← Book details Arangama 1 To Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 13

Sashe 9

Arangama 1 To Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

akurmandaji Hankalin kowa yatashi can Sai Sarki Rahux yabushe dadariya tamkar yahaukace jama,arsa suka Zubamai ido saida yaidariya ta isheshi sai kuma yakwarara ihu gamida cewa karyane lalllai babu wani mahalukin da ya isa yashigo Kurman daji ya mulkeni tabbas ba,abubane mai yuwa ba kodai mui mutuwar kasko dashi kokuma inkasheshi kokuma shi yakasheni yadaga murya yace tabbas wannanne kawai zai yuwu sai yadubi jama,arsa yaimurmushi yace ku kwantarda hankalinku kuma kusaurareni nanda kwanaki uku sai yai girgixa take rikida yaxama wani katon jemake ya yunkura yaisama yalolaka yabace acikin gajimare acan fadar Shu,umiyya kuwa bayan sun sauka afadarta Sai sukaga Zaki Asad da Dage Mauru acikin fadar koda Zaki asad yaga Bahayurada jaririnta sai yai wani gurnani yanufi inda suke yanaxuwa yakama lashe jarinnan wanda tunda aka haifeshi ba,asami natsuwarda za,aimar koda wankaba acan fadar Kasar Tamolika kuwa Fada tacika tabatse tamkar zata tsage kide kidene ketashi gamida wakewake kowa kaganshi akasar Tamolika yanacikin farin cikida annashuwa mata da maza sai tikarawa sukeyi anacikin wannan haline nashagali gamida Shagala sai Sarauniya Azira tafuto tareda Jariranta guda uku datahaifa alokaci daya woohoohoo ai sai fada tahargitse jama,a suka rika barka ihun murna take masu ganguna suka saki kida mawaka suka shiga rera wakokin yabo ga Sarauniya Axira da Jariranta inda Saboda tsananin murna da Farin ciki Saida Gimbiya Azira dakanta takama taka rawa dankari ai sai mata suka saki guda fili yarugume darawa ba babba bayaro Kwatsam Sai akaji tsawa maitsananin karfi kamar fashewa dutse kamar karan aradu tamkar tannatsa dankari ai saijama,a suka rude fada tayamutse akafara guje guje indadakaru suka zare makamai sunajiran kota kwana Sarauniya axira tai tsawa cak mutane suka tsaya kowa yakame a,inda yake kwatsam sai tsohuwa Uzaima tabayyana ranta abace fuskanta amurtuke idananunta na xubda hawayen takaici duk wani mahaluki dake wannan fada saida hankalinsa yatashi ganin tsohuwa Uxaima awannan hali tabbas kowa yasan balafiya wai kare yasha taba aikai curko curko tsakanin Tsohuwa Uxaibu da jama,ar Sarauniya Azira shuru kakejim Fadarkamar mutuwa taratsa fadar, Can sai sarauniya axira tanufi mahaifiyarta tsohuwa Uxaibu ta isadaf da ita ta tsaya agabanta suna kallon Juna kuma suna jin nun fashin Juna sarauniya Axira tabude baki zatai magana Sai tsohuwa Axira tadakamata tsawa gamida Dau keta damari Ai bakidaya fadar sai suka tsorata gamida Durkushewa bisa guiwowinsu suna Zubda hawaye Tabdijam akwai matsala DANHAKA NAFECEEEEEE MUHADU AKICIN ABOKAIINAARANGAMA LITTAFINA BIYU PART 5-6 Bakidaya jama,ardake Fadar Sarauniya AZira suka durkushe bisa guiwowinsu itakanta Sarauniya azira durkushewa tayi bisa guiwowinta gamida sunkuyarda kantakasa Tsohuwa Huxiyya tarika kaikawo atsakanin mutane saida takaitadawo kamar sau arba in sai takwarara ihu wanda saida bakidaya jama,ar fadan sudagakai sukalletatanuna Sarauniya Axira tacelallai kincika mahaukaci Sharafarmulki yadibeki har kimmance da makiyarki to kisani Dakarunda muka turaKurman Daji basui nasaraba hasalima sunkoma bangaran abokiyar gabace tabbas ahalin yanxu sune suke batatsaro afirgice jama,ar fada sukamike gamida zazzaro idonunsu Tabbas wannan magana yagirgixa sarauniya Axira domin saida takwalla ihu TSOhuwa huxxiya ta kyalkyaledadariya tace 'yata harkin tsorata togawani sabon labarin dayafi nafarko tashin hankali to Kisani Bahayura tahaihu dana miji wohoho ai sai Axira takwarara ihu takama Sambatu gamida Sakin maganganu marasa kangado Sarauniya Azira tadurkusa agaban tsohuwa Huxiyyatace yake ummu tamolika meneneabinyi kitaimakemu huxxiyya tasaki ashariya tace kumutanen kasar tamolika kusani sarakunan tamolikawa goma sha hudene aka haifa musu jarirai awannan shekara kuntaru kuna murnada farinciki to akurman daji Jariri daya