahun bayanshi, haka har aka idar da Sallah, bayan an idar duka fito, yana jere da Lamurɗe suna dan tattaunawa Zayn_maleeq da Abdul_Maleeq tare da Sayyid_Maleeq na bayansu tare da Ayman Yaron Lamurɗe, suna tafiya suma suna fira,sai dai Zayn_maleeq duk ya fi zuba, sauran Triplet dinshi kuwa Abdul_Maleeq da Sayyid_Maleeq basu cika surutu ba, duk ya fisu labari, dan su kusan zubin tsarin halittarsu daya da Shehi basu damu da duniya ba ayi ko kar ayi bb ruwansu, su dai kawai suna rayuwarsu.

In da aka tsayar da Motocin Rarrabar Azumi suka nufa, motoci ne Dav guda Biyar, daya Sugar ne ciki,daya gyero, daya wake, daya shinkafa sai dayar Mai ne ciki.

ga kuma jerun mutanan da duk suka hau hali suna jiran Shehi, bude motocin aka yi, fiffito da kayayyakin aka fara yi, Zayn_maleeq na gefe kasantuwarshi na mai son jiki yasa duk wani aikin wahala baya ciki..

Sayyid_maleeq da Abdul_maleeq kuwa suna bayan Shehi suna taimaka mishi, su da kansu suke dauka su bawa Shehi shi kuma ya miƙawa mutanan, bayan an gama rarrabawa, sai kuma ya bi kuwa da 10k , wanda wannan kyauta ta tsoma gaba daya yan Masarautar Baihan cikin murya da jin dadi, dan in ba shu ba sai Babanshi sune kawai suke bautawa Masarautar, da jikimsu da kuɗinsu, basa gajiya da dukkan buƙatun mabiyansu.

duk halin da mutun yake yaje ya fada musu sube masu kafadar dauka, wanda tausayin da Allah ya daurawa Lamido Abdul-azeez Arman Maleeq na talakawan garin shine mussababbin ciwonshi, yanda Al_umma suke kaunarshi shine mafarin ciwonshi, yarda yake da zaratan Mazaje wanda suka kasance Yaranshi ha cikinshi shine ya zama tubalin ciwonshi, wanda shekara day-daya har shekara 20years cif yana kwance bashi da lpy.

rashin lpy mai muni, wadda kwata-kwata baya iya aiwatarwa da kanshi komai, konai sai dai a mishi.

sai guraren 3:30 o'clock suka gama rarrabar cikin gajiyawa, Zayn_Maleeq ya taso daga in da yake zaune ya nufosu, yana zuwa ya riƙe hannun Shehi da yake cikin Alƙyabbarshi , cikin kulawa ya dan kalleshi, da ido ya mishi mgn .

fuskarshi ya dan ɓata kafin yace ,"Yaa Shehi akwai gajiya", ya fada yama kallon sauram Yan uwanshi, Abdul_maleeq yace " wa mai gajiya ??", a hankali yace "Shehi Zayn yake da gajiya..!", ga fada yana dan yin luuuu da idanunshi..

kallonshin Shehi yy cikin dan nuna hukunci ya rike yatsun hannunshi, tare da matsewa, yar ƙara ya saki, cikin dan yana yi yace "Ayya Hamma Shehi na tuba na bi Allah na bika,ba ni da Uwa , Uba ba lafiya Adda na bata kusa Kai ne kawai Babana Mmna , Addana, ka gafarce ni", ya fada yana shagwaɓe fuska.

tuni raunin Shehi ya bayyana, triplets din da suke jere masu bala'in kama da juna ya kalla, numfashi mai karfi ya sauke, tare da dan shiga tsakaninsu gaba daya ya rungumesu . suma riƙeshi suka yi, dan sun san duk lokacin da yake kewar Mahaifiyarsu ne kawai yake musu haka.

sun dan jimaa a haka kafin ya sakesu, ya kama hannayensu , suka nufi masjid.

