← Book details Akan Aikin Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 20

Sashe 16

Akan Aikin Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

1️⃣ Yawan ciwon kai mai tsanani da jiri.
2️⃣ Ciwon mara, baya da kwankwaso.
3️⃣ Jin motsi a gabanki kamar tana, ko jin motsi a cikinki yana zuwa bangare-bangare.
4️⃣ Jin abu kamar ƙiyashi na bin jikinki, ko kamar tsutsa, haka nan zaki rinka jin motsi a kanki kamar wani abu na tafiya.
5️⃣ Jin wani abu mai ɗan nauyi ya kwanta a wani bangare na jikinki, wani lokaci ya tashi daga wannan wurin ya koma wani wurin.
6️⃣ Jin zafi ko sanyi a tafin kafarki, ko kiji wannan wurin yayi dumi kamar an sa wuta, can kuma sai ya matsa ya koma wani wurin.
7️⃣ Jin wani abu kamar yana haɗiye ki.
8️⃣ Rashin son kitso ko wani abu da zai taba kanki, zubewar gashi, da sauransu.
9️⃣ Rashin barci da daddare.
🔟 Yawan faduwar gaba da tsorata da abu ƙanƙani.
1️⃣1️⃣ Rashin son mutane da gudun mutane, da tsoron mutane in ta shiga wurin da akwai mutane da yawa kamar kasuwa, da rashin son magana da mutane.
1️⃣2️⃣ Yawan fushi da tsiya, kiji kowa ma haushi yake baki haka nan kiji kin tsani mutane.
1️⃣3️⃣ Qin aure, da rashin son maza. Mace taji bata son namiji yace yana sonta, ko yace zai turo gidan su.
1️⃣4️⃣ Zaki rinka ji kamar ana miki magana, ana cewa ki aikata wani mugun abu, ko idan kina kallon wuƙa sai kiji kamar ana cewa ki coka ma wani.
1️⃣5️⃣ Yawan jin zafin jiki, kasala da kuma ciwo na rashin dalili.
1️⃣6️⃣ Yawan son kade-kade da raye-raye, wato aljani zai rinka saki yin wasu abubuwan da da can ba halinki bane.
1️⃣7️⃣ Yawan kallon madubi da yawaita kallon jikinki tsirara a madubi.
1️⃣8️⃣ Son dare, da son zama a cikin duhu.
1️⃣9️⃣ Jin kamar ana kiran sunanki ko firgita yayin da kike ke kadai a wuri.
2️⃣0️⃣ Yawaita kuka na rashin dalili.
2️⃣1️⃣ Qin karatun Al-Qur’ani, da kasa karanta shi ko ɗaukansa.
2️⃣2️⃣ Jin kamar ana tsira miki allura a jikinki.
2️⃣3️⃣ Rashin jin daɗin saduwa da mijinki da tsanar shi yayin da ya nuna alamar yana son saduwa da ke.
2️⃣4️⃣ Aljani zai iya sanyawa mace mugun infection ta yi ta fama yaƙi warkewa.
2️⃣5️⃣ Jin kamar kin aikata wani abu ba a cikin hankalin ki ba.
2️⃣6️⃣ Ganin inuwa kamar na wani, ko kiji an danne ki baki iya numfashi, sai kin yi addu’a sannan kika tashi.
2️⃣7️⃣ Yanke jiki ki fadi ba tare da sanin inda kanki yake ba.
2️⃣8️⃣ Jin kamar an daura miki dutse a zuciyar ki, ko kiji an matse miki numfashin ki.
2️⃣9️⃣ Samun ciwukan da da can baki da su, wanda likita zai duba ya rasa dalili.
3️⃣0️⃣ Yawan waswasi musamman a ibada.
3️⃣1️⃣ Rikitar miki da al’ada, jini ya dauke sai kin yi tsarki kin yi sallah sai kawai ki sake ganin jini.
3️⃣2️⃣ Hana haihuwa.
3️⃣3️⃣ Zama da datti da ƙazanta.
3️⃣4️⃣ Sumbatu da firgici a cikin baccin ki.
3️⃣5️⃣ Lalacewar jiki ko ciwo a wani sassa da aljani ke zama.