aka haifa Sannan shine ajali jarirai goma Shahudun da akahaifamuku tsohu tadaga murya tace lallai rayuwarku tanacikin hadari muddin yaronnan yagirma to sai yazame muku balbalin bala ii tabbas Sai yayaki sarakuna Tamolikawa goma Shahudu kuma sai yakifarda gwabnatinku Sarauniya Azira tace kitaimakemu ummu Tamolika Tsohuwa tace lallai ku yayanane dolene intai makeku amma kusani abin yafi karfina saboda haka Zan ziyarci Babban Boka Baharamal Majushi dake dogon tsauni saboda hakaku saurareni nanda cikar kwanaki uku kawai saita bace bat bata bayyana ako inaba sai adogon tsauni tasauka Saukanta keda wuya Sai wasubakaken aljanu su uku suka bayyana agabanta sukai gaisuwa agareta sai suka wuce gaba tabisu abaya sukai tafiya maidan tsawo sannan suka biwata yarkaramar hanya sucigabada tafiya Sannu ahankali su isa wani fafareren kogo aljanunnan suka shige cikin kogonnan itama tsohuwa huzziyya tabi bayansu suka isa wani wawukeken gurin maikamar falo inda akajera wasu kujeru da a sana antasuda kasusuwan mutane Gawani Basarakenan yana zaune adaya daga cikin kujerunnan kawai sai aljanunnan suka baceTshohu huxiyya tasami kujera daya dagacikin kujerunda aka sarrafasu da kashin dan adam taxauna zamanta keda wuya saita kurama mutuminnan dake xaune ido haka shima mutumin yakura mata ido suka xubama juna idanu kamarmasu kokari tuno wani abu tsawondakika talati suna kallon juna alokaci guda fuskansu taka sauya kamar ambusa musu kahosuka mike atare su dakama junansu tsawa Tsohuwa huxiyya tanuna Sarkinnan da yatsa tace kai Sarki Rahux dukda yau rabonmu damu hadu shekaraHamsin kenan kana tsammanin zamacekane lallai gabardake tsakanimmu ta asaline kuma yaxama dolene inrabakada duniya kamar yadda karaba kanwata Rmix daduniya Sarki Rahux yakwaredadariya yace mejiya tayi bare yau lallai bazaki iyamin komaiba domin ahalin yanxu nasami karfida Sirrikan tsafi huxiyya tace hakane torikemin wannan masifar kawai sai ta busomasa wata bakar iska maidaukeda iyayikai kafin yadauki wani mataki tuni iskannan tariskeshi wasu kananan wukake suka yayyakeshi asassan jikinsa tsanani Xafi saidayakwalla ihu huxiyya takyalkyle dadariya tace har yanxu yaro yaronetawatsomai wata wutar tsafi wutartanufoshi gadangadan hartana wani kore kore Sarki rahux yanuna wutarda yatsarsa gamida ambaton kalaman surkulle take wutar tamutu yawatsamata wasukananan macixai macixan sukanufi tsohuwa Huziyya sunatafiya suna kara girma suka xama murdamurdan macixai dankari tsafi gaskiyarmaishi aisai huxiyya tbude bakinta bakidaya tahadiye macixannan Sarki Rahux yatsorata kawai sai tsohuwa Huxiyya tahangame bakinta atsiyace macixannan suka futo acikinta suna wani feshin wuta sunufi Sarki Rahux dole kawar naki aikoda hango wannan masifa saiyabace bat suma macixan suka bace tsil saigashi yabayyana agaban huxiyya yakafta mata Sara dankari tamkar yasari dutse haka wani kara yatashi afusace huxiyya tasa kafa tabankeshi Saida yai sama yafado kansa yafashe amma Sai yamike yakwarara ihu yazare takobi yakwarma ihu yaikan Huxiyya saitai girgixa take tarikida tazama wata basadukiya yar shekara arba in itama taikansa afusace makami tsirara saura kiris suhadu sai suji ankwarara ihu gamida tsawa cik suka tsaya Sai Boka Baharamal Majusi yabayyana ransa abace yanacewa kai sakarkarun banxa kuna fada akan tsohuwar gaba tashekara hammsin bayan ga yaronda yau kwanakinsa bakwaine aduniya amma yananema yagirgiza bokaye da Sarakunan duniya suka zubarda makamansu yakallesu yace dukkanku matsalarku iri dayace Bahayura da danda tahaifa bakidaya sukalleshi yaceto bakukadai bane ilahirin sarakunan duniya da bokayen duniya suna cikiHadarin domin mutukar yaron yagirma zaiyiyi watadoguwar tafiya wanda ahanyarsa natafiya sai yakauda dukwani axxalumin Sarki dakuma bokaye sannan mutukar ya isa inada yakesom zuwa yadawo to ahanyarsa nadawowa sai yagusar daduk waniaddini yakafa nasa sabo wanda zaikarbo akasar BABILA Huxiyya da sarki rahux suka rude Sai boka Baharamal majusi yacemusu kuxo kui kallo a allon tsafina yauce