← Book details Akan Aikin Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 20

Sashe 20

Akan Aikin Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Sallamar bakinsa ta mak'ale takasa fita sakamakon ganinta zaune rungume da baby tana bashi mama sunyi matik'ar kyau itada babyn sanye take cikin wata jar Atamfa tasha stone's Wanda D'inkin ya zauna jikinta d'as tazuge zip D'in gaban rigar tana shayarda babyn,

Jin kamar Anzuba mata ido yasa tad'ago Mutum tagani kansu tsaye kamar Wani mahaukaci d'an tsorata tayi har tana Shirin sake babyn k'asa, ai Kuwa da sauri yak'arasa Tareda rik'e babyn yafad'a hannunsa kuka yaron saki Domin yaji tsoro Kuma gashi yaji babu maman Abakinsa, Rintse idanuwansa yayi tareda Saka yaron jikinsa yana jijjigashi Zuciyarsa sai bugawa take da k'arfi fat fat fat fat kamar zata Yanko k'irjinsa tafito, yaron kuwa karon farko dayaji d'umin Mahaifinsa yasa yayi Shuru Tareda lafewa dukansu sukayi tsitt itadai kallonsa take cikeda mamakin ganin yarda halittarsa tasauya, wata d'aya ta d'auka bata ganshi ba Amma saitakejin kamar Shekaru tayi bata ganshi wata Irin kewarsa da Soyayyarsa gamida tausayinsa suka mata diran mikiya lokaci d'aya Jin hawaye naneman fito mata yasa tayi saurin maidasu cikin k'arfin Hali tace"Kai bawan Allah meya shigo dakai bako sallama Dan Allah bani yarona," tafad'a Cikin had'e gira

Sai a lokacin yabud'e idanuwansa yasaukesu Kanta,

Jin bazata iya juran kallon nasa bane yasa ta d'auke Kanta daga kallonsa tana sake cewa"kafita kabar gidan Nan Kuma kabani yarona,"

Cikin mamaki yace"Muhseenarh yau nike kora"?

"K'warai kuwa banason ganinka Kuma ni kabani yarona kada kashafa masa d'abi'unka narashin kula da bakasan komai ba sai *AIKINKA*,"

Jinjina Kai yayi cikin jinzafin kalamanta Amma yashanye saboda yasan shine Mai laifin yamata badaidai ba dole shine zaibada hak'uri

"Kiyi hak'uri Muhseenarh nayi nadama kan duk Abunda na Aikata Miki, Amma meyasa kinsan kina tareda jinina A duniyar Nan Baki fad'amun ba Kuma Baki Neman ba, balantana nayi zab'i suna ga yarona,"?

"Wazai nemeka Kai damuwa kayi da uwar tasa ko shikanshi yaron kan yazo duniyar kadamu dashine Yaranka nawa ka hallakawar badan komai ba sai *AKAN AIKINKA* idan ka manta Dr Muhayseem bari natina Maka to ciki d'aya biyu uku kana Salwantarmun dashi duka *AKAN AIKINKA* ko wannan Allah ne yanufe yasha dashima yazama gawar ai kamar yarda d'an Uwansa yazama dabadan *AKAN AIKINKA* ba ai da yanzu su biyu ne da Y'an biyu na Haifa, Amma saboda *AIKIN MIJINA* yasaka Tsawon Shekara 5 yaro d'aya gareni sauran duk sun halaka Ahakan kake tunanin nizan damu dakai Kona Tina dakai,? Kaga Mlm kada kab'amun lokaci ka b'atawa Kanka kawai ka sallameni saki uku nake buk'ata gareka Domin bazan jure zama da mutuninda baisan komai ba sai *AIKINSA* bazan iya bawa duniya labarin cewar *AKAN AIKIN MIJINA* nake Bak'in ciki ba, bani d'ana nace," tak'arasa maganar tana fisge Yaron daga jikinsa

Maidashi tayi jikinta ai Kuwa yaron yadinga tsala ihu yana kuka kamar Wani Mai hankali duk k'ok'arinta nayi Shuru k'iyayi,

Su hajiya kuwa duka suna daga baya suna kallon komai Dake faruwa hardasu Yasmin dasuka iso gidan,

Aunty kubra tace"yawwa kaga to Mlm ka rubuta sakin sauka bata ko,"?

