← Book details Akan Aikin Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 20

Sashe 10

Akan Aikin Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

1️⃣ Yawan ciwon kai mai tsanani da jiri.
2️⃣ Ciwon mara, baya da kwankwaso.
3️⃣ Jin motsi a gabanki kamar tana, ko jin motsi a cikinki yana zuwa bangare-bangare.
4️⃣ Jin abu kamar ƙiyashi na bin jikinki, ko kamar tsutsa, haka nan zaki rinka jin motsi a kanki kamar wani abu na tafiya.
5️⃣ Jin wani abu mai ɗan nauyi ya kwanta a wani bangare na jikinki, wani lokaci ya tashi daga wannan wurin ya koma wani wurin.
6️⃣ Jin zafi ko sanyi a tafin kafarki, ko kiji wannan wurin yayi dumi kamar an sa wuta, can kuma sai ya matsa ya koma wani wurin.
7️⃣ Jin wani abu kamar yana haɗiye ki.
8️⃣ Rashin son kitso ko wani abu da zai taba kanki, zubewar gashi, da sauransu.
9️⃣ Rashin barci da daddare.
🔟 Yawan faduwar gaba da tsorata da abu ƙanƙani.
1️⃣1️⃣ Rashin son mutane da gudun mutane, da tsoron mutane in ta shiga wurin da akwai mutane da yawa kamar kasuwa, da rashin son magana da mutane.
1️⃣2️⃣ Yawan fushi da tsiya, kiji kowa ma haushi yake baki haka nan kiji kin tsani mutane.
1️⃣3️⃣ Qin aure, da rashin son maza. Mace taji bata son namiji yace yana sonta, ko yace zai turo gidan su.
1️⃣4️⃣ Zaki rinka ji kamar ana miki magana, ana cewa ki aikata wani mugun abu, ko idan kina kallon wuƙa sai kiji kamar ana cewa ki coka ma wani.
1️⃣5️⃣ Yawan jin zafin jiki, kasala da kuma ciwo na rashin dalili.
1️⃣6️⃣ Yawan son kade-kade da raye-raye, wato aljani zai rinka saki yin wasu abubuwan da da can ba halinki bane.
1️⃣7️⃣ Yawan kallon madubi da yawaita kallon jikinki tsirara a madubi.
1️⃣8️⃣ Son dare, da son zama a cikin duhu.
1️⃣9️⃣ Jin kamar ana kiran sunanki ko firgita yayin da kike ke kadai a wuri.
2️⃣0️⃣ Yawaita kuka na rashin dalili.
2️⃣1️⃣ Qin karatun Al-Qur’ani, da kasa karanta shi ko ɗaukansa.
2️⃣2️⃣ Jin kamar ana tsira miki allura a jikinki.
2️⃣3️⃣ Rashin jin daɗin saduwa da mijinki da tsanar shi yayin da ya nuna alamar yana son saduwa da ke.
2️⃣4️⃣ Aljani zai iya sanyawa mace mugun infection ta yi ta fama yaƙi warkewa.
2️⃣5️⃣ Jin kamar kin aikata wani abu ba a cikin hankalin ki ba.
2️⃣6️⃣ Ganin inuwa kamar na wani, ko kiji an danne ki baki iya numfashi, sai kin yi addu’a sannan kika tashi.
2️⃣7️⃣ Yanke jiki ki fadi ba tare da sanin inda kanki yake ba.
2️⃣8️⃣ Jin kamar an daura miki dutse a zuciyar ki, ko kiji an matse miki numfashin ki.
2️⃣9️⃣ Samun ciwukan da da can baki da su, wanda likita zai duba ya rasa dalili.
3️⃣0️⃣ Yawan waswasi musamman a ibada.
3️⃣1️⃣ Rikitar miki da al’ada, jini ya dauke sai kin yi tsarki kin yi sallah sai kawai ki sake ganin jini.
3️⃣2️⃣ Hana haihuwa.
3️⃣3️⃣ Zama da datti da ƙazanta.
3️⃣4️⃣ Sumbatu da firgici a cikin baccin ki.
3️⃣5️⃣ Lalacewar jiki ko ciwo a wani sassa da aljani ke zama.

Wadannan da kuma wasu suna daga cikin alamar akwai aljani a tare da mutum.

