← Book details Amani Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 13

Sashe 9

Amani Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ashe-ashe! To ni kam wace jinya zan yi banda in tambaye ki ya aka yi haka? Kika bada kai daga shigowa daki? Ai ni na dauka gudun aure zaki dinga yi kullum dare zuwa gun Mowa, irin yadda ake yi a zamanin mu in baa son mijin, irin dai yadda ba kya son Maina, na dauka har sai ya gaji ya daure ki jikin karfen gado Kawai kuma sai in ga kwana daya da zuwa an kar Boss? Kuma da Mukhtar din da ba so ake ba, ake wulakantawa? Amani kamar ta rusa ihu da wannan habaici na Babar ta Sahura, amma bata yi ihun ba. Tsaki tayi, tayi banza da Sahura, ta juya kai ta cigaba da kwanciya. Sahura ta hau latsa wayar ta tana cewa ai dole Yaya ya bani goron albishir, har Jalan ba zaa bari a baya ba. Nan kuwa ta kira Mamma Jalan ta ce Jalan, kunnen ki nawa? Kunne na biyu kara biyu ki sha labari Mamma na dariya ta ce na kara takwas ma sun zama goma Yawwa to yau dai su Uwa an kai munzali, yanzu zan wanke zanin gadon nan, ke baki gan ta ba abun tausayi duk bakin rashin kunya ya mutu! Mamma ta kashe wayar ta tana cewa Sahura-Sahura ban san yaushe zaki girma ba. A lokacin Haj Jalan ta fadi ta yi wa Ubangiji sujjadar godiya, ta yarda sa idon iyaye yana taimakawa tarbiyar yara ne kawai, amma kiyayewa tana wajen Ubangiji, a yadda Amani ta taso, wa zai mata wannan kyakkyawan zaton? Har digirin zamani ta yi. Surutun Sahura ciwon kai yake kara mata, sai ta ce don Allah don Annabi Baba Sahura na yafe jinyar taki ki je, ni lafiya ta kalau ba abinda ya same ni. Sahura ta kara babbakaro dariya sannan ta ce oho dai, mun ga karshen rashin kunyar Tafisu, da karshen rashin So, kwana daya da zuwa an mannewa bawan Allah an tsotse shi tas!. Sai kuka ya kwacewa Amani, ga damuwar dake ran ta ga bakin cikin da Baba Sahura ke kumsa mata. Ba wata jinya data wuni yi mata sai shakiyanci, da yamma Ummami ta zo ta gan ta a zaune tana shan madarar rakumi data bata, ta daina kukan amma bata yi wata kwalliya ba don haushin Mukhtar take ji sosai. Ummami ta dan zauna suka yi hira da Baba Sahura sannan ta koma sassan ta. Da Mukhy ya dawo daga Dosso gun Ummami ya fara zuwa, yace yana son zai sha tea, ta ce ka je wajen matar ka ta baka mana? Yace Ummami pls, ai na san da ita na ce ki bani din, kada in soma ce mata ina son wani abu, ta ji dadin yi min zancen Sadaka Ummami ta ce to bazan bayar ba, sadaka kuma zan roki Mai kada a baka yanzu, yar mutane na neman zarewa. Yar dariya Mukhy ya yi, ya tashi zai fita, a ran sa ya ce Umh, Ummami bata san Amani ba ne shiyasa take tausaya mata, ai shi kam wannan Sadaka ko baa bashi ba, ya gode da tayin su da aka yi masa, ko babu komai sun sa jiya ya more iya morewa. Yanzu ma da barazanar su zai ci gaba da samun kan Amani ya cigaba da yin yadda yake so, lokacin sa ne. Itama sanda take gaban iyayen ta tana kan tsinin ta na Tafisu wane rashin mutunci ne bata tata masa ba? Ai shi nashi nafila ne, tunda bai hadawa da cin zarafi kuma bai taba alaqanta ta da kama da shegu ba wai don tana da kyau, wannan magana ta dade tana haunting din sa duk da cewa in kyau ne ai sai dai su yi kunnen doki shi da ita. Haske kawai ya fi ta. Ya isa sassan su yana wannan tunanin, ya isa har falon sa yana waya da Kamilu, wanda ya gaya masa su Alhaji sun sauka gida lafiya, yau ga Alhaji a kujerar ofishin sa ta FASKARI INVESTMET (Executive Director) wato Alhaji ya koma office yana dan dogara sanda amma, farin ciki mai tsanani ya kama Mukhy, ya ce da Kamilu duk da haka kada ya dinga barin sa yana ayyuka masu yawa, ya san halin Alhaji sarai, wajen neman kobo. Jin shigowar sa yasa Sahura yi mata sallama, ta ce to Uwa zan je na kwanta, maigida ya dawo ko kula ta bata yi ba don akaifa take ragewa da nail-cut a lokacin. Har dakin ya shigo bayan sun gaisa da`Baba Sahura da ke fita, sannan ya kashe wayar sa ya saka a