Sashe 13
Amanata Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kaya haka na tattara na shiha toilet shima duk ta bata sai da na gyara mata kafin na tafi na Aunty kausar na ita ma na gyara mata duk da yana gyare bayan na gama ne na fito na nufi cikin na debi abinci na ci na yi wanka na kwanta don banson in ketare dokar Munay banson abunda zaisa ta wula kanta ni bayan nayi wanka Al-qur’ani na dauka nasoma karatu har zuciyata, tayi min sanyi nan na kwanta kan sallaya bacci ya dauke ni ban farka ba sai karfe 2:30pm wanka nayi ina son in fito falo ina tsoron karo da su manay ga warning din da tamin kar in sake inyi make up kuma kar na hadu da Yayan su Ahyan ko mai yasa oho ni ina ruwa na ma da shi gashi tasa nayi nisa da Ammar dina dole wanda kullum muna tare da shi ga kulawar da yake b an na musamman nan take naji wasu kwallan ta kaici yana zubo min na goge hawayena na jingina da gado na fara yan adu’ah dana saba ina mai adu’ah ma iyayena da sauran musulmai. Sannu a hankali suke tafiya yana kallon yanayin garin kunnensa dauke da ear peace yana bin wakokin Arjuli siyn shararen mawakin da ke raira wakokin India Ahyan yana son wakan sa sosai don shi ya raira wakar Ashque ma, a haka har suka iso G R A, a hankali Kausar ke tukin har suka zo kofar gate din su horn tayi cikin nutsuwa kafin mai gadi ya bude musu kofar gate din taje tasamu parking tayi parking da murna ya fito yana kiran Mum yayi cikin gd hajiya mamu ta fito da murnanta ta tari danta nan ta kawo masa ruwa mai sanyi sai kaga bakin hajiya mamu har kuni danta namiji tilo ya dawo yau kam murna ba a magana sai da ya huta kafin suka nuna masa dining kausar da munay suna gefensa Mum dinsu da kanta tayi serving dina sosai ya ke cin abincin yana santi bayan ya gama ya nufi dakinsa ko ina a gyare sai kamshi ya keyi wanka ya shiga bayan ya fito ya yi sallah sannan ya sake fitowa falo hira suka dan taba kafin H Mamu tace yaje ya huta nan ya tafi dakinsa kausar itama dakinta ta nufa. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Kausar tana shiga dakinta ta ganshi a gyare ko ina murmushi tayi Allah sarki baiwar Allah gsky auta tana da halin kwarai ko jikinta barin dubota yanzu haka halan ko abinci bata ciba dakin auta ta leka ta ganta jingine da gado ta lumshe idonta da alamar kamar bacci take amma ba baccin take ba fridge taje ta dauko mata kunun aya ta nufi kitchen ta dauko mata abinci da plate ta dawo dakin a hankali ta ke tada ta Zee ta bude idonta taga Kausar ce murmushi tayi tace Aunty Kausar kun dawo lfy ya hanya kausar tace wato ko ki fito ku gaisa da bros ko auta tace zanje in gaida shi Kausar tace to tashi kici abinci na san yanzu haka ba abinda kika ci ba musu auta ta mike taci abinci sukayita hira harsai la’asar kausar ta nufi dakinta don ganatar da sallah la’asar auta ma sallah tayi bayan sun idar ne suka shiga kitchen sukayi abincin dare bayan sun fito ne auta ta koma daki don yanzu ta hana kanta zaman falo bata son hayaniya sam. Ammar business ya zauna ga shago sai kara habaka yakeyi abun sai son barka burinshi kulum autarsa ya ganta cikin farin ciki san nan komai ya samu ita yake sayama wa haka account dinsa ma da sunanta ya bude duk kudin da ake basa nasa yana sawa a gun kamar kulum da ya saba zuwa sari kano yaje yayi sari nan ya ga wasu dogayen riguna masu kyau haka ya saya musu su uku Zee Auta maroon da ratsin golden colour na kausar baki na munay ash da ratsin baki sosai yayi sayya yana ta sauri ya dawo don ya gana da dan hajiya mamu wato Ahyan don shima ya nuna nasa farin cikin dawowarsa. * * * * * Kaduna kuwa haka rayuwan futha da sadiya ya kasance yanzu futha ta gama diploma har tasamu Admission a degree tana gamawa zata tafi school of law haka tacigaba da gu danar da yan bincikenta don ta dau ma kanta alkawari sai ta gano wanda ya kashe ma auta iyayenta. Sadiya ma haka abun yake karatunta take cikin kwanciyan hankali amma sai dai kulum tunaninta autar ta awani haki take ga iyayenta ku su nuna damuwarsu a kan magana gashi dukiyar sai habaka take abinda ya daure mata kai yanda taga wasu mutane tu da alamar ko bacun ransu baba isiya da Abbanta basa son gani gashi kuma mai gadin gidansu Auta da sun dawo sun dinke da iyayenta kuma wani abun daure kai yanda pinky kewasa da naira ba mai kulata sai kara daure mata gindi akeyi in yau ka ganta awan nan motar gobe da wancan kawaye