← Book details Amani Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Amani Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan ta ce wa Tarha ni dai kin ganni ban sani ba!.
Ya gaida Haj. Tarha dake fita, sannan ta wuce. Ya zauna a kujerar da Tarha ta tashi yana cewa,
Ummami ki yi hankali da ita fa, ni bana son kirkin Haj. Tarha sam, duk kudin goro nake musu ita da Haj. Ummu Aymana, ban yarda da ita ba, na bi kirki da gudu na tattake ba takalmi a kafa ta.
Ummami ta yi dariya ta ce lallai Maina ka ji Hausa a Katsina, kada ka damu, Tarha ba irin Ummu Aymana bace, akwai dai kishi wanda dole ne a tsakanin mataye da ke auren miji guda, amma bata da mugun nufi a kai na, sannan tsakani na da kowa a gidannan hasbunallahu waniimal wakeel.
Bana tsoron kowa sai Allah, kai dai ka rike Allah, sannan ka rike sallah, ka kuma rike addinin ka da imanin ka, wallahi kai da kowa sai gani sai hange.
Mukhtar ya gamsu da bayanin mahaifiyar sa, ya zauna dab da ita kamar zai shige cikin ta, yana fadin na gaji da yawa Ummami, mulkin alumma ba abu ne mai sauki ba, ina matukar ganin kokarin Mai, bawan Allah!
Ni kuma yanzu ga matar gidan can kuma ba lafiya na kasa gane kan ta.
Ummami ta sakar masa harara ta ce fita ka bani wuri kada surutun ka ya tashe ta, da kyar ta samu barci Mukhy ya ce wa kenan? Tace ita wadda kake zance barci take yi? Kuma a cikin dakin ki? Mukhy ya tambaya da mamaki. Ta ce eh mana, me ye da dakin nawa da bazaayi barci a cikin sa ba? Ba haka nake nufi ba Ummami? Ita bata da daki ko me?
Ummami ta mike tsaye ganin ya fara fusata, ta kwantar da murya ta ce Ka kyaleta don Allah Maina, har kayan ta ta hado ta dawo nan, na lura bed rest take so ta yi, duk da dai batace min komai ba.
Mukhtar sai ya mike tsaye yana cewa yau nake jin abinda ba zai yiwu ba Ummami ta ce ya yiwu ya gama, baka ganin bata da lafiya ne? Na tabbata matsanta mata kake Ummami ko suma take tana farfadowa bazan iya kwana ni kadai ba.
Umami ta ga ran sa ya soma baci, sai ta ce to Tarha da take so a tafi Guinea da ita wajen Saadiya ashe bazaka bari ba?
Ya ce what! irin yadda ya tsorata abun saida ya baiwa Ummami dariya.
Kai tsaye ya wuce dakin Ummami ita kuma sai ta dauki mayafin ta ta bar musu dakin kada a yi abun kunya a gaban ta.
Tana jin duk abinda suke fada domin lomomin tuwo take kaiwa bakin ta a lokacin, wani na bin wani, Mukhy ya bi abinda ta ke ci da kallo ya ga tuwon dawa ne da yaji kanwa da wata bakar miya, duk dakin ya cika da warin daddawa, yana toshe hanci ya ce.
Halan AMANIE baki da lafiya? Halan something is fishy with you? Whats this annoying smell for?
Amani ta ajiye kwanon tuwon, ta hau side hannu, sannan ta daga robar ruwa ta kai bakin ta ta shanye tas, kamar Giwa, ta daddage ta saki gyatsa mai ban haushi, Mukhy ya rasa inda zai sa kan sa da wannan sabuwar Amanin mai matukar ban haushi da takaici, yaushe rabon yayi magana ta yi masa banza!
Tashi kiyi brush mu tafi muyi wanka mu kwanta haka don Allah, na debo gajiya tausa nake so kimin yanzun nan, kin ji Amani-Amani na?
Ta russunar da idonta kasa ta ce ka yi hakuri Ya mukhy, ba inda zani gaskiya, na dawo nan kenan. Mukhtar ya soma shaqa, sai ya juya kawai yana cewa to babu laifi, bari in je in yi changing, sai in dawo da filo na nan, mu kwana tare a gadon nata.
Ta dauka wasa yake yi, amma ba jimawa sai gashi ya dawo cikin fararen kayan barci riga da wando masu kauri a jikin sa samfurin Blooming Dales, yayi wanka ya kara yin fresh da shi, har da turaren sa da ya san yana jan hankalin ta da shi wato Azzaro Visit ya fesa, ya taje sumar kan sa tayi lub gwanin shaawa duk dan ya ja hankalin Hajiyar tasa ta ta yarda ta bi shi, yana shigowa ya jefa filon a gadon Ummami, ya haye yayi kwanciyar sa yana danne-danne a wayar hannun sa.
Amma sabanin baya da hakan ke tasiri a tare da ita, ta isa gare shi da kan ta, ta ce Ya Mukhy me kake so? Shi kuma yace message ko Amani. Don a irin wannan yanayin ko Mukhy bai yi magana ba ta san yana gayyatar ta ne, daga messaging bata sanin sanda yake zarcewa.