sai da ya tsayar da su bayanshi, kafin ya matsa gurin Liman ya zauna, Al-qur'ani ya dauka duk ya mimmiƴa musu, shma ya dauka, cikin ƙira'a mai dadin gaske suka fare karatu gaba dayansu. bama sa kallon Al-qur'anin saboda suna da haddarshi a kansu, dan sittin ta zauna musu daram a kansu.

sun san yi karatu mai yawa kafin lokacn Sallah yy, miƙewa yy ya ajiye Al-qur'anin, suma ajiyewa suka yi suka kiƙe, kabbara Sallah yy, duk mutame suna shishigo cikin Masjid din, bayan sun idar suka fito, yana jere da Ƙananshi dukkansu Ukkun dan Dsn Lamurɗe baya tare sa su tuni Lamurɗe yy mishi wata Uwar harara da tasa bb shiri ya barsu.

suna tafiya Zayn_maleeq ma duƙewa, sa boda tsananin yunwar da yake ji, sun kusa shiga part din Shehi ya dan yi yar ƙara tare da dafe cikimshi, da sauri suka jujjiyo gareshi, kafin suyi taku daya ya isa in da yake da sauri ya taroshi, karashi yy da jikinshi, tare da tsura mishi kyawawan idanunshi, yana kallonshi.

sai kuma ya kalli Abdul_maleeq da Sayyid_ Maleeq, kallon sa yy musu kawai ya fahintar da su mai yake nufi, da sauri suka tarairayi Dan Uwansu, suka kakkamashi zuwa part din su, har sun gilma part din Jadda, Zayn_maleeq yace su shiga da kyar, su sama mishi abun da zai ci.

ba suyi musu ba suka shiga, zaune suka samu Jadda ƙafa daya kan daya tana kallon TV , zaunar da shi suka yi, cikin irin maganarshi yace "Jadda ina son a bani Abin ci", ya fada yana dan riƙe ciki, yarda ta dan washe fuska ta miƙe, kitchen dinta ta nufa da sauri, kallon juna suka yi, kafin su kalli Zayn_maleeq da ya dawo ƙasa yana jiranta .

bata jima da shiga ba ta dawo , baiwarta na bayanta hannunta dauke da babban tray mai dauke da wormers marasa girma sosai, da plates da spoons , sai dan jug mai dauke da juice .

ajiyewa tayi gaban Zayn_maleeq tana washe bakinta, kai da ganin irin murmushin da take zakasan akwai wata a ƙasa, dan farkom shigowarsu palon ko kallo basu isheta ba.

gyara zama Zayn_maleeq yy tare da bude katuwar Wormer din gabanshi, kyakyawan tuwan shinkafa da yake fari tass an mulmuleshi a cikin fararen ledoji ya mayyana, tuwo daya ya dauka, tare da bude wormer din miyar.

haɗaɗɗiyar miyar Egusi , da tasha kifi banda ta bayyana, plate ya dauka ya zuba miyar a plate. a hankali ya fara ci yana jin wani dan karci a bakinshi, sai dai bai kawo komai a kanshi ba, har ya kusan cin rabi.

kallon Abdul_maleeq da Sayyid_maleeq tayu, tare da ɓalla musu harara tace "ku ba zaku ci ba ...?", ta fada tana kallonsu da idanunta da suka ji bakin kwalli jail.

taɓe baki suka yi basu ce komai ba, tsaki ta jaa tare da cewa "Shegu ni zaku wa kwanere, ni na ci Uwarku har da Ubanku a Iskanci", ta fada tana kwata, tari ne ya dan tsarke Zayn_maleeq a hankali ya fara tarin, har ya fara yi sosai.

tari ne ya tsarkeshi sosai, har idanunshi suka fara kakkafewa,, a tsorace Sayyid_,maleeq da Abdul_maleeq suka nufeshi, suna jijjigashi, sai dai baya jin su dan ya fita a hayyacinshi.
Chapter 5 · 0% Book details