← Book details Amani Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 13

Sashe 2

Amani Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ya isa sassan Ummami yana tunanin abubuwan da suka faru tsakanin sa da Amani yan mintunan da suka shige. Mukhtar yace a ran sa kenan gatan iyaye ma wani abu ne mai girma ga dan adam! Da Maimartaba bai bijiro da zancen bashi Sa-daka ba, da bai san ranar da Amani zata yi nadamar halayen ta har da abubuwan data yi masa irin haka ba, don shi har yanzu jikin sa bai karbi ikirarin Amani tana son shi yanzu ba, ya dai ji ta, and he was puzzled, ya dai fi yarda da cewa gudun kishiya ne ya ruda ta. Bai dawo gidan ba ma don baya son ta sake saka shi gaba da kukan ta da fitinar ta, sai lokacin da ya kintata cewa ta yi barci, don baya son ta kuma saka shi a kwana kada tayi saurin samun lagon sa, da raunin zuciya ya wuni yau, sabida kasalar da nadamar Amani da kukan ta suka saukar masa. Sai da ya dauke takun sawun sa kamar mara gaskiya da ya shigo falon da ya raba nashi da nata. Kuma yana shigewa dakin sa ya rufe a hankali har da key, ba tare da Amani ta san dawowar sa ba sam. So yake ta koyi son nasa da gasken gaske, har ta zo tana kewar ganin sa, mai yuwuwa in ta daina ganin sa ta yi kewar sa, don ya ga canji mai yawa ranar da ya dawo daga Burkina Fasso. Amani kamar tayi hauka, ganin har washegari Mukhy bai neme ta ba, ga dakin sa ya rufe da key, ta kasa gane a gidan ya kwana ko aah? Jikin ta ya bata kawai watakila an kawo sadakokin, a can wajen su Mukhtar ya kwana, to a ina aka sauke su bata da masaniya? Kafin garin Allah ya waye in ka ga yar Daddy bazaka gane ta ba, ta zama kamar kudin guzurin da kullum ake yafita yake karewa. Haka Mukhy ya dinga yi mata wannan batan dabon har kwana uku, ko sassan Ummami bata iya zuwa yanzu don ta san sai ta tambayeta me ke damun ta. don Amani bata saba da shiga damuwa ba a rayuwar ta, shi yasa yanzu data sameta ta kasa controlling din ta, gashi in zaa kashe ta idan an tambaye ta meye damuwar ta ta san ba abinda zata ce yana damun nata din sai kewar Mukhy. Tunda ta ajiye damuwar sadakokin sa aside, ta bar musu shi, amma hakika rashin ganin sa (for good three days) dinnan yana azabtar da ita yadda bata zato a zuci da ruhi. Da tunanin ta na yana can tare da sadakoki yana shan shagalin sa, shiyasa ta daina ganin sa a sassan ta kwata-kwata. Baba Sahura kuwa in ta zo bata ko bari su yi doguwar magana zata ce ta kyaleta ta, ta tafi gunUmmami don Allah, bata son dogon surutu irin na Baba Sahura. Hatta Sugra da Tahirah sun san uwardakin su ta shiga yanayi, ta ce kada ta kara ganin kowaccen su a gaban ta in ba ita ta neme ta ba. Baba Sahura sai dai ta yi dariya, ta ce, ai wato shi Allah haka yake alamarin sa, duniya rawar yammata wai na gaba ya koma baya. Amani ta zama daga kwanciya sai kwanciya bata umh bata umh umh, domin ta gama gayawa ran ta an kawo sadakokin nan, an basu wani gidan, Mukhy yana can tare da su. Da safe Baba Sahura ta shigo dakin ta don taga lafiyar ta yau da safe, ta same ta ta hada kai da guiwa tana kuka tamkar marainiya, haushi mai tsanani ya kama Baba Sahura, sai ta kada kai ta ce, lallai, aure mai ladabtar da mace, Uwa duk kin yi sanyi kamar ba Tafisun Alhaji ba, kin koma talalabuwa, yo idan ma Sadakan ne aka kawo ai ba ta haka zaki gabza da su ba, tsaf kina nan kina wannan doloncin zasu janye shi, ke kina nan kina cika bokiti da hawaye, ai ta shi tsaye zaki yi ki zama kamar Ummami wajen karawa da kishiyoyi komin yawan su, in ya so mai karfi da iya kissa da iya gado da iya kula da miji ta kwata. Ba miji irin Maina ake sakarwa kwarkwarori a koma gefe ana kuka ba, ni wallahi duk kin zama sullutuwa, wannan karfin ikon naki da izzar taki duk sun bar ki, a irin wannan lokacin kuma suna da amfani, ni nafi son Tafisu ta baya ba ta yanzu ba da namiji ke neman kassarawa. Sai ta ji tamkar Baba Sahura ta yi mata allurar sanya kuzari, da gaske kishi da soyayyar Mukhtar ke neman kashe ta a tsaye in tayi wasa, ya gama narka Tafisu ya gama kashe lagon ta da soyayyar sa, shi bai san ma tana yi ba, yana can yana murzar kuruciyara sa da kyawawan yammatan abzinawa har biyu. Shin da soyyar sa da ke cin ran ta, da kishin Mukhy da ke azabtar da ita zata ji ko da bakakaen maganganun Baba Sahura na yau daban na gobe