"Auntie kubra Dan Allah kuyi hak'uri wllh natuba bazan sake sakaci Irin wannan ba, Indai *AKAN AIKINA* ne to wllh A shirye nake Dana hak'ura da Aikin Muhseenarh indai Zaki hak'ura kizauna Dani wllh zan hak'ura da *AIKINA* zan Aje AIKIN gaba d'aya Amma Dan Allah kada kibarni bazan iya Rayuwa babu keba," yak'arasa maganar yana kuka Sosai Yana k'ok'arin matsawa inda Muhseenarh

Saurin jabaya tayi duk da Abunda take na k'arfin haline Domin ita kad'ai tasan zafinda takeji gameda kukansa wllh ita kanta tanason Dr Muhayseem saidai *AKAN AIKIN MIJINTA* tana ganin Rabuwa dashi shine yafi sauk'i,.

"Kaga kawai ka Aiwatarda Abunda Auntie kubra tace nikaina bana k'aunar Ayanzu kawai karabu Dani Allah yabaka wata Nina Allah zaibani Wani"

Tamkar tasoka masa mashi haka yaji, Cikin rawar baki yace"Muhseenarh yau nike fad'awa nasakeki da bakinki? Kuma Agabana kikecewa Zaki Rayu dawani baniba,? Shikenan tinda sakin kikafi buk'ata Kuma shine zaisaki Farinciki zan sakeki Amma kisani inasonki Kuma. ....." Wani tarine yataso masa Wanda yahanashi k'arasa maganar kafin su Ankara kawai sukaganshi yafad'i k'asa Asume,"

Dagudu sukayo kansa hajiya da Faisal suna kuka suka d'auke shi suka nufe Asibiti dashi,.

Ai Kuwa yaron hannunta yasake sakin k'ara yadinga zunduma ihu kamar yasan Abunda ke faruwa ita kanta tamakar Wanda Aka sassak'o haka tadawo, Umma cema ta Anshe yaron tasoma jijjigashi Amma Ina yak'i Shuru kamar Mai wayo,

Cikin Jin takaicinsu Yasmin tace"Haba auntie kubra ku tausayawa bawan Allah Nan mana yayi laifinnan yanzu Kuma yatuba yana Bada hak'uri kuyafe masa mana, wllh Muhseenarh bakida masoyi a yanzu sama da Dr Muhayseem Dan Allah kibawa Zuciyarki hak'uri Kuma kinsani cewar kawai Ansamu damar zubarda cikin ne saboda sakacinsa da Rabin kulawarshi Amma bawai shine silaba kawai *AKAN AIKIN MIJINKI* ne Akasamu damar shigardaku matsalan, Niba ganiba Muna tare da Dr Faisal kinfi kowa sanin RAUNIN da faisal yasamun *AKAN AIKINSA* yafi naki, ke cikinki kika rasa da kwanciyar hankali *AKAN AIKIN MIJINKI* nikuwa Mutuncina k'imata soyayya ta hak'uri na duk rasa *AKAN AIKIN MIJINA* kada kizama d'aya daga Cikin marasa Afuwa mana, yanzu so kike yarasa ransa ko me,"

Sai Alokacin tasamu damar sakin kuka tana fad'in"Dan Allah kukaini inda yake inason mijina wllh inason Dr Muhayseem na Hak'ura nidai Koda *AKAN AIKIN MIJINA* zanmutu naji zan Rayu dashi,"

Itakanta aunty kubra Jikinta yayi sanyi Ayanzu Kuma ta tabbatar zai daina halinsa, dukansu suka d'unguma zuwa Asibiti,

Koda suka isa waje suka tarandasu hajiya na kuka Sosai, shikuwa yana cikin emergency room Domin Zuciyarsa ce tabuga tacikin glass taga Yarda likitocin suke Neman dawoda numfashinsa Wanda ke barazanar guduwa, ai da sauri taturesu Husna tafad'a d'akin Hannu tasa tafisge oxygen D'in ta d'aura Bakinta kan nasa tasoma Hura masa iska gamida danna masa saifin Zuciyarsa