---

SHAWARWARI GA MASU JINNU

Duk wanda yake fuskantar matsalolin jinnu akwai abubuwan da ya kamata ya fahimta kuma ya kiyaye:

1️⃣ Yadda mutane ke ganin tasirin magani yana da nasaba da yadda zuciyarsu take. Idan kana da kokwanto, abu mai wuya ne ka ga tasirin sa.
2️⃣ A kiyaye hakuri da gujewa gaggawa yayin neman magani.
3️⃣ Kada a fara magani sai a watsar bayan an samu sauki.
4️⃣ Kada a nemi magani ta hanyar zuwa wurin boka ko malamin duba.
5️⃣ A tabbatar da yin yaƙi da zuciya wajen amfani da addu’o’i da magungunan Manzon Allah.
6️⃣ A tsananta addu’a da roƙon Allah.
7️⃣ A koya da haddace addu’o’in kariya, musamman na safe da yamma.

Ina roƙon Allah ya kare mu daga sharrin shaiɗanu!

AMEEN

*Page 51 to 60*

......... Asibitinda suke Aiki sale yakaisu suna zuwa kuwa Emergency ganin jinin yana zuba iya tashin Hankali Yasmin tashiga Musamman ganin jinin baidaina zuba ba, ciki sukayi da ita suka soma bata taimakon gaggawa, yawo tafara Agurin tana share hawaye,

" Amma madam maizai hana kinemeshi tinda naga Nan yake Aikin"

Sai Alokacin tatuna harda fa Faisal Nan yake, juyawa tayi tanufe office D'insa saidai office D'in rufe, security Dake tsaron Bakin k'ofar yace"Madam basanan fa sunfita Sallah"

Batace komai ba tajuya motar tabud'e ta d'auke wayarta dariyar Kiran faisal saidai ganin missed barkatai daga Auntie kubra kafinma tayi Wani yunk'urin Wani Kiran yasake shigowa tad'auka duk Afirgice take tace"wllh Auntie kubra babu lafiya cikin mugun yanayi nasameta duka hankalina tashe yake shiyasa bankira kiba"

Mik'ewa tsaye auntie kubra tayi Cikin dabircewa tace"Meke faruwa da ita? wane hali take ciki yanzu? Ina shi mijin nata Dr Muhayseem D'in,"?

Batasamu damar Ansamata tanbayoyin ba Sale yanufota da sauri yana fad'in"wai Dan Allah bakida number shine ki kirashi sunce dole saisunga mijinta Kuma wai suna buk'atar kijini Domin tasamu miscarriage,"

"Miscarriage!? Wai cikin shine yazube,"?

"Haka sukace wllh"

"Nashiga Ukku kinji Auntie kubra wai cikin yazube tayi miscarriage "

"Subhanallah innalillahi wa Inna ilaihin rajiunn"

Shine kawai Abunda auntie kubra take maimatawa Tareda zama tana dafe kanta,

Yasmin kuwa dama tadatse Kiran tasoma kiran Faisal Saida takusa katsewa yad'aga

Cikin mugun Haushinsu suduka tace"Idan kasamu lokaci saika fad'awa Shashan Abokin naka dama halinku d'aya saidai banbanci ku kad'an ne, ka fad'amasa idan zai iya gamunan Asibiti Muhseenarh babu lafiya Kuma Ana buk'atar jini sannan haryanzu babu likita Kanta" batajira Ansarsaba takashe wayar wllh haushi sukebata dukansu, k'ofar word D'in takoma

Cikin Damuwa yace"Madam ce Kuma tace suna Asibitin Nan takawo Madam D'inka babu lafiya"

Cikin tashin hankali yamik'e yafito baiko saurare Kiran nasaba yanufo cikin hospital D'in bayan gama sallarsu ne Faisal yajasa Siyan Dambun nama,

Dama babu nisa Sosai Hakan yasa take ya iso, baiko tsaya yin magana ba yashiga d'akin cikin tashin hankali,

Drip kawai suka sakamata sukabarta Domin Basu biya dukan k'ud'in Aikin ba kuma Basu Bada jinin ba Hakan yasa sukabarta,

((Hunmm kad'an daga cikin halin ma'aikatan Asibiti kenan zuwa kansu doctor's D'in, Koda yake yanzu komai na k'ud'ine bawai Dan Allah ba tho Allah dai Yasa mudace....))

