← Book details Amani Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 13

Sashe 3

Amani Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi dan sanyi, kuzarin balain data shigo da shi yayi kasa sosai, ko daga irin kwanciyar da Mukhy yayi yau zaka fahimci bashi da lafiya. Farar rigar barci ce a jikin ta iya guiwar ta mai santsi, amma ta daura zanin atamfa a kai, gashin kan ta ma duk ya susuce babu taza, babu kitso, tafi dacewa da a kira ta da birkitacciya Amani yanzu ba yar gaye Amani Faskari ba, sabida yadda ta koma sam ba nutsuwa da walwala da farin ciki a tare da ita, duk a dalilin rashin samun kan Mukhtar Issouffou Massaoudou. A lokacin da zuciyar ta ta afu a kan sa, da son ganin su a wani matsayi na cikakkun mata da miji cikin kauna da soyayya kamar kowadanne maaurata, ba wannan matsayin da suke kai a yanzu ba, kamar dai Mai Diffa da Ummami, kai bazaka ce sun tsufa ba, kullum cikin kaunar juna da tattalin juna suke, da ka zauna da dayan su sai ka ji ya ambaci dayan a cikin zancen sa na koyaushe, ta hanyar bada misali da kyautatawar da dayan su ke yi masa. Yadda son Mukhy da kishin sa suka taru suka sukurkuta Amani sai ta koma kamar ba yar gayun nan kuma yar kwalisa (wanke hannu kafin ka taba) da ya sani a gidan Hon. Usman mai suna Amani Usman Faskari ba. Amma yanzu kam fama yake da kan sa da ya tambaye ta dalilin wannan ramar haka, da dalilin susucewar ta, to ko magana baya son yi, ya rasa dalilin wannan masassara data same shi yanzun nan, jikin ta duk yayi sanyi da yanayin da ta gan shi a ciki na rawar dari don bata taba ganin sa cikin irin sa ba, sai ta zauna a gefen gadon jikin ta ya dau rawa itama, murya a sanyaye kuma tana yar rawa ta ce. Ya Mukhy are you alright? Why are you shivering?! Ya ce umh cikin karfin hali, sai ta zauna a daidai kan sa ta ce. Na ji dadi yau ka dawo da wuri, amma kamar baka da lafiya sai itama ta soma karkarwa, ta tambaye shi da me zan iya taimaka maka? Akwai magani a dakin? Ya sake cewa umh da murya irin ta mai jin zazzabi, Amani ta gama firgita, ta yi kwanciyar yan bori a kusa da Mukhy don ta gane ba kalau yake ba, ko ta hanyar saukar numfashin sa da ke sauka a kai-akai cikin hucin zafi, don haka ta ji ta kasa korafin ina yake kwana da ta so yi, ko tambayar sa an kawo masa kwarkwarorin ne ta daina ganin sa yana kwana a nan? Maimakon hakan, sai ta samu kan ta da cigaba da nacin tambayar sa Yaya Mukhy, don Allah da me zan iya taimaka maka? Kwarai a wannan yanayin yana bukatar taimakon nata, amma kuma... Im not well! Ya bata amsa da kyar, ta kara matsowa daidai kan sa, bakin ta tasa daidai kunnen sa ta ce me yake damun ka Ya Mukhy? A gajarce yace sanyi. Amani sanyi nake ji, wani irin sanyi har cikin bargo na, duk da na rufa, amma kamar ina ciki kankara still, ko dai mutuwa zan yi? Amani ta kara gigicewa ta mike a sukwane to bari in kashe maka A/Cn, ta mike da niyyar tafiya kashe AC sai taji Mukhtar ya riko ta da hannnun hagun sa da ya dauki dumi da karkarwa, ta juyo ta dube shi idanun ta sungama kwalalowa, cikin karkarwar jiki ta tsaya, domin gabadaya ta rude ta rasa abin yi, sai ta ji muryar Mukhtar a hankali yana fadin. “Amani sammin dumin jikin ki, it wil be absolutely okay for me. Ta so ta gane me yake nufi wato dumin jikin ta yake so, shi kadai zai taimaka masa ya samu rangwamen sanyin da yake ji, amma da ko kusa bata kawo hakan a ran ta ba kuma a rude take, sai bata gane me yake nufi din da dumin jikin ta ba, don haka ta tsaya tana dawurwura, sai ji ta yi Mukhy ya ja ta a hankali ya kwantar, ba tayi musu ba ta bi umarnin sa, sannan ya daga bigilar rigar jikin nata ya cire ta ta sama, ya warware zanin jikin ta da kyar cikin rawar hannu ya jefar da shi a kasa, da wata irin azama Mukhtar ya manna Amani a jikin sa, wuyansa da sajen fuskar sa cikin nata wuyan. Ya kuma kudundune su cikin bargon tare. Wato su sha zafin zazzabin tare. In ma mutuwa zai yi, yana fatan ya mutu manne ciki jikin ta.. Ko hakan ya sa su tashi tare ranar lahira a matsayin mata da miji, tunda a duniya Allah bai yi zasu rayu tare ba. Kusan zafin jikin Mukhy jikin Amani ya dinga komawa, irin yadda ya mannata a jikin sa ya sa komai nasa ya fara sauyawa, hatta saukar numfashin sa ya sauya, Amani ta samu kan ta da kara rungume Mukhtar, suna raba zazzabin nasa tare. Duk da cewa kuwa ba karamar wahala take sha