← Book details Amanata Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 22

Sashe 8

Amanata Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ta kwanta masa ajiki bai san lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ba, har azuciyansa yana son auta ko da aure zatayi ba iya bayar ta ga wani ba don bai son wani yaci Amanar da dad ya basa ko in auta tace bata sonsa to dole ya hakura don ba zai takura ta ba, gwanda ya shiga ko wani irin hali ne da ya sata a damuwa. a hankali ya kara kan kameta a jikinsa wanda sai da itama taji wani shock ya ziyarci jikinta ajiyar zuciya tayi ahaka suka kwana yau kam bacci mai dadi tayi ajikin Ammar wanda rabonta da ta yi tun iyayenta suna da rai, sai da asuba ta mike da ta fiti kofar asibitin in da taga randar ruwa ta diba tayi alwala ta shin fida dan kwalinta tayi sallah, bayan ta idar ne ta zo da ruwan ammar da kyar ya iya tashi sabida jikinsa yayi tsami tana zuba masa ruwan yayi alwala yana kwance yayi sallah don kansa ya masa nauyi. Sai da gari ya waye sosai gurin karfe 9:00 mai gari yazo duba sa da yar kununsa a kwanon sha da kosai nan suka gaisa bayan sun gaisa ya ke tambayan su mai ya kawo su gari da har zasu kwana a kasuwa nan auta ta basa lbr ya tausaya musu sosai, nan ya musu sallama akan darana zai zo dubasu auta haka take kula da ammar dan kudin da malam ya basu shi suke yasan abun da ya dan musu su ci, kwanan Ammar uku a asibiti aka sallamesa jikinsa ya warke sai tabo, ko da suka fito a asibiti gdan mai gari ya nufa ya masa godiya san nan yace yana so su kara gaba don yana son cikin birni inda zai samu sana’a yayi da karfinsa, nan mai gari ya ce yanzi kana fita sai garin bauchi shine babban gari, nan yaji yana son garin don ya dade yana jin lbr garin bauchin yakubu ga Addini ka mutunta mutum ga iya karama baki, ga masa waina sai wanda kazaba, nan yayi godiya mai gari ya rakasu suka shiga motar bauchi. ®WISDOM HAUSA WRITER’S Rash Kardam [7:32PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Mota su ka shiga, a hankali suke tafiya, haka kurum ya tsinci kansa da farin ciki, tun a hanya yaji yana son garin ya burge shi. Auta ma haka abun yake tana gefen Ammar ta dan jingina kanta a kafadarsa, haka kurum take jin sanyi a zuciyar ta, nan ta fara tuna irin rayuwan da sukayi abaya lokacin iyayenta suna raye, ku ina zataje a mota suke tafiya mota mai AC ba hayaniya, amma yau gata a motar kasuwa, Allah sarki yarinyan da taso cikin gata da kulawa ya daya tilo yau gata a cikin gararin rayuwa Allah ya kawo masu sauki Ameen. Karfe goma da minti sha uku, suka iso cikin garin bauchi, driver ya sauke su a waje tashar mota na winti market, nan suka sauka, kowa ya kama gabansa, Ammar ya riko hannun Auta suka bar gurin, titi suka tsallaka suka zo ta gefen stadium akwai dan guri nan suka zauna, kallo daya zakayi ka ga kamanin su auta yanda ya canza sunyi baki ga rama da sukayi sosai. Sun dade a gurin sosai, amma sun rasa inda zasuyi can yace bari yaje ya nimo musu abinci, tace to gefen gun masu sai da jarida da gyaran mashin ya ga mai sai da shinkafa da wake nan ya saya musu roba biyu da pure water kwaya 2 ya kawo musu, haka suka ci sukayi godiya ga Allah ya mayar wa masu shinkafa ya karbi canji ya dawo, haka suka zauna sai da aka kira sallah, nan ya sake saya mata ruwa tayi alwala shi kuma ya tafi masallacin da ke gefe yayi sallah, bayan ya dawo suka zauna hira ya rinka mata yana bata dariya don ya debe mata kewa sabida yaga damuwa a idonta sosai, haka suka yini har dare agun suka kwanta. Da gari ya waye sallah yayi yace ta zauna a gun kartaje ko ina zaije ne man abunyi ko da dako yasamu don su rinka samun abunda za suci da in da zasu zauna, haka ko akayi ya shiga cikin kasuwar winti, haka yayi yawo sosai amam shiru ba lbr aiki sai azahar ya dawo yaje ya sayo musu shinkafa sukaci, bayan sunci tace Yaya na anyi nasara kuwa cikin mutuwar jiki yace ina Allah baisa an dace ba, idonta yaciko da kwalla tana shirin yin kuka ya girgiza mata kai alamar aa, yace ko kin manta Allah yana tare da mu bazai barmu haka ba, kuma duk bakin da Allah ya tsaga bazai hana shi abinci da zaici ba. haka suka sake kai dare nan suka sake kwana. Washe gari ma haka yafita yayi yawo har ya gaji gashi yan kudinsa sun soma karewa saura dari biyar, yau sai bayan la’asar ya dawo dake ya ba ma Auta naira dari don tasayi abunda zataci ko da yadawo yasamu tana bacci akan yar fallen zanin da ta shimfida tausayinta ya kama shi, Allah sarki