Komawa gefe likitocin sukayi suna kallon iKon Allah,

Hannuwanta tasaka tana dukansa Tareda cire bakinta cikin kuka tace"katashi ni kada katafi kabarmu kada kamaida Anam Maraya katashi na Hak'ura zanrayu dakai na Amince zan iya zamadakai *AKAN AIKINKA* zan iya jure komai *AKAN AIKIN MIJINA* Amma bazan jure rasa Mijina ba," tak'arasa maganar tana kuka sosai,

Dukansu Saida suka tausaya Musu gamida jinjina Irin soyayyarda ke tsakaninsu,

Kanta ta d'aura masan Zuciyarsa tana kuka sosai Mai ban tausayi, Ahankali yasoma Wani tarin kafin ya Bud'e idanuwansa, jinkukanta yake har cikin k'wak'walwarsa hannunsa yad'aga gamida rungumota jikinsa tare suka sauke Ajiyar Zuciya, kallonsa tayi tasaki murmushi Shima murmushin yasaki,

Tafi sukaji Abayansu da hanzari tawaiwaya Ganin su Faisal da Sauran Dr's D'in suna Musu murmushi sai kunya takamata tayi Saurin k'wace jikinta tafiya dagudu, Aikuwa suka sake sakin dariya shikuwa mik'a Hannu yake yana Kiran tadawo Amma Ina batamasan yanayi ba,

Shigowa su hajiya sukayi suna masa Anam Daketa kuka ya karb'a ai Kuwa yayi Shuru

Umma tace"Kinganmun ja'iri waifa yayi Shuru, ai Kuwa zakayi bayani duk randa kazomin gida,"

Dariya sukayi dukansu,

Ba'ad'auke Wani lokacin ba Aka sallameshi,

Zama na Musamman Akayi tadeda iyayensu nanne take Bada Labarin dakwai Aljanin Agidan bazata iya komawa cikinsa ba saidai yanemamata wani,

Tun Anan Daddy yabasu Wani gidan kansu komacan waccan kuwa za'ayi masa karatu

Hakan kuwa takasance saiga Aljanin yabayyana bayan Mlm yayi karatunsa Nan yake fad'in shi turosa Akayi Adaina k'onasa,

Mlm sani yace"waya turoka to,"

*Ubangidana shine yaturoni Shima Aiki Akabasa sunanta Zeeza itace Silan zuwana nan, Kuma nasamu damar bata wahala ne dama shiga gidan Saboda sakacinda tafara Kuma bamusamu damar samun sakacin nataba Saida ta shagala da Damuwa *AKAN AIKIN MIJINTA* tanan muka samu damar Aiwatarda komai"

Cikin mamaki Dr Muhayseem yace"Zeeza"?

Mlm yace"kasanta ne,"?

"K'warai kuwa Mlm nasanta"

"To daga baya mayi magana Kanta,"

"Yanzu Kai inason karabu da bayin Allah Nan duka kafita Rayuwarsu har Abada,"

"Ni bazan iya sab'awa Ubangidana ba, Domin Akwai Amana tsakaninmu"

"To ai shikenan kaida Ubangidan naka Kuwa duka zaku mutu Kuma Allah zai Muku Hisabi kafin kaje katarda naka Hisabin kafin kaje Yanzu zan k'onaka,"

Ayoyin Qur'ani yashiga karantamasa

Ihu yafara zanfita zanbar gidan zanbar Rayuwarsu, kadakata zantafi,

Dakatawa Mlm Yayi kamar hayak'i haka yatashi sama yabi tacikin Celine yatafi

"Masha Allah yanzu dai babu Wani ragowar Wani iska tareda ku saidai Kaine zaka k'ara dagewa gurin bawa Matar kulawa hankalinta kwanta tanan zatasamu damar Maida hankali kan ibadarta itama, kudaina d'aukar Imaninku kacokam Kuna d'aurawa *AKAN AIKINKU* Wani wllh saboda AIKINSA baidamu da ibadaba Wani sharholiyar yasake bako tuna mutuwa, Musamman wannan zamanin saikaga Mutane masu Aikin Asibiti dama Malaman boko saikasamesu dayawan ma'amala da matan banza Wanda sune kawai suka d'aurawa kansu wannan bak'ar Agida bazanso Jin ko wacce garekaba Amma Dai kagani Kaga Abunda yafaru yabzu saika kiyaye gaba kamaida hankali Kuma kaji tsoron Allah *AKAN AIKINKA* Domin shikanshi *AIKIN* naka Abun tanbaya ne gareka gobe k'iyama saboda haka sai A k'ara kula Allah yakaremu,"

