← Book details Amanata Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 22

Sashe 7

Amanata Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka dan yi hira kasancewar lokacin damina hadiri ya hadu aka soma iska, dole yasa suka shiga dakunan su don bacci, ruwa akayi sosai washe gari da safe bayan sun karya ne, Malam yayi shirin zuwa gona nan Ammar yace zai bi shi suka tafi tare, inna da Auta sukayi aikin gd. Haka rayuwan su ya kasance acikin kauyen cikin kwanciyan hankali, yau kwanan su 10 kafar Auta har ya warke, Ammar ma ciwonsa ya bushe har yayi bawu, nan yasoma tunanin mafita don zamansu kauyen kaduna sam baiyiba, don marasa imanin nan suna sanin yana cikin kauyen to zasu iya turowa a kashesu baki daya, malam ya samu ya masa baya ni yana so su kara gaba don in mutu nen nan suka samu lbr zasu iya turo wa a kashesu malam yace hakane jiki ba kwari ya dau ko yan kudinsa da ya tara na kayan gonan da ya sayar ya basu yace suyi guziri inna kam da taji zasu tafi har da yar kukanta don sun shaku auta ma tayi hawaye, washe gari alhamis suka fito da ga kauyen nan suka shiga motar zuwa rigiyar malam wani kauye da ke jahar bauchi, a cikin motar suka zauna shiru ba mai magana sai yan motan da suke hira duniya. Haka har suka iso wani kauye wai shi na bardo, nan yaga ana sauka kawai sai yace bari su sauka gurin nan suka sauka, koda suka sauka gefen rumfunan garin dake bakin hanya ne ya sayo musu fura da nono roba biyu ya ba ma zee ta amsa, tafara sha kenan sai ga hawaye, ammar na ganin haka yace Auta hakuri zakiyi shi rayuwa haka take yau dadi gobe ba dadi mukasance cikin gode ma Allah, sai ya kara wada yar mu cikinta yayi sanyi amma takasa shan nono, wai ita ce yau a titi a kuma kasuwa take cin abu, rayuw kenan Allah ya jikan su dad, ganin taki sha yasa Ammar yakasa sha shima, don baya kaunar ganin zee cikin tashin han kali, nan2 sai yashiga damuwa. haka suka bar gurin suka dawo gindin wata bishiya suka zauna, lokacin sallah yayi ya nufi masallaci, yayi sallah dake a gefensu yake bayan ya idar ya dawo auta tayi alwala ta shinfuda dan kwalin zanin da inna ta fata ta daura, tayi sallah, haka har dare yayi koda aka watse gashi basu san kowa ba, Ammar ya duba musu gurin wani mai shayi da benci a gun nan ya hada ma auta kwaya biyu yace ta kwanta, haka ta kwanta idonta na zubar da hawaye, tabbas tasan ammar ne kadai ya rike iyayenta da gsky, Allah ya saka masa da dawai niyar da yakeyi da ita, Allah ya jikan iyayenta da nasa Ameen, Ya Allah ka bani abunda zan saka ma Ammar da shi, kuka ne yazo mata marar sauti haka tayi mai isarta daga baya tayi shiru, ammar ko kasance wan benci biyu ne a gun mai shayi ba wanda zai kwanta yasa ya dan zauna ya jingina da jikin falangen gurin shayi haka har bacci ya daukesu. Cikin dare misalin karfe daya da rabi, cikin bacci Ammar ya rika jin ihu daga nesa tun abun na nesa har ya matso kusa sai auta ma taji ta tashi, ihun yayi yawa gashi gudu sukeyi sai a lokacin yaji ana cewa barawo barawo, yace ma auta ta tsaya kar ta fito jikinta sai bari yakeyi nan ya fita itakuma tana lekawa, aiko yana fitowa sai ga wani tutum da gudu yabi bayan gurin shayi ya gudu, ana haka sai ga mutanen sun yi kansa suka nan suka fara dukansa suna shine barawon, auta na ganin haka tafito da gudu ta na ihu, wayyo Ammar dina ba barawo bane, wayyo dad kuzo ku kuga halin da muke ciki zasu kashe shi kansu tayi gadan2 tana so ta kutsa, da kyar ta samu tashiga dai2 wani ya kai masa duka da dorina kenan ya sauka akan Auta nan tasaki wani razanen kara. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam [6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Wani kara tasaki, sai a lokacin suka kula da ita, take suka haskata da toci sai sukaga macece, wani daga cikinsu yace mai ya kawo wan nan guri, sai da yace tsaya in ga barawo nan tukun don wancan gajeren wando ne ajikinsa, yana haskawa ko ah… ah.. wan nan ba barawon bane to ina yayi, sai dayan yace wan can na da kirar gutun mutum, auta ko sai ihu take, ammar ko motsi ba yayi sanadin dukan da aka masa harda bora, wasu ice haka akayita kwana masa. A kaduna kuwa sadiya Al’amari abban ta ya daure mata kai don yasaka dukiyar auta gaba sai ci sukeyi, a ko a jikinsu, wata ran kam ma intasoma masa zancen auta ya hauta da fada kenan, haka yasa ta soma zargin wani abu a tare da su, Wani yammacin asabar sun fito gidansu futha suna tattaunawa akan batun auta da yanda zasu bi al’amarin kenan sai suka hango abban sady, tun