← Book details Amanata Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 22

Sashe 16

Amanata Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gyara ta kama wasu ayukan. Su mum sun isa sakoto lfy, tayi duk abunda ya kaita, da taso su kwana 2 amma sai aka mata kiran gagawa dole suka shirya don ta jirgi zasu dawo yau din nan 5 jirginsu zai sauka. Auta ko han kali kwance take aikin ta, har da yar waka ta, ahyan ne ya shigo gd ya leka daki munay yaga bata nan, murna fal ransa ya nufi dakinsa ruwa ya watsa kafin ya canza kaya zuwa boxer da singlet ya nufi dakin auta, nan yaga fata dawo dakin ba, buya yayi a toilet. Auta na gama aikinta ta shigo dakinta, bata rufe kofa ba turawa tayi don zata koma jimawa kadan ta dauko zobon da taha kafin yayi sanyi, kan gado ta fada, bata wani dade ba ta fara gyan2di, a hankali ahyan ya bude kofar, lokacin bacci barawo ya dauketa, kusa da ita yazo nan ya fara mata wani irin salon, “(ido na zaro ina rokon Allah ya kubutar da wannan baiwa daga hannun wan nan maras tausayin)”. Auta kamar daga sama taji ana mata wasu abun da ya basa tunaninta, a hankali ta soma bude ido ganin ahyan yasa tasoma kokawan kwace kanta, amma ina yafi karfinta, sai kokarin rabata da kayanta yakeyi, da kyar ya samu ya yaga rigan jikinta, ganin daga ita sai bra yasa ta ja da baya ga hawaye da ke zuba, shiko sai wani dariyan mugunta yakeyi, haka har suka iso bangon dakin, ya nufota gadan2 tasaki wani razanane kara, Wanda yayi dai2da shiigowan Ammar gidan, bai karasa parking ba sai ga su hajia mamu sun iso, auta ganin ba wanda ya jita yasa takara takarkarwa iya karfinta tasaki ihu ta fadi kasa sumamiya, shiko hakan baisa ya ci gaba da abunda yayi niyar yi ba. aiko dukansu da ammar da su hajiya bansan wanda yafi wani gudun shiga ba, nima ina ganin haka na bisu da mugun dugu har sai da wayata ta fadi. Mai karatu ban samu daman daukar wayata ba, nabisu don inji gurmin da za a toya, kar ya wuce ni, in na dauko zakujini a next page….lol… Taku a kulum mai kaunarku Yar Mutan Kardam ®WISDOM HAUSA WRITER’S Rash Kardam [7:56PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Da gudu suka nufi cikin gidan, duk a rude suke, ammar garin hawa stairs ya fuge kafarsa, nan take sai ga jini ya soma fita, amma ko ta kansa bai bi ba, yana isa yaga kofar arufe yayi zaton da key ne ajiki, komawa yayi da baya yayi wani duka ma dakin, sai yaga ko motsi baiyi ba kafin yasake naushin, H Mamu ta zo da sauri ta murda kofar sai gashi ya budu, duka suka shiga dakin, abunda suka gani ne yasa su suman tsaye, ammar da gudu ya kaima ahyan damka wanda shi gaba daya baya cikin hayyacinsa yana kokarin kire ma auta skirt yakeyi, ammar ya shake wiyarsa ya makasa da garu take kansa yasoma zubda jini, ran hajiya mamu ya baci idonta ya rufe, ga hawaye zai zuba yakeyi dai2 nan munay ta shigo ganin abunda ammar yake ma bros dinta yasa tafara dukansa wani naushin da ya mata sai da ta fadi gebe dan azaba kasa kuka tayi, hajiya mamu tazo tafara taya ammar dukan ahyan, sai da suka ga baya ko motsin, suka kulyalesa, kausar kam kuka take kamar ranta zai fita, ammar da gudu ya dauki auta yayi waje da ita wanda marabanta da gawa kadanne, kausar da H Mamu suka rufa masa baya, akabar munay da bros sai kuka take tayi. Ni’IMA CLINIC, ya nufa gudu yakei kamar zai tashi sama har sai da yan hanjin cikin kausar suka kama disko, suna isa emergency suka nufa, da sauri nurses suka karfe ta suka shiga da ita, ba a dade ba na hango Mrs Adul cikin shigan kayan likita, tayi emergency, ammar ko kasa zaune yayi sai zagaya wa yakeyi, yana hawaye nan wani bakin ciki ya tokaresa, bai san lokacin da ya buga hannunsa a garu. Har sai da hannu tayi kass, kausar duk ta tsure da lamarinsa daman haka yake da zuciya, (ni rash nace hmm). Can Mrs Abdul ta fito fiskan nan baya bo ba fallasa da sauri Ammar yayi gunta, Dr ya jikintan? Ta tashi kuwa? Atare ya jero mata wayan nan tambayan, ajiyar zuciya tayi kafin tace Alhamdulilah, bata tashiba amma zamu ce da sauki, amma meye ya razana ta haka don tayi dogon suma, amma muna sa ran farfadowanta a kowani lokaci, aziyar hrt ammar yayi, Mrs Abdul taci gaba da cewa, zamu kaita dakin hutu ba kuma mai zuwa kusa da ita don bata son hayaniya, suna tsaye akazo aka wuce da ita special room, hajiya mamu kam duk takasa cewa komai wai ace ahyan ne ya aikata haka, ina tarbiyan da tabasa duk yasa kafa yayi watsi da shi, in sonta yakeyi, mai yasa bazai fada mata, sai ayi musu aure ba? Dole in gwada wa ahyan bacin raina dole nasan abin