Wadannan da kuma wasu suna daga cikin alamar akwai aljani a tare da mutum.

---

SHAWARWARI GA MASU JINNU

Duk wanda yake fuskantar matsalolin jinnu akwai abubuwan da ya kamata ya fahimta kuma ya kiyaye:

1️⃣ Yadda mutane ke ganin tasirin magani yana da nasaba da yadda zuciyarsu take. Idan kana da kokwanto, abu mai wuya ne ka ga tasirin sa.
2️⃣ A kiyaye hakuri da gujewa gaggawa yayin neman magani.
3️⃣ Kada a fara magani sai a watsar bayan an samu sauki.
4️⃣ Kada a nemi magani ta hanyar zuwa wurin boka ko malamin duba.
5️⃣ A tabbatar da yin yaƙi da zuciya wajen amfani da addu’o’i da magungunan Manzon Allah.
6️⃣ A tsananta addu’a da roƙon Allah.
7️⃣ A koya da haddace addu’o’in kariya, musamman na safe da yamma.

Ina roƙon Allah ya kare mu daga sharrin shaiɗanu!

AMEEN

_3/4/2025 Thursday/ April_

*Page 91 to 98*

```SECOND TO THE LAST PAGE IN SHA ALLAH```

..........Da sallama Auntie kubra tashigo d'akin, Inna labara ce parlour ta Ansa mata tazauna suka shiga gaisawa cikin kulawa, dama Aunty kubra batada girman Kai Hakan yasa kamar tasan Inna laraba,

"Halan masu gidan basananne kece kawai Inna,"?

"Eh shidai Dr bayanan kinsan dama bazama yakeba to ita yanzu ma ba'a jima sosai ba tatashi Nan inda kika zauna tacemin zata mik'a tahuta, kinsan masu ciki basajin dad'in zama guri d'aya Musamman Yanzu daya fara girma dole taga canji kala kala,"

"Hakane kam Allah dai yarabasu lafiya, bari nashiga naganta batasan da zuwana ba bazata namata"

"Ameen Ameen, Ah to lalle tho ko yau munada Bak'i Ashe"

Tana dariya tashiga parlour da sallama Shuru zama gefen gadon tayi tana tunanin kota toilet ne? Ganin tajima yasa tanufe toilet d'in tad'an kara kunnenta jikin k'ofar waikotaji motsi Amma Shuru Hakan yasa tad'anyi nocking nanma Shuru, Hakan yasa tatura k'ofar tasaka Kanta ciki tana waige waige kwatsam idanuwanta suka fad'a kanta tana yashe k'asa bako Alamar Rai tareda ita jini yana tazuba harda gudajinsa tak'asan k'afafuwanta fuskarta takumbura jinin yana zuba tabakinta,

K'aramin k'ara tasake tareda fad'in"Innalillahi wa Inna ilaihin rajiunn, Muhseenarh! Muhseenarh!! Muhseenarh!!!" Tafad'a tana k'ok'arin janyota jikinta tana kuka,"

Jiyo ihun nata yasaka su Inna da sale sukashigo d'akin toilet D'in kaitsaye sukanganta rumega Ida tana kuka sosai,

"Innalillahi wa Inna ilaihin rajiunn, Kai Amma Anyi tsinannen Miji Wllh gashi ko Yanzu *AKAN AIKIN MIJINTA* tasake shiga Wani hatsari,"

Tsaida kukanta Auntie kubra tayi tareda juyowa takallesa cikin mamaki tace"dama *AKAN AIKIN MIJINTA* take fuskantar hatsuruka Irin Wad'annan,"

"Sosai ma Kuwa wallahi dama ni Ina jiran randa zansamu dama naga Wani jininta nafad'a masa gaskiya Kai Koda nayi yunk'urin fad'ar gaskiya baba Audu shike Hanani wai kada nashiga tsakanin ma Aurata, Amma Wallahi nidai tinda nazo gidan Nan bata tab'a shafe sati d'aya da Farinciki ba, koda yayi sanyi kamar zaidaina to wallahi kwanciyar d'aukar Rai yayi gameda mata wayo datagama warwarewa zaisake komawa y'ar gidan jiya, Indai *AKAN AIKINSA* ne to bazaka tab'a Gane kansaba, baida lokacin kowa komai saina *AIKINSA* Shidai *AIKINSA* shine Rayuwarsa, ko cikin farko daya zube Wallahi babu Wani dalili face *AKAN AIKIN MIJINTA*"