ba, ga zafi kamar ya kashe ta. Sai tsakar dare suka samu zazzabin ya soma sauka, ta gane hakan ne da yadda ya soma yanka gumi yana jika ta, amma hakan bai sa Amani ta tashi ba, duk kuwa da cewa ba barcin take yi ba ita har tsayin lokacin. A yau ji take wata irin nutsuwa na shigar ta, kasancewar ta cikin wannan intimacy din na body contact tsakanin ta da mijin ta Mukhtar Diffa, soyayyyar Mukhtar da wata gigitacciyar kaunar sa na kara ratsa ta, yanayin jikin ta ya soma sauyawa itama ta kara kankame shi, shi kam zuwa lokacin ya samu barci mai nauyi, sai ta kara manna shi a cikin jikin ta, tana fatan su dawwama a haka. Tana fatan kada gari ya waye. A haka suka kwana, da asubah Mukhy ne ya fara tashi da kyar ya raba jikin sa da na Amani saboda yadda ta bi ta makale shi cikin jikin ta, wadda ya gama jikawa da gumin jikin sa jagab, ji tayi kamar ta rike shi ta hana shi tashin, don ta fi so su dawwama a haka. Mukhy ya je yayi wanka da ruwan sanyi kana ya dauro alwallah ya fito, yana mamakin abinda ya same shi jiya kamar farfadiya kamar bugun aljannu, ita sai a lokacin ma ta samu barcin ya zo mata. Mukhtar ya soma kokarin tuno abinda ya faru da shi a daren jiya da mamakin ganin Amani kwance a kan gadon sa, don ya manta ma yadda aka yi ta shigo tsabar yadda zazzabin ya buge shi jiya. Amani ta ji alamar tsayuwar Mukhy a kan ta don haka ta bude ido tana kallon Mukhtar a hankali da idanun ta da ke cike da barci, shima yana kallon ta da kyawawan idanun sa yana kara son komai nata, mace kamar ita tayi wa kanta halitta komai nata mai ban shaawa ne da daga hankalin da namiji. A hankali ta lumshe idanun ta cikin nasa, tana jin karin son sa a ran ta, sai hawayen suka dirgo marasa dalili bare madafa. Mukhtar ya dauke kai kamar bai ga hawayen ba, ya kada kai ya wuce ga sallayar da yake sallah a kai, ya ce mata. Tafisu ki tashi ki sallah haka!. Daga kwancen da take ta ce ciki raunin murya Ya Mukhy ka yafe min? Na yarda banida kirki, na yarda bani da hali, na yarda ban fi kowa ba, na yarda wanda yafi kowa shine wanda yafi kowa tsoron Allah, na tuba na bi Allah na bi ka! Kada ka sake tafiya ka bar ni, I promised to become a changed person. Muryar Mukhtar wannan karon cikin jin dadi da tausayi. Ya ce cikin kwantar da idanun sa a kan ta. Kiyi sallah Amani, sai ki zo mu yi magana ta fahimta, bana so wannan ramar da kike faman yi, kin ji? Gayun ma duk kin daina, haba Tafisu ni ina son gayun ki fa!” Dadi ne ya kama ta, tana son tashi amma ta kasa janye bargon daga jikin ta, sabida rigar ta da Mukhy ya cire cikin zazzabin da ya makanta shi jiya. Daga ita sai bra da panty din ta. Cigaba da kwanciyar tayi har sai da ya tada sallah, sanan ta yi maza ta dauki rigar barcin ta ta maida amma bata daura zanin atamfar ba, ta wuce nata dakin don ta shirya sosai. Sosai ta zauna ta cancada kwalliya, gayu iya gayu, cikin wani (swiss lace orange colour) da aka yi wa dinki riga sa da siket matsatstsu, ta fesa turaren ta na dindin watau Elizabeth Arden. Ta yi alkawarin yau ko kofar gida bazata bar Maina ya fita ba, jinyar sa zata yi da tarairayar abun ta, in an neme shi zata ce ai bai da lafiya, sai ta tabbatar ta wanke duk wata tsatsar ta dake ran sa, in dai ta amsa suna Amina-Amani, Aminatu Mamar Manzo, ba wai sauran mata ta rako duniya ba kamar yadda ake goran ta mata ta koina. Zata gwada nata diyaucin na ya mace da kissar da ake cewa da ita aka haife kowaccen mu. Amani ta yarda za ta bada hakuri yau, ta duk hanyar da zata iya da irin nata baiwar da Allah ya yiwa kowacce diya mace. Ta koma dakin nasa ta same shi ya idar da sallah ya koma ya kwanta don jikin sa ba karfi. Hidima sosai take ta yi da shi yana daga kwance yayi dai-dai wai bayan sa ke ciwo, hatta tea yau har kan gadon sa ta hada masa ta kuma bashi da cokali a baki, har sai da ya ture ya ce ya ishe shi. Amani ta koma taga an shirya musu kalaci kala-kala ta zubowa Mukhy farfesun koda da hanta ta kawo masa, ya ce na koshi fa, bani dai magani in sha, sai kiyi min tausa a bayan nan, duk jikina ciwo yake, akwai first aid box a cikin drawers din can, duba ki dauko min paracetamol, Ta yi yadda ya umarta, ta dauko maganin ta ballo biyu ta hado da gorar ruwan Faro mara sanyi ta kawo masa, a baki ta saka masa maganin, sannan ta kafa masa gorar ruwan a baki ya hadiye. Shi da kan sa bai
Chapter 3 · 0% Book details