← Book details Akan Aikin Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 20

Sashe 3

Akan Aikin Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

1️⃣ Yawan ciwon kai mai tsanani da jiri.
2️⃣ Ciwon mara, baya da kwankwaso.
3️⃣ Jin motsi a gabanki kamar tana, ko jin motsi a cikinki yana zuwa bangare-bangare.
4️⃣ Jin abu kamar ƙiyashi na bin jikinki, ko kamar tsutsa, haka nan zaki rinka jin motsi a kanki kamar wani abu na tafiya.
5️⃣ Jin wani abu mai ɗan nauyi ya kwanta a wani bangare na jikinki, wani lokaci ya tashi daga wannan wurin ya koma wani wurin.
6️⃣ Jin zafi ko sanyi a tafin kafarki, ko kiji wannan wurin yayi dumi kamar an sa wuta, can kuma sai ya matsa ya koma wani wurin.
7️⃣ Jin wani abu kamar yana haɗiye ki.
8️⃣ Rashin son kitso ko wani abu da zai taba kanki, zubewar gashi, da sauransu.
9️⃣ Rashin barci da daddare.
🔟 Yawan faduwar gaba da tsorata da abu ƙanƙani.
1️⃣1️⃣ Rashin son mutane da gudun mutane, da tsoron mutane in ta shiga wurin da akwai mutane da yawa kamar kasuwa, da rashin son magana da mutane.
1️⃣2️⃣ Yawan fushi da tsiya, kiji kowa ma haushi yake baki haka nan kiji kin tsani mutane.
1️⃣3️⃣ Qin aure, da rashin son maza. Mace taji bata son namiji yace yana sonta, ko yace zai turo gidan su.
1️⃣4️⃣ Zaki rinka ji kamar ana miki magana, ana cewa ki aikata wani mugun abu, ko idan kina kallon wuƙa sai kiji kamar ana cewa ki coka ma wani.
1️⃣5️⃣ Yawan jin zafin jiki, kasala da kuma ciwo na rashin dalili.
1️⃣6️⃣ Yawan son kade-kade da raye-raye, wato aljani zai rinka saki yin wasu abubuwan da da can ba halinki bane.
1️⃣7️⃣ Yawan kallon madubi da yawaita kallon jikinki tsirara a madubi.
1️⃣8️⃣ Son dare, da son zama a cikin duhu.
1️⃣9️⃣ Jin kamar ana kiran sunanki ko firgita yayin da kike ke kadai a wuri.
2️⃣0️⃣ Yawaita kuka na rashin dalili.
2️⃣1️⃣ Qin karatun Al-Qur’ani, da kasa karanta shi ko ɗaukansa.
2️⃣2️⃣ Jin kamar ana tsira miki allura a jikinki.
2️⃣3️⃣ Rashin jin daɗin saduwa da mijinki da tsanar shi yayin da ya nuna alamar yana son saduwa da ke.
2️⃣4️⃣ Aljani zai iya sanyawa mace mugun infection ta yi ta fama yaƙi warkewa.
2️⃣5️⃣ Jin kamar kin aikata wani abu ba a cikin hankalin ki ba.
2️⃣6️⃣ Ganin inuwa kamar na wani, ko kiji an danne ki baki iya numfashi, sai kin yi addu’a sannan kika tashi.
2️⃣7️⃣ Yanke jiki ki fadi ba tare da sanin inda kanki yake ba.
2️⃣8️⃣ Jin kamar an daura miki dutse a zuciyar ki, ko kiji an matse miki numfashin ki.
2️⃣9️⃣ Samun ciwukan da da can baki da su, wanda likita zai duba ya rasa dalili.
3️⃣0️⃣ Yawan waswasi musamman a ibada.
3️⃣1️⃣ Rikitar miki da al’ada, jini ya dauke sai kin yi tsarki kin yi sallah sai kawai ki sake ganin jini.
3️⃣2️⃣ Hana haihuwa.
3️⃣3️⃣ Zama da datti da ƙazanta.
3️⃣4️⃣ Sumbatu da firgici a cikin baccin ki.
3️⃣5️⃣ Lalacewar jiki ko ciwo a wani sassa da aljani ke zama.

Wadannan da kuma wasu suna daga cikin alamar akwai aljani a tare da mutum.

---

SHAWARWARI GA MASU JINNU

Duk wanda yake fuskantar matsalolin jinnu akwai abubuwan da ya kamata ya fahimta kuma ya kiyaye:

1️⃣ Yadda mutane ke ganin tasirin magani yana da nasaba da yadda zuciyarsu take. Idan kana da kokwanto, abu mai wuya ne ka ga tasirin sa.
2️⃣ A kiyaye hakuri da gujewa gaggawa yayin neman magani.
3️⃣ Kada a fara magani sai a watsar bayan an samu sauki.
4️⃣ Kada a nemi magani ta hanyar zuwa wurin boka ko malamin duba.
5️⃣ A tabbatar da yin yaƙi da zuciya wajen amfani da addu’o’i da magungunan Manzon Allah.
6️⃣ A tsananta addu’a da roƙon Allah.
7️⃣ A koya da haddace addu’o’in kariya, musamman na safe da yamma.

Ina roƙon Allah ya kare mu daga sharrin shaiɗanu!

AMEEN

*Page 6 to 15*

"Subhanallahi baba Audu kaji ihun hajiya kuwa,"

"Nima wallahi ihundanaji ne yafito dani danni harna fara gyangyad'i,"

"Kodai mushiga muduba meke faruwa,"?

"Habadai sale taya zaka shiga gidan Mutum bayanan har ciki inda iyalinsa,"?