kuwa sai yayan manya take harka da su abun sai hmmm don yanzu ji take da kanta tana kallon Big Girl ce ita ga naira ga hutu. Ammar ya dawo yayi murna da ganin Ahyan sosai ya kawo tsara ba masu auta da kausar san nan yanzu an yanke shawarar zai fara fita waje nan yayi murna da godia san nan ya ce ma auta ya kamata suje kauye su gaida su Inna larai da Malam don su musu karamci da bazasu taba mantawa ba, hajiya mamu ya samu ya mata bayani tayi murna san nan ta basu goma na arziki sukai musu nan kausar tace zata bisu tunda gobe zasu dawo munay sai wani yatsina take ita ala dole tana kyamar yan kauye, Tunda Ahyan ya dawi ko da wasa basu taba haduwa da auta ba yau kwanansa 4 ya ba masu kausar hakuri akan kayansa ran Thursday sai iso sukace ba matsala, Ammar wanka yayi sosai haka ma auta sunyi kyau kausar ta dau Camera don tana son zuwa kauye ran asabar da safe suka dauko hanyan suwa kauyensu Malam suna masu farin ciki. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam [7:49PM, 9/20/2016] Rash Kardam: [10:47AM, 4/5/2016] Rash Kardam : AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Sai karfe 12:00 suka isa garin sun samu su inna cikin lfy bakaramin murna sukayi da ganinsu ba nan ina ta musu tuwon geronta mai kaushi miyar danyen kubiya ga man shanu sosai su kaci suna zuba santi baran Kausar ma tafi kowa santi don ta dade bata ci irin wan nan abicinba ga surki yaji suga sosai koni rash sai da na lashe baki don yawuna yana tsilo tsabar kamshi ya ishen. Sai da suka huta bayan sunyi sallah asazahar tukun ammar ya basu tsarabansu nan sukayita murna kafin suka fara hiran yaushe gamo nan ammar ke bama su inna lbr bayan barin su garin sun tausaya musu sosai sai yamma sukayi wanka suka fita zaga gari dandali suka nufa tun daga nesa suka hango yam matan garin sunyi wanka masu sayar da abinci na sayarwa abun dai sai kun gani. Najaat ce da tawagar kawayenta tunda ga nesa ta hango ammar da su auta zunguro ummen da zulai kaii kalli wancan kamar wanda suka taba zuwa maciya da malam la shine dan birni kai kali wancan auta ta nuna sina kama da wan nan yar India mai gashinan ga kawarta ma kamar yar india nan suka saki baki sai kallinsu suleyi haka su auta da kausar da ammar sukayita hotuna sai magriba sukamar dandali suka dawo gd bayan sunyi sallah ne suna zaune suna hira sukaji surutun mutane da yawa kuma mata sai azo a dan lekasu a koma can dai abun yayi yawa sai malam ya mike ya a hankali ya fake aiko lokacun su najaat suka leko karaf malam ya rike ta waye nan tafara inda2 daman tazo gaida ina ne sai taga yan birni malam da ya gane waye sai ya kyaleta yace su bar labe ba kyau nan suka shiga cike da murna suka gaida su inna sai satan kallon ammar sai da suka dade sosai kafin suka musu sallama suka nufi gd su malam ma sukayi sallama wa su auta suka shiga dayan dakin inna da kausar da Zee suka kwana daki daya da safe inna ta soya musu kosai da yar tsame ta musu kunun tsamiya haka suka karya cikin farin ciki daga nan suka fara shirin dawuwa bauchi, Su inna sun cika mu da tsaraban kauye su daddawa ne wake gyada kuka harda zuma, Wanka sukayi sannan ammar ya ciri 10k ya bama malam inna ko 5k godia sukayi sosai kafin suka rakosu gun motarsu suka dau hanyan bauchi. Tun bayan da su kausar suka tafi kauye da yamma ahyan tazo cin abinci ya ga ga abinci har abinci a ido yana sawa a baki yaji ba test karshe haka ya hakura tea ya hada ya sha mum ma da tana sawa a baki ta ajiye gashi hauwa bata nan ta shiga cikin gari yau munay ce tayi abinci sai da ta sha tea kafin ta kira munay tayi mata fada akan ta dage ta koyi girki din girki shine mace kiga kausar da Zee mana yanzu ina ne zasuje baza suyi abinci wa mitum yaci har yana santi Munay sai zun bura baki takeyi ita a dole an mata fada ta tashi ta nufi daki sai kunkuni takeyi haka dai a daddafe suka kai washe gari Mum ke musu abunci ahyan ma ya masu kausar ta dawo don yafi gane cin abincinta sai ko in mum ce ta musu yana ci sosai. Ba mu iso cikin gari ba sai kusan 1:40 dake ba mu fito da wuri ba ko da muka dawo wanka mukayi muka ci abinci kafin mukasa aka shigo da tsaraba muka nuna wa mum yau hauwa’u mai girki ta dawo dan haka daki na nufa na fara baccin gajiya. Yau kwanan mu 3 da dawuwa daga kauye kulum gidan mu cike yake da wakar india daga gani nansan yayan su kausar ke sawa kuma shima da alama masoyin wakokin india ne kulum