auta yau itace tamkar wata tsintaciyar mage gwamma shima namiji ne, idonsa ne ya ciko da kwalla a zuciyarsa yake adu’ah Allah ya kawo musu dauki baisan hawaye yana sauka da ga idonsa ba saiji yayi auta na share masa hawaye itama idonta yaciko da kwalla, tace Yaya na sai dayaji sanyi har cikin ransa, mai yasa ka kuka ban son ganin hawayen ka, in kai kayi hawaye wazai rarrashe ni, kaine mai sani farin ciki, Allah gatana kaine gata na, yaya na waya taba ka karkasa kanka cikin damuwa Allah zai kawo mana mafita yana tare damu kaji, kaman karamin yaro ya daga mata kai, tace kayi min murmushi, ammar baisan lokacin daya murmusa ba, itama murmushin tayi ta rike hannunsa tace Ya Allah kaja kwanan yaya na kabani abunda zan saka masa dashi. ®WISDOM HAUSA WRITER’S Rash Kardam [7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Hancin ta ya lakace yace Ameen amma kwanan mu gaba daya, haka suka zauna cikin farin ciki har dare yayi suka kwanta. Da safe ammar ya sake fita nan ma ya barmata kayan karin kumalo ya fita, nan yayi ta yawon niman aiki da kyar ya samu wani shago zasuna debo kaya daga stored suna kaiwa cikin shago amma ba kullum ba sai randa za a saka kaya a shago ko sun dawo daga sari, haka ya dawo da murna yake sanarmata, nan ta tausaya masa tace Yaya na zaka iya yin dako kuwa kai ya daga mata yace eh kan wata, in dai zamu samu abunda zamuci Alhamdulilah. Washe gari haka suka tashi kudin su ya kare sai naira hamsin shinkafa ya sayo ma auta ya zauna yasata a gaba taci, tace aa sai dai su ci tare fir yaki don ba zai ishesu dukansu ba, auta taki ci ganin haka yasa ya dau cokalin roba ya fara bata lbr abun dariya yana bata a baki tana ci har ta cinye , ta kalli kwanon tace kai yaya na gashi kasa na cinye kai ya girgiza mata alamar kar ta damu, haka sukayi ta hira har dare, Futha ce ta fito sanye cikin shiga ta alfarma ta shiga motarta ta nufi makarantar da tafara zuwa, bayan sunyi lectures kenan tafito tana zaune, kiran sady ne ya shigo bayan sun gaisa ta tambayeta kwana biyu tace lfy nan suka taba hira ta hakuri gameda abunda babanta ya mata nan sukayi sallama ta dau ko hanyan gd tun daga nesa ta hango wata sabuwar mota honda ta hadu motar blue kalo daga gidan su Auta tafito wanda yanzu su Sady ne acikin gdn, sai da tazo kofar gidansu ta tsaya don ta karbi lab top dinta da tabada ya duba mata, bayan ta karba ta fito taga wan nan Honda tatsaya dai2 ita nan aka zuge glass wacce ta gani a motar bakara min mamki tayiba da ace itace a wannan motar, pinky ce yar kanini baban Auta wato yar Baba Isiyaka, hy tace mata sai a lokacin ta dawo daga duniyar tunani gaisawa sukayi ya kwana biyi tace lfylau ya school tace Alhamdulilah, sun dayi hira kafin sukayi sallama, futha ta tafi tana tsananin mamaki sosai da sosai pinky ce haka harda mota lalle sun samu duniya tabbas dawata a kasa dole ma tabi didigi haka taja motarta tashiga gida tan tunani kala2. Can cikin dare wani hadari ya hadu ga iska daya taso sosai, Yaff yaff yaff ruwa da iska yasoma zuba, kan kace me sai ga ruwa ya barke baka dan ba, nan Ammar suka farka kafin sunimi matsuguni rua ya soma dukan su bakadan ba duk inda zasu fake ankulle nan suka dun kule a gindin shiya ruwa nan dukansu Auta ta kan kame ammar tana yar kuka ga ruwa sai dukar su yakeyi wani tsawa aka sake sosai wanda yasa Auta kara rugume ammar har sai da yaji tsikar jikinsa ya tashi yaso ya ture ta don yanda yasoma feelings, ga wani murdawan da maranta keyi alamar period ga ruwa na dukan su gaka ruwan ya kare akansu tass barin sanyi auta takeyi ga maranta na murda mata gashi ba kayan canzawa haka suka tsuguna a tsugune har gari ya waye jikinsu har ya bushe auta kam mara ke ciwo gada2 ga zazzabi na neman mata mumunan kamu nan hawaye ya soma zuba don tabbas period dinta ne gashi kudinsu ya kare ga pant daya ke jikinta kayan da zata canza ma baba gashi kwananta 2 ba wanka sai yau da ruwa ya mata duka Yasalam!!! Allahuma ajirni fi musibati wa aklifli khairan minha, jikinta yayi zafi sai barin dari takeyi Ammar ko da ya taba jikinta nan take ya rikice ya shiga da muwa gashi kudinsu ya kare ga auta jikinta yayi zafin Innalilahi wa inna ilaihi raji’un yake furtawa a bakinsa. ®WISDOM HAUSA WRITER Rash Kardam [7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Jikin auta yayi zafi sosai ga ciwon mara, ammar duk ya rude yarasa me ke masa dadi ga kudinsu ya kare gefen wani shagon daya ga ba a budewa yaje ya kwantarta lokacin
Chapter 8 · 0% Book details