"To Amma ai kamawa tayi baba Audu Kuma idan zaka lura ai Koda Dr yananan nakan shiga parlour tinda Nike karb'ar guga ko sayen wasu Kayan cefane"

"Eh nasani duk da Hakan dai gara kafara Kiran shi Dr D'in Kaga yasan halinda Ake ciki"

Wayarsa Sale yaciro A Aljihunsa yasoma Kiran Dr saidai harta gama ringing Bai d'auka ba,

"Bai d'auka bane sale"

"Eh wllh Baid'auka ba Amma bari nasake gwadawa nagani"

Sake Saka Kiran yayi kusan 3 messed call yamasa Ana 4 yaji wayar switch off

Sake Baki yayi yana kallon wayar

"Yaya dai Bai d'auka D'in ba? Koyana cikin Aikine kasan fa su likitawa Musamman idan sunada girma da k'warewa basucika samun Hutu ba,"

"Haba Dan Allah baba Audu Aikoda Aiki wllh da mugun hali fisabilillahi kakira Mutum Irin wannan lokacin Kuma bayan yasan baka saba kiransa ba kakira yanzu Dan walak'anci tayi ringing harta gama yak'i d'auka daga k'arshe waisaiya kashe wayarsa Kai wannan bawan Allah Rayuwarsa da gyara wallahi Hajiya tana k'ok'arin zama dashi,"

"Sale kasanfa yanayin Aikinsa Kuma idan yana cikin Wani Uzurin nefa,"

"Dan Allah kadaina ganin kamar baida laifi wallahi ni indai gameda Aikinsa ne har Haushinsa nakeji Domin baida lokacin kowa da komai saidai Aikinsa shidai Aiki Aiki saikace garesa Akafara Aikin likitancin Ace *AKAN AIKIN MIJINA* baida lokacina habadai baba Audu kaduba wllh konida bawani nake cikin gidan ba nasan Hajiya tana cutuwa Badan komai ba Saidan *AKAN AIKIN MIJINTA* ni wllh dazan ga Y'an Uwanta nasamu damar magana dasu wllh saina fad'a musu halinda take ciki Wllh "

Sake Baki baba Audu yayi cikeda mamaki yace"Sale, Sale baruwanka shifa Baki shike Yankee wuya babu ruwanka kada kasake kayi wannan gangancin wllh babu ruwanka, Kuma yanzu darene gashi batasake ihun ba saboda haka kaje kakwanta yafi nima zankwanta Allah yakawo muna sauk'i"

Yana k'ananan gunguninsa yawuce ciki suma suka kwanta...

Washe gari sai kusan k'arfe 9:00 Am nasafe yadawo gidan hong yadanna Baba Audu yabud'e Masa, direct inda Akatanada Domin Aje motoci yashigarda tasa, fitowa yayi Ahankali hannunsa narik'e da jakarsa da lapcort D'insa sai wayoyinsa kallo d'aya zaka masa kahango gajiya taredashi, inda babu Audu ya tsaya suka gaisa cikin mutunci da girmamawa yanufi ciki gaskiya shi D'in maikyau ne Domin shiba dogo sosai ba Kuma ba gajere ba saidai yanada haske Sosai kamar idan katab'a shi jini yafito Musamman yanayin kalan Hutun da yake samu kansa d'auke yake da lallausan suma haka fuskarsa ta k'awatu da sake zuwa gemunsa Kai kawai ku hasko kyawonsa da kanku reader nabaku damar Amma doctor Muhayseem kam maikyau ne Ajin farko Acikin maza ga k'ud'i Kuma ga ilimi gamida Hutu, k'wararren likita ne kan Abunda yashafe fid'a indai shiga theater ne takan ko wane b'angare to doctor Muhayseem yayi fice Anan Domin har K'asan waje yake fita gudanarda Aikinsa, bayan gama master's d'insa can k'asar Indonesia sunso yasoma Aiki dasu Amma iyayensa suka hana kan saidai yataimake k'asarsa Nigeria Shima yanada ra'ayin hakan yasa yadawo gida Nigeria cikin iKon Allah Allah ya had'asashi da Muhseena Wanda kallo d'aya Yamata Allah yajarabceshinda mugun sonta cikin Amincewar Allah Akayi bikinsu,.

Parlour rufe yayi Mamakin ganin har k'arfe 9:00 nasafe parlour rufe master key d'insa ya d'auka yabud'e yashiga parlour da kallo yabi parlour Shima tsit babu kowa Kuma babu motsinta Anan, baikawo komai Aransa ba direct yawuce d'akinsa yarage Kayan jikinsa yashiga wanka, Koda yafito idanuwansa har rufewa suke saboda bacci Hakan yasa yazura jallabiyansa kawai yahaye gadon Tareda k'ara gudun AC yasoma bacci...........

_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

Whatsapp number 07064904617 or 07031012948

*AKAN AIKIN MIJINA! 🧟👹🧟* _FREE BOOK_

_Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK..., (29)GUBAR MATSAFA!!! HORROR STORY ☠️💀👹😈... (30)NUR RAINON D'AN FASHI!!! FREE BOOK. (31) ZUCIYA...Free book... (32) ƘARAR KWANA PAID BOOK ₦300..(33) YARIMA ASHMAN🤴🏻 (THE PRINCE) PAID BOOK 300 ONLY.. (34) SILAR GRADUATION PARTY, HORROR ☠️💀😈👹☠️💀 FREE BOOK. (35) SULTHAN ANEEM🤴👑 PAID BOOK. (36) And know AKAN AIKIN MIJINA🧟👹🧟 FREE BOOK is
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *AKAN AIKIN MIJINA! 🧟👹🧟FREE BOOK*

_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._
Chapter 3 · 0% Book details