yi, kausar kam kasa hada ido tayi da ammar don tana jin tsanar ahyan amma sun gode ma Allah da Allah yasa bai kita mata haddi ba. Munay kuwa ganin kar dan uwanta ya mutu, yasa ta mike tana dingishi, ta nufi harabar gidan isa mai wanki ta ganin nan ta kwala masa kira, kazo ka taimaken, sanin halinta yasa ya biyo ta da sauki, sama suka haura nan tace ya kamata ahyan ahaka suka fito, mai gadi ke tambayan ta, maike faruwa? Wani mugun kalo tamasa wanda yasa dole yaja bakinsa yayi shiru, sabida sanin halinta, da gudu suka nufi T.H, suna zuwa emergency ta kaishi nan doctors sulayi caaa akansa basu dau lokaci ba suka gyara masa ciwon da yaji kuma ya farfado amma sun masa aluran bacci, sannan suka nufo munay suka fada mata san’nan ta tanadi kayan tea, don in ya farka ta fara bashi ruwa mai zafi ya sha, nan tayi godiya ta nufi hanyan gd. Ammar ko ganin an wuce da auta ga kayan da ke cikinta duk ayage yake wani sas’san jikinta na aje, yasa ya nufi gd don ya dauko mata kayanta acanza mata, bai ce kala wa H Mamu ba don wani haushin su yakeji, fita yayi ya nufi gd a mota don yana hanzari baya son yin nisa da auta, gani yakeyi kamar za’a sake mata abunda aka mata, yana isa gd, dakita ya nufa ga mamakinsa bai ko ga su munay ba amma dake ba damuwar sa bane kuma baya son ganin su, nan ya dau mata fallen zani da karamar riga, sai hijab, yazo fita kafarsa ta gogu da takalmin auta nan yaji wani azaban zafi da sauri ya kali gun, sai alokacin yaga ciwon da yaji, bai tsaya takan ciwon ba yazo sauka daga stairs yaga munay tana tahowa sai dingishi takeyi, wani mugun kalo ya watsa mata, fuskansa sam ba ko annuri, kamar baitaba dariya ba, nan take wani tsoronsa ya dira mata azuciya. Luv u all my fanz Rash Kardam [7:57PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Wani mugun kalo yamata, yanzu tsoron ammar ta ke baran da ta tuna nashin da ya mata da sauri ta dawo da baya, ta sauko sai da ta bashi hanya ya fita, sannan ta haura ta debi duk abunda zata diba ta dau poss dinta dake tana da kudi aciki ta nufi asibiti, tana zuwa ta nimi gu ta zauna ta zuba tagumi tana kalonsa, tana fatan Allah yasa ya tashi. Ammar ko yana fita ya nufi dakinsa ajiye ki din mota, don shikam yabar amfani da abun gidansu kuma yau zaisa afara nima musu gd, don tabbas shine silan ja ma auta wan’nan abun, in da bai yarda yazo gidan nan ba da ahyan bai mata haka ba, ko da ya fita abokinsa auwal ya kira yace masa gd yake so mai dan saukin kudi, amma ba wanda yake da mutane da yawa ba, auwal yace an gama zuwa gobe zakaji “feedback” nan sukayi sallama ya nufi asibiti, yana zuwa yasamu H mamu suna inda suke sun zuba tagumi, nan yaji tausayinta, gsky tayi masa karamci gashi tilon danta na miji ta wasa abunda bata tana zaton zatayi ba, bata so kanta ba ta bama dan ta laifinsa, gaskiya hajiya mamu tacika mutuniyar kirki uwa ta gari, wacce take son yayan wasu ta kuma kula dasu tsakaninta da Allah, Hajiya mamu Allah yasaja miki ya biyaki da rikon gsky da kika mana ameen, amma bazan iya cigaba da zama’a cikin gidan ki ba, don tunda yasoma kuskuranta, nan gaba zaiyi abunda yafi haka ni daman hankalina bai kwanta dashi ba, cikin zuciyarsa yake magana, sai da yaji H mamu tace ammar sannu da dawowa, firgigit ya dawo hayyacinsa, Murmushi ya kakalo wanda yafi kuka ciwo yayi, ammar duk yaba ma hajiya tausayi lokaci daya duk ya canza kamar bashi ba, kausar tamasa sannu, ya amsa ya tambayesu ya mai jiki sukace haryanzu dai ba lbr, kayan ya mika musu yace ya kamata su je gd su huta, h mamu tace ina ae ba inda zata zata kwana da auta, tace kausar taje gd, ido ta zaro don auta bata tsira itama tanaga intaje abunda zai mata kenan bare uwansu badaya bare uba, don da aure a tsakaninsu, ajiyar hrt tayi kafin tace mum kata kafarki, h mamu dake babbace ta gano kausar kuma sai taji badadi azuciyarta danta yau ake gudu,(umm tsakanin uwa da danta sai Allah duk da taga laifinsa amma sai da taji wani iri, yan’uwa ya kamata mu na tausaya wa iyaye mu kyautata musu, don sun sha wahala ba kadan ba akan mu ya Allah kaba mu ikon tausaya musu da jin kansu, kaman yanda suka mana muna kanana Ameen). Su hajiya mamu da kausar suka kwana a dakin masu jinya, shiko zama yayi a kofar dakin akwai chair azaune ya kwana da safe bayan sunyi sallah yaje ya sayo musu abinci, suka karya sai ga Dr ta zo nan suka gaidata, suka tambayeta ya mai jikin tace musu da sauki nan ta wuce office dinta, wayarsa ce tayi kara yana daga wa yaga auwal da sauri ya dauka, bayan sun gaisa yace my
Chapter 16 · 0% Book details