Sashe 12
Amani Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Washegari da ya zo gaida Ummami, ya maka bakin glass don boye kumburin idanun sa da launi da suka canza irin na rashin barci, yana ta cin magani, kuma har suka gama hirar da zasu yi da Ummami bai yi korafi akan Amani ba, ya barwa ran sa, mai nufin ya yi fushi da ita.
Ita Ummami ce da kanta ta fahimci hakan, don haka sai ita ce da kan ta ta dauko zancen Amani, inda ta ce masa cikin lallashi.
Maina sai ka yi hakuri da Amani yanzu, a lokacin da mace ke da yaron ciki ta kan samu sauye-sauye a jikin ta, wani zubin har da na halaye da dabiu, sakamakon halittar da ubangiji ke yi a mahaifar ta.
Wata kuma tsanar mijin take gabadaya, ta ji bata so ya zo inda take, wata kuma kamshin jikin sa ma bata so sam.
Abun daban-daban ne (from one woman to another), ka yi fatan Allah ya raba su lafiya kawai, kai kuma ka jure na dan lokaci ne, in kuma a kawo sadakokin toh? Sai in yi wa Mai Diffa din magana.
Mukhy ya rasa a yanayin da kwakwalwar sa ta karbi zancen Ummami, idan ya fahimta daidai, to Amani juna biyu gare ta kenan shiyasa take masa tutsu? Allah da girma yake. Wannan wane irin rantsatstsen rabo ne na gaggawa haka daga Allah! Burin Alhaji Usman zai cika, cikin dan lokaci kalilan na hada zuria tare da shi, Ummami da Mai zasu samu jikoki daga gare shi tun suna raye da sauran karfin su. Tsakanin Hon. Usman da Mai Diffa, bai san wa zai fi farin ciki da wannan kyakkyawan albishir din ba. allah abin godiya.
A lokacin Maina ji ya yi son Amani na ninkuwa a ran sa, kamar yau ne ma ya fara koyon son nata. Bacin ran ta da ya kwana da shi yana tafiya daga makogaron sa yana narkewa.
Mukhy, ya lumshe idanun sa a hankali, ya samu kan sa yana tambayar Ummami ko sai zuwa yaushe ne Amani zata iya koma masa daidai ta daina sababbin dabiun ta da ke ci masa rai haka?
Dariya Ummami ta yi, ta ce ya danganta, mai yiyuwuwa in cikin ya cika watanni hudu ko biyar. Mukhy ya mike tsaye cikin daburcewa ya na cewa.
Ummami, ko dai wata kasar zamu tafi ta ga kwararren likita? Ummami ta ce babu inda zaka dauke ta da karamin ciki jirgi ya jijjige shi, don babu wani likita da zai mata maganin wadannan abubuwan sai lokacin tafiyar su ya yi, babu inda zaku, har sai Allah ya sauketa lafiya don ga dukkan alamu, cikin Amani mai tsirfa ne, in ka dauke ta kuka tafi wani wurin ina zaka nemo mata ire-iren abubuwan da take son ci din nan?
Suka saki wannan hirar suka cigaba da wata hirar daban, amma dai Mukhy ya saki fuska ba kamar sanda ya shigo ba. Daga bisani Amani ta fito falon, ya bita da kallo tana zama daga kasan kafafun Ummami, Mukhy ji yayi kamar ya ciro cikin daga jikin ta ya ajiye a nasa ko Amani ta samu lafiya su cigaba da rayuwar su mai nagarta yadda suka saba.
Ummami sai ta tashi ta fita cikin gida ta bar su a falon. A sanyaye ta ce, Ya Mukhy ina kwana? An tashi lafiya?
Ga dukkan mamakin sa sai ya ji baya jin haushin ta yanzu, sai tausayi, ya tausasa murya ya mika mata hannu, yana mata kallon rahma da kulawa, yace ta shi mu tafi kawai, duk abinda baki so na daina, in ma ya kama mu raba daki sai mu raba, amma (for now) ban iya zama a gidan nan ni kadai.
Sakamakon yadda ya sa idanun sa cikin nata, ya kuma tausasa harshe sannan ya bata hannu, sai ta kasa tankwabe tasirin wannan soyayyar da sadaukarwar, tunda har ya yarda in ma daki zaa raba a raba, shi dai kawai ta kasance cikin gidan sa, don gani tayi ya fi ta zama maraya a kwana daya kacal, duk da gashi a dakin mahaifiyar sa.
Sai kawai ta juya ta soma hado kayan ta da ta kwaso, ta fito da su rie da jakar tana kiran Tahirah, Tahira da dam aba wani nisa suka yi ba suna falon da suke zama su jira ta ta zo da sauri ta amsa ta yi gaba da su, Mukhy ya saka ta a gaba suka kama hanyar komawa gidan su.
Baba Sahura ma yau sai komawa tayi sassan Ummami da zama, da ta zo ta tarar sun rufe sassan su da safiyar Allah. Su Sugrah ma duk sai wajen Ummami suka koma gabadayan su, wai Maina da kan sa ya ce musu su tafi sai ta neme su.
**** ***** *****