← Book details Amanata Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 22

Sashe 3

Amanata Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gefen window, cikin hantsari ya fisgo Auta ta fadi kasa wanda faduwar wata ya dai2 da wani dutsi nan ta buge bakinta sai ga jini, kara tasa yayi sairin toshe mata baki, su gumus da kawu isiya suna isowa harbi suka fara amma bai kai ta inda su Auta suke ba, baba sani ne ya ciza yatsa don ya ji haushi ga window ya musu kankanta baza su iya fita ba da sauri yace ku zo mu zaga mu bisu da sauri suka fita ga ruwa haryanzu zuba yakeyi sosai. Ammar na ganin sun bar window yayi kokarin rashi ga jiri na debansa don jininsa ya zuba sosai, ga Auta kuma jiki ba kwari, ya mike yana tan gadi ya dagata kasa tsayuwa tayijijjigata yayi da kyar sai ta sauke ajiyar hrt kafin ya mikar da ita suna mikewa suka hango motar su baba sani sun nufosu, nan ya fara janta da gudu tunda daga hayin rigasa layin waya suke gudu sai da suka wuce kantin yawo, kafin suka kara gudu dai2 zasu fita a hayin rigasa, Auta ta fadi da sauri ya dauketa ganin in yace zai miki hanya zasu kamasa sai yayi gurin wani sabon gini wanda dogayen ciyawa sun bullo agun gabansa kuma katon ruwa ne wanda ya taru, nan ya kaisu gun ya tsuguna ya tare Auta da numfashinta ke shirin daukewa abunka da rashin sabo ga razana don Auta in banda girki da take taya hajiya bata wani wahala, tasaba da rarrafen carpet tun tube da waya, baran da ta rage ita daya ma Dad da Hajiya ba irin gatan da basa mata. Su baba sani da suka iso gurin nan suka fita ga ruwa na sauka sosai duk dube2 da sukayi basu gansu ba, Ammar kuwa suna gurin a tsugune da ke Auta ce ta jikin garu, nan wata kuna ma ta fito sabida ruwan da ya dameta a gidanta tana fitowa kuwa kafar jidda ta hau sai da tazo kusa da gwiwanta ta danna mata cizo, har saubiyu duk da zafin da taji tayi saurin damke bakinta , Ammar na ganin haka ya kara matse bakin nan kuwa kunamar ta kara yanka mata cizo, sai murkususu take tayi, gumus da duna sukace alhaji ku tafi kawai mu zasu tsaya mu ne mesu in baku mu kawo maka gawarsu ba to zamu maka da lbr mutuwarsu, nan suka tafi da motar suka bar su gumus a gurin, sun dade suna dube2 sosai agun kafin suka soma fita, Autakuwa wuya yayi wuya bata san lokacin da ta kwace bakinta ta saki kara da sauri su gumus suka juyo nan suka fara nufo gurin da sukaji karan, Ammar na ganin haka ya mike yasoma jan Auta suna kara gaba kawai suka ga kato kogin ruwa ne a gabansu ga su gumus sun nufosu. Abun gwanin tausayi nikaina Rash bansan lokacin da na fara zubar da hawaye ba . Allah sarki su Auta da Ammar Allah ya kwace ku a hannu wayan nan Azzalumai din Ameen. Sai dare zakuji ni Taku a kullum mai kaunar ku ®WHW® Rash Kardam [9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Ammar ya ma rasa ya zaiyi ga Auta numfashin ta na kokarin daukewa da sauri ya suguna akasa ya ajiyeta acikin tabo ga jini yana ta zuba daga hannunsa, Gumus suka nufo su da sauri nan ya harba bindigan ya sake harba wa yaji bullet ya kare cikin jin haushi yace oh ya wurgar da bindigan akasa ya nufosu ko da yazo daman Ammar na ankare yana isowa suka fara kokuwa cikin ukon Allah karfin yazo ma Ammar ya wurga shi a wan nan ruwan, aiko dan uwan gumus na ganin haka dake yana haskasu da touch light, ga shi gumus nata fanjam aruwa dake shi bai iya ruwa ba, kuma ruwan da dan yawa, da sauri yayi gun ruwan ko ta kan su Ammar baibiba ya je gun dan uwansa don ceto rayuwansa, Ammar na ganin haka ya dauki Auta yasa gudu sai da yayi nisa ga ruwa ya soma tsagaitawa, ya samu wani rumfa ya ajiyeta ya huta, basu dade sosaiba ya auta sai hawaye:'(:'(take tayi ko da ya laluba kafarta yaji ta kubura suntum, taba kafar dayayi har sai da tayi ihu haka ya dauketa suka cigaba da tafiya. Su gumus ansha wuya da kyar aka ciro shi don har yasoma shan ruwa, yana dawo wa hayyacinsa yake tambayar mugum ina suke yace sungudu, mtssss bahaka nasoba nan yace naga abunda ya faru kar ka sheke zuwa lahira da wuri shiyasa na ciroka kai kajimin wayan nan sai kace mutuwar nima izini takeyi, mikewa sukayi gumus ya karbi wayar mugum don nasa ruwa ya bata, baba sani ya kira ya tambayesu suna ina yace yanzu zasu bar gidan Alhaji kenan sukace gasu zuwa. ko da suka isa nan suka samu baba isiya da sani sun daure sale mai gadi da musa, don daman sunyi akan zasu daure su sabida ace barayi ne suka zo, hakan sukayi, ko da su gumus suka iso nan sukaga