ranan daza ai bikin sunan danda BAHAYURA tahaifa kuma ayaune Sadauki Dunguruma dadakarunsa zasukai harin bazata awurin wannan biki tobari mugani Wani Suna za,asama wannan tsinannen yaro kuma wacce dambarwa za,adiba Idan Sadauki Dunguruma yadira ana tsakiyar shagali TOGAFA BIKINCI BAZANIARANGAMA LITTAFINABIYU PART 6-7Fadan shu,umiyya tacikamakil taron aljanu damutane harmada manya manyan dabbobin daji saikaikawo sukeyi amasarauta sakamakon cewa yaune ranan da Bahayura zata bayyana sunan Jaririn data haifa saboda haka masoya dakuma Dakarun Hatsariyya dana Hatsabiyya hadida na shu,umiyya gamid Zaki Sad dadage Mauru sune suka taru suna jiran futowar Bahayura da Jaririnta can saigata tafuto tacaba ado irinna yayan Sarakuna tanarungume dadanta bakidaya jama,ar aljanuda mutane suka mike inda wasu matan aljanu suka rika watsamata fure mawaka suka rika reramata wakokin yabo ita dajaririnta Bahayura tatsaya atsakiyar jama,ar aljanu damutane tafara magana tana cewa yaku taron maso hakika yau ranace tamasamman a Kurman Daji domin yaune za,afara radama jariri na farko da,akahaifa akurmandaji suna tadaga jaririn sama tace yaku al,umardake cikin kurmandaji masoyanmu da makiyammu aljanu da mutane lallai kushaida sunan wanna yaro Silahul,Mulk akarangada guda wanda bakidaya saida gudan takarade kurman Daji nanfa makada suka sakiganguna mawaka sukacigaba darera wakaturkashi rawa harda Zaki Asad dadage mouro anacikin wannan shagaline sai aka fasa wata kururuwamai raxanara samatai bakinkirin akadinga watsa walkiya dankari aisai wata tawagar aljanu da mutane sukarika dira daga sarari samaniya kamar farin annoba saida akadauki tsawon sa,a uku cur mazaje nadiro suna hada Sahuta dakarun kimanin miliyan arba,in sufuskanci inda Bahayura take hoho ai sai HATSARIYA HAYTSABIYYA SHU,UMMIYYA SUHAILA ZAKI,ASAD DAGE MAURU suka jadaga suka fuskanci makiya nanfa aka fara kallonkallo gamida hararan juna can sai asaki wanitsawa mai kamada fashewar dutse kawai sai Sarki Dunguruma yabayyana yadubi su Shu,umiyya yabushe dadariya akarshe yadaure fuska gamida daka musu tsawa yace kai kananan shaidanu hakika kundade kuna nuna hatsabibanci aKurman Daji to daga yau toxo karshe yadaga murya yace lallai ni Sarki Dungurima inamai rantsuwa da girma gamida daraja da ixxata yau sai nakawo karshen hatsabibancinku tabbas saina kawo karshen Hatsarinku indakatarda Shu,umancinku awannan daji tahanyar sarekawunanku sannan yai shiru gamida kare musukallo yakara bushewa dadariya yanunasuda tsinni takobi yace ammakunada wata alfarma mutukar xaku barmu mukama Bahayura da Jaririnta Silahul mulku salim alim to sarki Dunguruma zai barku kurayu Kaiiii hatsariyya tadakamai tsawa tace karyane ruwa da iska mutum da aljan lallai bazasu iya rabamuda wannan yaroba Hatsabiyya takarba taceda Sarki Dungurima Kai wawan sarkine azotonka dankakwasotarkacen dakarunka shine zaka tsotamu to lallai kunadazabi kodai kujuya kusan inda kunufakokuma kuhassalamu kugayyato mutuwarku dakanku sarki Dungurima yakwarara ihu dakarajin fusata,yai,umurni da afara yaki hodijon ai sai dakarunsa sukai gunji gamidakururuwa sukai kansu su shu,umiyya kaiya ai suma hakasukai yunkuri su afkamamakiya wayyo fashi barnan aiki take yaki kullu akafara cinikin rayuka Hatsariyya tafara tafiyar ruwa darayukan makiya domin wani irin bahagon yaki takeyi tanarike dakubbaguda biyu sa fille kan aljannu da mutane,takeyi duk inda tai gunji takai kora saidai kaga mazaje naxuba wohoho hannu ya iya jiki yasaba Shu,umiyya tatashi sama tamakale asarari samaniya saiwatsomasifu takeyi marasa kangado tarika konewa da babbake tawagar makiya tabbas awannan ranace Hatsabiya tatabbatarma da makiya cewa ita hatsabibiyace domin alokacin da ta afkama mazaje dasara dasuka sai makiya sukarika ganinta takasu kashi dubu tawatsu atsakiyarsu kuma,kowacce kisan kiyashi takema makiya guri yai guri yaki yai yaki aljana suhaila haka tarika raba kyauta mutuwa ga makiya inda Zaki asada yadinga sa kiji yana bige maxaje
Chapter 9 · 0% Book details