daban? A wani bangaren, ga kuma kwadayin son ganin fusatattar kyakyawar fuskar sa da ke addabar ta a yanzu. Don haka yau Tafisu ta kwarara zuciyar ta, ta kuduri aniyar ko zata kwana a zaune zata hana idon ta barci zata yi hakan, don ta bincika ta ga inda Mukhtar ke kwana. Aka ce sa kai ya fi bauta ciwo. Kuma shima wani ikon Allah yau ya kasa yin daren da yake yi a gun Ummami don kan sa ciwo yake yi kadan-kadan, kuma shi kan sa ya gaji da boyon da yake yi mata don yana takura kan sa a daki ne, domin ya gane wahalar da yake baiwa zuciyar sa ba kadan bane, ko ya ki ko ya so, yayi kewar kyawawan idanun Tafisu, masu kama da kwan zabo, koko dan itacen nan na almond. Murmushin ta da bata fiya yi ba sai wuri ya kure, da takun tafiyar nan nata mai kama dana macen Dawisu don rangaji da iya takun tafiya mai daukar hankalin namiji. Mukhy ya sa hannu ya rike kan sa da ke sarawa tamkar zai rabe gida biyu. Ya ce. Wash! Ummami ta juyo tana tambayar shi lafiya kake rike kai? In barci kake ji ka tafi ka kwanta mana? Nima yanzu gun Mai zan wuce, kwana biyun nan na rasa gane kan ka, duk ka bi ka hanani sakat da binbini, duk inda nayi sai ka bi ni cikin gidan nan Maina kamar yaron goye? Ni ina matar ka ne ma kwana biyun? Itama na daina ganin gilmawar ta a sassa na sai kai uban yan binbini, bita zai-zai. Mukhy yayi murmushi bai ce komai ba yana kara dafe kan sa da ya kara sarawa. Na rasa dalilin da yasa kake yin dare yanzu a waje na ko wajen Mai, kai da aka ajiyewa amarya ko sati bata rufa ba, amma sam baka dokin ta, anya Maina? Lafiya?. Murmushi ya sake yi kadan, ya ce Ummami ai kanwa ta ce wane irin doki kuma? Ni kanwa nake yi da ita, ba amarya ba. Tun daga nan Ummami ta ke fahimtar wani abu is fishy a tsakanin su a kwana biyun. Ta fahimci tun ranar da aka yi zancen sadakoki ne Amani tayi mata batan dabo. Don itama Tafisun kwana biyu da ya tsiri shigowar ya jima mata a sassa har wani lokacin yayi barci ya farka, ita kuma ta daina shigowa kwata-kwata. Baba Sahura dai ta tabbatar mata Amani lafiya take, shakiyancin ta ne ya motsa ko kofar falo ta daina fitowa. Ta kori su Sugra ma. Ya shiga gidan sa ko in ce bangaren sa cikin jin ciwon kan na karuwa masa, shi kan sa ya san akwai matsala a tare da shi yau, don duk dauriyar sa ta kare, da gaske daurewa kawai yake amma tunanin Amani da yake kwana da shi yak e tashi da shi da son kasancewa da ita ko sau daya ne a rayuwar su, ya fara haifar masa da rashin sukuni a cikin jikin sa, zai ratsa ta falon karshe wanda a nan dakunan barcin su suke, ya ga Amani zaune firgai-firgai tana dakon jiran shigowar sa, ta ki shiga dakin ta balle ta kwanta, ta yi rantuwa yau sai ta ga gadon barcin Mukhy da sadakokin sa. Sai ya sa kai zai wuce ta ba tare da ya ce mata komai ba, but hes touched da ganin yadda ta rame ta yi zuru-zuru kamar ba yar gayun nan Amani Faskari ba, hakan ya taba zuciyar sa sosai, kuma hakan yasa nan take ya tuna Alhaji, da yadda yake lelen abar sa, sai ya ji kamar baya kyautawa abinda yake mata, kamar yana cin amanar Alhaji Usman, duk da haka har yau Amani bata yi hankalin da yake so ba, shi kuma in har ba ya tabbatar da canzawar ta da halayen ta da baya so, ko da ba duka ba, tunda ance hali zanen dutse ne, amma a kalla ta cire wanda Allah baya so (girman kai), izza da fariya da tunanin ta na ta fi kowa, yana so ya tabbatar da cewa tana mishi so na hakika na fisabilillah irin wanda zata sake da shi a shimfida da zuciyar ta da gangar jikin ta bakidaya, ba don shaawar gangar jikin ta na yar adam ba, sai don so da kauna na domin Allah, sannan ne zai iya sakin jiki da Amani su fara rayuwar da yake musu tanadi shi da ita. Makeken Gadon sa ya haye ya kudundune yana amsar zafin da jikin sa ya dauka, jikin sa har yana rawar dari, domin tuni zazzabi ya kawo masa hari, ya ja bargo ya kudunduna har kan sa. Amani duk da bai kula ta ba, ya wuce ta ne a zaune sai bata yi kasa a gwiwa ba wajen biyo shi dakin, ta yi saa bai saka key din ba yau, don bai san inda kansa yake bama, amma kuma bata ga wata sadaka a dakin ba sai shikadai. Amani har da sauke wata lafiyayyar ajiyar zuciya, rigimar da ta shigo da ita ta nema ta rasa, ko don irin kwanciyar da taga Mukhy yayi da kudunduna cikin duvet kullihin sa ko AC bai kunna ba. Sai jikin ta
Chapter 2 · 0% Book details