"In sha Allah Mlm zamu kula mungode sosai"

"Kai Ina taya Hakan zata faru haba boka bakamun Alk'awarin zasu rabu ba taya yanzu Kuma zakace Aljanin yadawo amma...."

"Ke rufemin Baki Anan Ina Miki maganar Ank'onamin Aljanina kinamun zancen banza shasha kibar gurin Nan kafin Raina yab'aci Kuma keda Aure har Abada Domin wannan Aljanin damuka tura yafusata Yanzu haka Ina biye Dake dashi Zaki Rayu,"

Mik'ewa tayi cikin firgici tabar gurin bokar tana waige waige harta kawo bakin tatin Sam bata cikin hayyacinta batareda taduba ba taje tsallake titin take wata k'atuwar mota tabi takanta Nan take mutuwarta taziyarceta,,

Yanzu basuda damuwar komai sai Farinciki da Walwala gamida k'aunar juna Saida tanuna fushinta da b'acin ranta kafin tasamu Dr Muhayseem yakoma kan Aikinsa,..

BAYAN SHEKARA UKU

A yanzu yaransu Dr Muhayseem 5 Maza 2 mata 3, inda su Yasmin kuwa yaransu 6 su khaleepha da Khairat kuwa Anyi Aure,

Zaune suke iyayen suna fira suna dariya cikin raha,

Yasmin tace"Yanzu dai *AKAN AIKIN MIJINA* Ina Alfahari dashi, tafad'a tana Kashe masa ido d'aya,

Muhseenarh tace"to nidai yanzu *AKAN AIKIN MIJINA* ai saidai sanbarka da k'arin soyayya Yarda nake samun kulawa kuwa ai ko jinjiri Albarka, sab'anin da danakejin *AKAN AIKIN MIJINA* gwanda Rabuwa to yanzu *AKAN AIKIN MIJINA* Saidai mutuwa nidashi,"

"Nikaina Saida na k'ara Banda hak'uri Kuma kullum ina cikin godiya ga Allah daya bani ikon gyara halina *AKAN AIKINA* Kuma nasamu damar faranta ran matana *AKAN AIKINA* Dr Muhayseem ya fad'a yana rungumarta

"Nikaina danafi kowa b'arna *AKAN AIKINA* yanzu saidai nace Alhamdulillah Kuma hak'ik'a samun Macce Mai ilimin Addini wllh baiwane Kuma dace Allah yak'ara tsaremu da Imaninmu dama *AYUKANMU*,"

Da Ameen suka Ansa dukansu cikin Farinciki da nishad'i,.............

TAMMAT BI HAMDULLAH

ANAN KAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFIN NAWA, ALLAH KABANI LADAN ABUNDA NAYI MAIKYAU ACIKI INDA MARA KYAU KUMA ALLAH YAK'ARA KAREMU DUKANMU KUMA ALLAH YABAMU IKON GYARA RAYUWARMU DAMA GOBENMU,..

KUMA INASON KUSANI YAWAN LITTAFI BASHINE KYAWONSABA , ZAYYANA FITSARA KO BATSA BASHINE KYAWON LITTAFI BA, ABU MAFI KYAU SHINE KATSAYA CIKIN NATSUWA KAYI LABARI WANDA ZAIBADA MA'ANA DA WA'AZANTARWA DAMA FAD'AKARWA GAMIDA ILIMANTARWA......ALLAH YASA MUDACE 🤲 SAIMUN SAKE HAD'EWA CIKIN LITTAFINA NAGABA, TAKU HAR KO YAUSHE ✍️ MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR QUEEN OF WRITER'S HAUSA NOVELS 📚📖📚 AND DESIGN GRAPHICS

_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

Email [email protected]

Whatsapp number 07064904617 or 07031012948
Chapter 20 · 0% Book details