aljihun sa. Ta daga kai a hankali ta dube shi, sai annuri, cikar zati da kwarjinin mulki ke fita daga fuskar sa maabociyar zati da kamala, ya ji dadin labarin da Kamilu ya bashi na samun lafiyar Alhaji da komawar sa office, Mukhy ya sha rawanin sa fari kal, ya fito a cikakken Diffa-Arab din sa, ya tsaya daga kan ta yana warware rawanin, ya ce, Sweetheart, na dawo me zan samu Maam Amani? Bata yi magana ba, ta cigaba da cutting farcen ta kwarjinin sa da kamshin turaren sa duk sun cika ido da hancin ta, sai ta tuna ta yi alkawarin zama macen kwarai, macen kwarai kuwa tana yi wa miji sannu da zuwa da adawo lafiya. A hankali ta daga sexy eyes din ta ta zube su a kan shi, ta ce, sannu da zuwa Ya Mukhy. Ta mike tana cewa bari in taya ka cire rawanin nan, na ga alama tsayi gare shi, ta shiga taya shi warware rawanin, sai ya ruko kwibin ta, ya rike ta cikin hannayen sa ya dube ta da idanun Rahma har cikin ido. Duk kin rame, a abinda bai fi sati guda ba kacal, me yake damun ki haka Tafisu? Mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki sai ta saki kukan dake cin ran ta a hankali, a sukwane ta fada jikin sa. Mukhy ya samu yadda yake so domin ta rike shi gam tana rawar jiki, tana fadin yau a gaban ka zan tube, ka kalle ni da kyau ka gani ba abinda bani da shi da sauran mata ke da shi, watakila nawa ma ya fi nasu cika, idan nayi hakan zaka fasa karbar sadaka? Mukhy me zai yi banda fashewa da dariya, ya ce By Allah you will be the death of me Amani.. Ya soma sumbatar ta ta koina, don ya samu ya mantar da ita zancen sadaka. Amma bata yi shiru ba, cigaba ta yi da fadin. Wallahi Ya Mukhy da gaske nake na tuba, na tuba na bi Allah na bi ka ba zan sake ba, to ni nace kin min laifine a bani sadaka a kan hakan? Ko shi Mai (Sarki), bai san ma me kika yi min ba, balle ya bani sadaka don ya rama min. Alada ce kawai kyakkyawa ta gidannan yake son ya cikasawa, alada ba addini bace Ya Mukhy, besides yanzu addini ya daina supporting concubinage, irin wannan auren wasu malaman ma yanzu suna fadin bai halatta ba a wannan zamanin, tun da baa yaki balle a samo ganimar bayi. Mukhtar ya kasa hadiye dariyar sa yace Ya Shaikh! Amani kenan, su bayin basu da yaya? Kuma yayan su ba bayi bane? Baki san ana gadar su ba daga iyayen su? Kuma in ban karbi Sadaka ba aure kike so in kara da kuruciya ta mata su cika min kwanya? Ai adalci ne aka yi miki, ta hanyar girmamaki, a baki su a matsayin ababen ikon kisai kin so zasu zo inda nake haka sai kin nemi hutawa zan bukace su. Mukhy ya cigaba sumbatar ta a dokance, yana cigaba cewa, In kina son mu zauna lafiya kada ki sake yi min zancen Sadaka, wallahi na gaji da jin zacen nan, na gaji Amani, ki bar ni in huta. Amani kawai nake so yanzu, amma kina neman haukata min ita, duk kin birkita min Amani ta koma kamar zararriya. Daga haka ya juya akalar hirar tasu zuwa wadda yafi so a yi, wadda ya dawo cikin dokin ta, Amani bata da zabi ban da bin umarnin sa, na barin zancen sadaka da baya so, ba don ta gamsu cewa Mukhtar ya fasa karba ba, tunda kuwa bai furta fasawar da yawun bakin sa ba har yanzu. Sai taji duk kokarin sa na faranta mata rai, ta hanyar nauikan soyayyar sa da sumbar sa mai shiga har kololuwar ran ta yanzu sun daina sanyata nishadi ko irin yanayin da yake saka ta a baya. Ta dai yi hakuri ne ta kyale shi amma yau bata yi kowacce hobbasa ta taya shi. Mukhtar a ran sa ya ce in haka mata ke kin kishiya da dukkan zuciyar su, willing to do everything ga mazajen su don su kada a yi musu ita, da ya baiwa duka maza shawara su kara aure, ko don mata fitinannu irin Amani su shiga taitayin su. Shi kam yau dan gata ne sai yadda ya juya abar sa.. madalla da iyaye masu son cikar farin cikin yayan su irin nasa iyayen. ko babu komai sun samo masa kan Amani yadda baya zato, daga jiya zuwa yau ya mori auren sa har fiye da kima, daga jin zancen sadaka. ***** ***** ****
Chapter 9 · 0% Book details