daga nesa yasoma wurga mata wani kallon tuhuma, ganin haka yasa tayi sallama ma futha tashiga gd, aiko kamar jira yake yazo ya fara zazzaga mata bala’i akan tafita harkan futha ko ya saba mata, shi baya son kawancen su, ganin su tare ma baya so, sady tace kayi hakuri abba ina tarayya da ita ba dan komai ba sai tun auta ta nan muna tare mun kuma shaku, abban sady yace hungo nan uwaki da autan nace uwaki da auta kar ki kara kira min sunan wayan nan banza mutanen, nan take idon sady ya kawo hawaye ita kam bazata manta auta ba aminiyarta jininta, anya baba na da imani kuwa ko tausayinsu babu a zuciyarshi ko ya manta dukiyar iyayenta yake wada kansa shi, ya Allah kasanya mana tausayi da imani a zukatan mu Ameen ranan tayi kuka haka ta yini sukuku, sai yamma tayi shirin issalamiyya ta tafi ko da taje nan ta saida wa malaman su akan sutayata adu’ah ta kuma musu bayani ko mai ake ciki, tun daga ranan ya zamana kulum a makaranta bayan an gama karatu sai anyi ma auta da iyayenta adu’ah. Futha kuwa kwana 2 taji sady shiru nan tashirya ta shiga gdnsu aiko nan sukayi karo da abban sady, tun daga nesa yasoma hararanta, tana isowa kusa yace kee wajen wa kika zo cikin ladabi tace baba kawar Auta ce nazo gun sadiya ne, yace maza ki juya kar na kara ganin lafarki a gdn nan yata batayi kawance da ke ba don ban yarda da kee ba. ran futha in yayi dubu ya baci haka ta juya gd jiki ba kwari kuma tana tunani akan al’amarin nan, anya ba hannu baban sady a kisan su abban auta, to tabbas ko ma miye sai na binciko ko da hakan yana nufin rasa raina ne ya Allah ka bayya na gsky. Muta ne da ke gun duk suka soma watsewa ganin baya motsi gashi sun dakesa ba akan wani laifi ba, gudun shiga Case, auta ko in banda kuka da ihu ba abinda take sai kiran sunan Allah ga idonta har ya kubura yayi ja ga ammar shi da matatce marabansu kadan ne, wayyo Allah na ka taimaka min ka min agaji in ammar ya tafi bani da wanda zan kalla inji dadi, rayuwata zata zama abar tausayi Allah kaine gata na ka tai make ni ammar dina ya tashi, cikin kuka take jijiga Ammar ga hawaye ga majina duk sauka sukeyi, Ammar dan Allah ka tashi kar ka barni ka manta Dad ya baka “AMANA TA” ka tashi ka kula da “YAR AMANA” ka kuka take sosai mai ban tausayi tana ta surutai amma shiri ganin haka yasa takara fasa wani kuka mai ban tausayi wanda ni kaina Rasheedah ban san lokacin da na fara zubar da hawaye ba, gsky Auta da Ammar kun ga jarabawar rayuwa ga wlh Allah sarki auta abun tausayi, Allah yasa ammar dinki ya tashi Ameen. Jumma’at Mubarak 2 all my muslim sisters n brothers. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam [7:32PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Kuka take sosai ammar ko motsi baiyi ba nan takara jin natsara su baba sani suka jefasu cikin irin wan nan halin, wani bawan Allah ne mai tausayi ya dawo yace bai war Allah daga ina kuke, cikin kuka tace ka taimaka min dan uwana ya tashi shikadai ya rage min an kashe iyayenmu, nan kukanta ya tsananta cikin tausaya wa yace ki tsaya tai mako daya zan miki yanzu ga gidan mai gari can barin je na kirashi da gudu ya tafi ko da yaje ya jima yana buga kofar kafin aka bude, masa, mai gari ya fito suka gaisa nan yasa sai damasa cikin damuwa mai gari ya dauko garensa ko da suka zo har lokacin ammar bai farfado ba, hakan yasa suka daukesa zuwa asibitin garin nan aka bashi agajin gaggawa, bayan sun dan masa treatment ne suka shin fidesa akan yar gadon asibiti, auta ko in banda kuka ba abunda take, bayan ansa masa ruwa mai gari ya musu sallama akan da safe zaizo duba su, auta kasa bacci tayi ga haddiri ya hadu nan akara walkiya da sauri ta haye karamin gadon duk tsoro ya ci kata baran data ga wajen asibitin jeji ne, nan ta kan kame ammar sosai hawayen ta na sauka a akan kirjinshi cikin barci yaji an kan kamesa, a han kali yasoma bude ido yaga duhu da kyar ya iya daga hannunsa yaji auta ne nan kuma yayi kokarin mikewa kansa ne ya masa wani nauyi ga sara masa da yakeyi, a hankali ya shafa kan yaji bandeji ne an daure, sai a lokacin ya tuna mai ya faru hawaye ne yasoma zuba masa shima tabbas yasan suna cikin wani yanayin da Allah ne kadai zai fiddasu. Auta jin alaman na motsa hannu yasa da sauri ta shafi fiskansa nan taji hawaye a hankali ta daga hannun ta tasoma share masa hawaye tana cewa kayi hakuri Allah zai saka mana kaji kuma Allah yana tare damu yaga halin da muke ciki ba zai bar mu haka ba, nan ya karajin jikinsa ya mutu ga auta
Chapter 7 · 0% Book details