abunda ke faruwa dariya sukayi sosai sukace Alhaji baku da dama, Baba sani yace ya ina fatan kun sheke su cikin sauri gumus yace ai har gawan ma sai da muka yardasu inda ba mai gani, nan kawu isiya yace aikin ku na kyau, gumus yayi murmushi yace oga sai kudin fa baba sani yace ina zuwa cikin gidan suka shiga dakin dad suka duba drawer nan suka ci karo da damin kudi sai dasukayi dariya sosai kafin suka diba nan suka fito falo, baba sani yazo cikin izgilaci yace su Al-hassan yau an sheka kiyama to ina naira kai dan taurin kai yau zamu facaka da dukiyar da kake ta kama dashi, yana zuwa kan hajiya sai da ya shureta da kafa, ke kuma yar iyeye yau munyi maganinki da yar da kuke so, harda dauko bare wanda bakusan daga ina yake ba ku fifita shi akan mu gashi yau duka bakwa nan mun kuma samu dukiyar cikin ruwan sanyi sai ya kece da dariya sosai, nan suka fita suka shiga mota suka tafi don suke su sallami su gumus. ®WHW® Rash Kardam [9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Ko da sukaje gidan kawu isiya wanda tutun nufawa, ba kowa aciki kuma ba nisa sosai da gidan Alhaji marigayi, nan suka shiga ko da suka zauna nan baba sani yace yau burin mu yacika na gama wa da Al-hasan da iyalansa, kamar yanda mukayi Alkawari zamu ba ku 400k kowa zai dau 200k kenan gumus ne yace oga mungo amma munaso aba mota koda kwaya daya ne ehhh musamu na yawo a gari, ko wani aiki kuke so zamu muku cikin sauki kawu isiya yace aaa bazai yuba abun yaso ya dawo musu rikici baba sani yace ba matsala za a duba in komai ya lafa abaku, nan ya ciro 300k ya basu yace kurike wan nan kafin komai in ya lafa zamu sallame ku, gaba daya nan sukayi sallama kowa ya kama gabansa. Da safe yan unguwa suka fito don wasu sunji karar tsayuwar don haka suka yi cirko2 gashi jiya anyi ruwa sosa, mukwabcin dad wani mai suna Alhaji Abubakar yace yan uwa yau ban ga Al- hassan a masallaci ba kuma duk rintsi in ba jinya yayi tsanani yana zuwa sallah amma yau shiru, ko lfy wani mai suna Alhj kabir yace ni jiya fa kamar an shigo unguwan nan don duk da karan ruwan sama dake zuba naji ihu san nan naji harbin bindiga sun dade suna jimami kafin wani acikinsu yace kamata yayi mu shiga gidan mugani, nan suka dun guma suka shiga tun a kofa sukaga masu gadi an daure su, da sauri suka isa wajansu, bakinsu an toshe da tsumma, kunce su sukayi nan Alhaji Abubakar ya fara tambayan lfy, sun wahala yasa ba wani amsa don dauri da aka musu mai kyau ne hakan shi ya gala baitar dasu, da sauri suka nufi cikin gidan bayan sunshiga a falo suka tarar da gawan Alhaji da hajiya nan suka soma jimami masu kuka suka fara, alhaji abubakar makocin dad police ne nan take ya kira ja mi’an tsaro suka fara binjike nan sukaje dakin Auta inda suka ga yanda aka baza kaya da alamar kare kansu da sukayi da kuma fasa window da akayi gashi ba auta ko da suka zaga nan sukaga jini da kuma alaman harbin da akayi ta waje, Alhj Abubakar yace cikin daya biyu ko sun kashe Zainab ko sun dauketa ko da suka dawo gd sai alokacin ya tuna da ammar nan ya nufi dakin da ke tsammanin nasa ne sallaya tagani a shin fide da alamar anyi sallah akai ki da suka fito suka nufi kofar baya nan sukaga an tura kofar anshiga duk binciken da sukayi ba wani amsa nan suka kira Alhaji sani da baba isiya suka sai da musu, ko da suka iso gidan kuka sukeyi sosai kai ka rantse basu da hannu aciki har sani na ikirarin imyasan wanda yayi kisan nan sai ya dau fansa, kawu isiya kam ko mace iyakaci yanda yake kuka. haka police suka tafi da gawarwakin don kara bincike. Ammar da auta kuwa tafiya yayi sosai, sun shigo cikin gari kuma dare yayi sosai don asuba ya kusa, nan yasamu inda ba ayi ruwa ba ya kwantar da Auta ya yagi zanin dake daure a saman kayan baccinta ya kulle hannusa sai runtse ido yakeyi alamar zafi, ya daure hannuta ya dauketa suka cigaba da tafiya sunyi nisa sosai, sai ga wani mai mota yazo wucewa nan ya tsare shi sam yaki tsaya haka ya cigaba da tafiya sai ga wani da alamar wan nan irin yan taxi masu zuwa gari zuwa gari har yaki tsayawa komai ya tuna ya dawo daukarsu, nan Ammar nace ina zan kaiku Ammar yace ban sani ba mutumin yace to ni saminaka zanje yanzu, yace muje ka ajiye mu a hanya. ®WHW® Rash Kardam [9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Motar suka shiga nan mutum min yace subada 1500 kudin mota sai a lokacin ya tuna basu da kokisi, innalinahi wa inna ilaihi raji’un abunda ya furta gashi
Chapter 3 · 0% Book details