Sashe 7
Amani Part 4 Complete Hausa Novel · about 5 min read
a sanyaye. Yaya Mukhy, wanda ya sake cutar da wani tsakanin mu daga yau, koda da zazzafar magana ne, ko maganar da dayan mu ya nuna baya so, bayan mutual understanding din da muka samu yau, and forgiveness to each other, ina rokon Allah ya bi masa hakkin sa a kan dan uwan sa!. Sai kuka. Juyawa yayi bayan ya ajiye mata maganin akan bed-side din, jikin sa ya dan yi sanyi da jin kalaman ta, ya yarda da gaske Amani bata son maganar sadaka. Ai kuwa shi maganar yanzu ma ya fara domin ya samu makamin yakin sanya Amani ta yi masa abinda yake so a duk lokacin da ya ga dama da barazanar Sadaka, ba don wai ya yanke a ran sa zai karba ko ba zai karba ba. Ganin kukan da take bilhaqqi take yin sa, sai ya koma lallashi To shikenan, ki yi hakuri Sweetheart, idan na daina maganar Sa-daka, kullum sau nawa zaa yi mun alfarmar? Kafin in fita fada, da bayan na dawo? Kin ga ke din Sweetheart dina ce bana gajiya da rabar niimar da Allah ya yi miki, ga ki Sweet 16 Amanin Mukhy, Allah da ya halicce ki ba da kyawun sura kadai ya bar ki ba, daga sama har kasa har ciki Amani Tafisu ce, Tafisu ba dai abunnan ba. Ya karasa da rungumeta sosai yana kissing idon ta da suka yi narai narai da hawaye, ta ce ko sau nawa kake so Ya Mukhy, ko zan mutu zan amince, in dai zaka bar maganar sadaka. Sai Mukhtar yaji wani dadi a ran sa, ya riko hannayen Amani cikin tafukan sa, ya kai su ga fuskarsa suka tallafi lallausar sajen dake kwance a kowanne gefe na fuskar sa. Balle ma bazaki mutu ba, sai dai hakan ya kara min son ki, sannan ki yi ta suburbudo min yaya ina kara son ki da kaunar ki, ina kara kula da ke Tafisu. Ke din wata mutum ce mai daraja a waje na saboda ALHAJI! Wadda komai tsayin lokaci da canjin da zamani zai kawo, ko tsufa, ko canzawar halitta saboda shekaru ko girma da ya same mu, ko wani abu makamancin hakan, bazan taba iya wulakantawa ba. Daddyn ki mutum ne da bazan taba manta alkahirin sa a rayuwa ta ba. Don haka zan kula masa da tilon Tafisun sa, in adana masa ita a daki na ni kadai, in mayar da ita TAFISU TA GASKIYA, amma ba da komai tawa Tafisun zata fi sauran mata ba sai da nagarta, kyawun hali da rikon addini, kula da miji da iya soyayya ga mijin auren ta, da kuma iya kula da yayan ta da iyayen ta. Kalaman sa sun kashe Amani don dadin su a ran ta, Mukhy ya daina ce mata shashasha, ya yarda ita din, ba ballagaza bace. Idon ta fal hawaye ta dube shi da dukkan kauna da soyayya a kasan idanun nata, ta soma magana cikin rauni murya. Na san bazan ce ina son ka ka yarda ba yanzu Ya Mukhy, na san na makara, bazan ce maka tuntuni ba kin ka nake ba, kishin yadda Alhaji ya fifita son ka a kaina ne ya sa nake kyarar ka ka yarda ba, bazan ce maka a kasan raina ina yawan yaba surar ka da a fili nake kushewa ka yarda ba, don na bar baya da kura mai yawa, bani da say a yanzu da zai yi tasiri a zuciyar ka a kan SO, tunda baki shi ke yanka wuya, kuma maganganu zarar bunu ne. Na fadi maganganu cikin jahilci da yawa, wadanda da inada dama a yanzu, da na mayar da su na hadiye su a ciki na. Mukhtar ban fara son ka don na ga kai waye bane, ko don nasabar ka, ni dai kawai gani nan ne, zan iya cewa tun a Saliyo! Ranar nan. Na fara samun sauyi a zuciya ta a kan ka. Ka yi min rai Ya Mukhy kada ka karba Sadakoki, ba don ni ba! Ta cigaba da matsar kwallah tana cewa duk abinda kake so zan maka daga yau, ko da ya fi karfi na, zan aro karfin a duk inda yake, wani irin kishi ne da ni a kan ka, mai barazanar haukata ni, idan suka shigo. Mukhtar yama rasa me zai ce don dadi yau. Ya shirya tsaf cikin irin kayan gidan su, amma bai nada rawani a kan sa ba. Your actions will prove your words Hajjaju, babu bukatar rantsuwa anan Hajiya Amani, abun nufi, in gani a kasa kawai, Mukhy sama Mukhy kasa ana kula da ni, wato ki cigaba da yadda kika fara yau, saboda ke dinnan tsoro kike bani, sakamakon halin ki na hawainiya yau fari gobe baki, na rantse tuban ki na muzuru ne a yawancin lokuta, ba kya taba tuba don Allah! Sai kin ji wuya. Maganar sa ta so ta bata dariya don tasakanin sa da Allah ya fada. Iya karantar da yayi mata kenan sama da shekaru goma. Halin ta mai wuyar canzuwa ne don an ce hali zanen dutse ne, sai dai ma iya cewa zata rage wasu in aka cigaba da ankarar da ita a hankali cikin kauna da soyayya. Zani gun Mai, daga nan zamu je Dosso nadin sarautar dan sarkin Dosso, probably sai Maghriba zan dawo. Ya juya zai fita, Amani daga kwance ta kira sunan sa, muryar ta abun tausayi ta ce. Ya Mukhy! Ya dakata ba tare da ya juyo ba. Sai ji yayi Amani ta ce. Baka yi min goodbye kiss ba, you know I love your kisses! Mukhtar dai yau duk abubuwan da ke faruwa a mafarkai yake kallon su, amma gara ya zarce a cikin mafarkin nan da dai ya farka daga niimomin dake cikin sa. Murmushi yayi ya daga mata gira da kafada a tare, ya ce cikin dariya. Na ki din! Maana wato ba zai yi goodbye kiss din ba, har da make kafada alamar ya ki, sannan ya fita yana mata murmushin dake neman narka zuciyar ta. Idan wadannan canje-canjen da yake gani a tare da Amani cikin dan lokaci na gaskiya ne kuma zasu dore, baya jin zai yi maraba da wasu kwarori, kowacce mace kazama kuma dukun-dukun zai gan ta a kan Amanin sa. Sai dai ita din Zuma ce sai da wuta, amma hakika Amani ta sanya shi cikin madaukakin farin ciki yau, da yake fatan su dawwama a cikin sa har karshen rayuwar su. ***** **** *****