Amma sabanin sauran renakun na baya, yau matukar haushi Mukhy ya bata. Ta zaro idanun ta waje tana fadin.
Ya Mukhy! Ka rufa min asiri ka tashi, gadon Ummami ne fa ya ce ko na Mamma Jalan ne, in baki tashi mun tafi ba nima a kai zan kwana, ta yaya karfi da yaji kin hana min karbar kwarkwara yanzu zaki bullo da wannan yaren da ban gane masa ba?
Kunya da tsoron kada Ummami ta zo ta gan shi kwance a gadon ta duk ya addabe ta, ta shiga rokon sa Allah Annabi ya tashi, kada Ummami ta ce basu da sauran kwalli a idanun su.
To ki tashi mu tafi, tunda ke kina da sauran kwallin a idon, sarkin masu kunyar suruka, ba kuma rokon ki nake ba umarni ne ki tashi mu tafi.
Kamar ta fashe da kuka ta ce wallahi na gaji, Allah ya gani yanzu bana so, kai abinka babu hutu sam? Ko inji wani zubin ai yana bukatar hutu balle mutum, ni yanzu ba sadakoki biyu ba, in ma su goma da mata uku zaka karo, bisimillah, ga fili mai doki, don kaga bana so ne kake amfani da hakan kana uzzura min, to na baka dama yanzu Ya Mukhy ka karbi Sadakoki as much as you like.
Mukhy yayi sakale! Daga kwance yana jin ta, yana mamakin ta, yarinya kamar mai hawainiya, rana daya daga yin amai duk tabi ta birkice tana masa tutsu, in ya ce gaban sa bai fadi ba da wadannan kalaman nata ba ya yi karya, don kamar ta daina son nasa kenan.
Kenan ta daina damuwa da shi ko watanni biyar basu rufa suna amarcin ba.
Shi kuma yanzu ne ma ya fara so da dokin Amani ta kasance tare da shi, sakamakon niima irin ta mace mai yaron ciki da ta fara saukar mata.
Murya na dan rawa, Mukhy ya ce ki yarda mu tafi, I will not force you kin sani, I will never force a woman to sleep with me, ni ba wasu Sadakoki da nake so yanzu, ONLY AMANI- I LOVE!
Ki tambayi Ummami ki ji tuntuni na ce ta gayawa Mai bana so, bana bukata, matata AMINA ta ishe ni rayuwar duniya, domin ta fi min goman su.
Hawaye take yi sosai, amma kalaman sa na tasiri sosai a ran ta, sun sa ta jin kan ta ya kumbura, ta ji ta a Tafiun ta, kamar tana yawo a kan gajimare.
Ni bana so ne kana zuwa inda nake yanzu, Kiss din ma dana ke cewa ina so, kana min yanga a kai to yanzu bana so, barci kawai nake so in yi ta yi, kada a tashe ni!
Ta fada da iyakacin gaskiyar ta, tana kaucewa kaifin idanun sa. Yau Mukhtar yana ganin ikon Allah, da kyar ya ce Ni Mukhtar dan Issouffou Massaoudou, na yi alkawarin bazan kasance da mata ta Amani a daren yau ba, sai bisa yarda da amincewar ta.
Amma ai ina gani kana toshe hanci da ka shigo, wato doyi nake yi ko? Ta kara fashewa da sabon kuka.
Ni ban ce kina doyi ba, dakin ne ina shigowa naji yana wani wari-wari da ban saba ji ba tuwo na ne fa, kuma ni yanzu shine abinci na, kada in je gidan ka ka ce kuma na kai maka wari gida kuma to yanzu saboda Allah Amani, me kike nufi?
A wane dalili ina da mata ta a cikin gida na zan yi kwanan gwauranci? Ai ko ban ce ban yafe ba, Allah zai saka mini sau sabain, tun da na lallashe ki na kuma yi miki duk alkawarin da zan iya kin ki ji.
Ya mike yana cewa. Since you insist, do as you wish.
Ya dauka ganin bacin da ran sa ya yi muraran, zai saka ta biyo shi, amma har dare ya tsala bata ba alamar taita a lokacin ma ta kai Zaria a barcin ta har da minshari na kwanciyar hankali da hutu.
Kwanan kadaici da damuwa yayi, sai yanzu ya san yayi mugun sabo da Amani yadda baya zato, kuma ta shiga ran sa yadda baya tsammani. Bai san yana son Amani har haka ba, bai san soyayyar da yake mata ta yi wannan zurfin ba, sai yau da duk inda ya mirgina babu ita sai filin ta a gadon barcin su, ya rasa kulawar ta a gefen sa, da nacin ta na son yayi kissing din ta, ko saukar numfashin ta a kunnen sa yau bai samu ba, wanda hakan yasa Mukhy yayi kwanan wahala ba yar kadan ba.
Yayin da Amani tayi barcin ta cikin salama, don koda Ummami ta dawo dakin bata ko tashe ta ba, don ta gane da gaske tana bukatar hutun.
**** **** ****
Chapter 11 · 0% Book details