K'ok'arin treating d'inta yafara dakansa ganin Hakan yasa nursing D'in suka shiga taimaka masa jininsa yabada Akasamata Saida ganin komai yalafa kan yakoma gefe yazauna share gumi cikin tashin hankali da damuwa Domin kuwa cikin yariga yazube Kuma Hakan yasamune saboda yawan jinin da tazubar gashi batasamu taimako kan lokaci ba,

Ai Kuwa yafufe duka nursers D'in gurin da Fad'a kamar zaidakesu, Saida falsal yashiga lamarin tareda Basu umarnin barin gurin

Zama yayi k'asa Tareda dafe kansa Domin juyamasa yake gashi jininda yabada bashiri yasa yakeganin jiri

"Kanatsu mana Dr kaimafa na buk'atar bed rest D'in saboda bada jinin cikin rashin shiri,"

D'aga masa Hannu kawai yayi Alamar yarabu dashi, shi K'ad'ai yasan yaya yakeji A Zuciyarsa na Rashin wannan cikin Domin yasaka ransa da soyayya ga Cikin gashi Kuma shine silar zubewar jikin nasa,..

"Waimeke faruwane ne naga kina had'a kaya"

"Ina lafiya nakasa rik'e Amana inanan y'ar uwata tanacan tana wahala ni Nigeria nakeson komawa yanzu"

"Nigeria kuma Momyn Khairat? Kinfasan komai basai nagaya Miki ba Ina kowa Nigeria yanzu Babu Shiri ko booking tickets bamuyi ba Kuma babu shiri, waima meke faruwane wacce Irin wahala waya gayami Muhseenarh tana da damuwa,"

Hawaye tasoma"wllh Abban Khairat da matsala dama inajin Hakan Ajikina gameda ita sai yanzu Kuma nakejin tana Asibiti Kuma tasamu miscarriage nidai Amin duk Abunda za'ayi gaskiya Nigeria nakeson komawa inason ganin y'ar Uwata"

"To shikenan zakiji Amma bayanzu ba Amma kinatsu kifara kwantarda hankalinki kinji," lallashinta yasoma hardai yasamu ciyo Kanta ta hak'ura saidai tacigaba da Kira...

Bayan wasu A wanni Ahankali tashiga ware idanta komai yashiga dawo mata kamar yanzu cikin firgici tamik'e Zaune Tareda sakin k'ara,

Shigowa Yasmin tayi Cikin sauri tazo gefenta inda Dr Muhayseem dama yajima da rik'eta tinda yana d'akin tareda ita, rungumarta yayi yana bubbuga bayanta tareda mata Addu'a Ganin kamar bama Cikin hayyacinta takeba, sunma suna tofa mata Addu'ar harda Yasmin

Saican tadawo daidai Kuma sai lokacin idanta ya sauka kan cikin nata bataji motsin komai ba Kuma bataga Cikinba,

Cikin sark'ewar murya tace"Muhayseem Ina cikina banji motsinsaba, Yasmin Wllh cikina baya motsi"

Matsawa baya Yasmin tayi tana hawaye

"Me Hakan kenufi yasmin kukan me kike? Meyasa baka bani Ansar tanbayana ba Muhayseem Ina cikina, kada dai kacemin narasa cikina,"? Tak'arasa maganar tana hawaye Sosai Tareda shafa cikin nata.

"Saidai Muyi hak'uri Muhseenarh Amma kinyi miscarriage"

"Innalillahi wa Inna ilaihin rajiunn, cikin yazube fa"

"Kiyi hak'uri my dear K'addara ce Kuma...."
Yimin Shuru Muhayseem!! Tafad'a Cikin b'acin rai, tareda k'wace jikinta daga nasa tace"Kaine Sila wallahi Kaine silan zubewar cikin nawa Muhayseem Domin baka damu dani ba balantana kulawa *AKAN AIKIN MIJINA* narasa d'an cikina!!!......…...............

_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

Whatsapp number 07064904617 or 07031012948

*AKAN AIKIN MIJINA! 🧟👹🧟* _FREE BOOK_

_Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
Chapter 10 · 0% Book details