Wata nannauyar Ajiyar Zuciya tasauke Mai d'auke da zafi, "Kutaimakamin mukaita Asibiti,"

Dataimakon Inna laraba sukakaita Asibiti wannan karon wata Asibitin daban takaita Emergency Akashiga da ita, duk iya k'ok'arin sunkasa tsaida jinin numfashin natama yasaka dawowa, dole Auntie kubra takira su Umma cikin k'ank'anen lokaci suka iso ganin Irin yanayinda take ciki naruwa da mutuwa yasa Abba yasoma cuku cukun yankamusu ticket zuwa birnin New York, Sale ne dakansa yakira su hajiya ya fad'amusu, Hajiya takira Dr saidai wayar bata Shigaba dole suka nufo Asibitin, Wani Dr yafito yana sharce gumi yace"Jikinta yayi tsanani Sosai dakwai buk'atar Ayimata theater Kuma dakwai na'urori na Musamman da za'a buk'ata Kuma wannan Aikin yanada hatsari yana buk'atar k'warewa dole dai sai Annemo Dr Muhayseem Domin shine da k'ware tawannan gefen,"

"Babu buk'atarshi Anan zamu d'auketa daganan zuwa k'asar waje nasan Acan za'ayi solving matsalar" cewar Aunty kubra cikin fushi

Ko kula su hajiya Dake magana batayi ba,

"Wai to meyayi zafi kubra dazakice ba'anemansa mijinta nefa kobayan zamansa Dr D'in yafi kowa Hake Kanta"

"Au haba shindama yana da hakke akanta to ai bansani bane tinda banga hakken nata daya sauke ba, yana da hakke ita Batadashi kansa Kenan Hajiya,"

"Taya Zaki fad'i Hakan kubra ai kinfi kowa sani kan Miji nada hakke kan matarsa hakanma matar tanadashi kan mijin,"

"Masha Allah gwanda dakika fad'a dakanki cewar itama tanada hakke kansa to ki fad'amun wane hanke nata ya sauke, Banda Wahala da Bak'inciki metasamu Agidan Auran nashi, Mutum baisan komai ba sai *AIKINSA* kawai yasawa neman duniya gaba yana neman kashe Muna ita, badan komai ba sai *AKAN AIKINSA* saunawa tayin miscarriage? Kuma ba silar kowaba sai shi Mijin nata Dr Muhayseem Kuma babu Wani dalili face *AKAN AIKINSA* shikenan ita haka zata k'are cikin zubewar ciki da K'unci da Bak'inciki tana fad'in cewar *AKAN AIKIN MIJINA* narasa Farinciki to wllh bazaiyu ba idan Ada Anyi bananan to Wllh yanzu nadawo Kuma dole yasake ta bazaiyu tazama Macce tafarko daza'a buga kan jarida cewar *AKAN AIKIN MIJINA* narasa Farinciki hartakaiga rasa Rayuwa, inda Wani ne ai da yanzu yazo, kira nawa Ana masa daga k'arshe ai kashe wayarsa yayi badan komai ba saidai yanuna cewar *AKAN AIKINSA* zai iya barin komai to badamuba wllh badamuba Hajiya,"

"Kubra yau nike kallo idona kike fad'amun maganganu Hakan bako tuna surukantaka haba ai yakamata kisan da K'addara"

*Amma ko kinbani mamaki K'addara fa kice to idan K'addara ce kijira ta fad'a kan sauran y'ay'anki mata Kinga kinada kan d'auka saiki d'auka maganar kuwa dole na fad'amiki domin d'an kuka shike jawa Uwarsa jifa, inma banda k'in gaskiya ga komai Bayyane Amma kikasa bin gaskiya,"

"Ke Aunty kubra ya isheki wllh bazaiyu kisaka Mahaifiyarmu gaba kina gaya mata Magana ba Kuma kina k'ok'arin muzanta d'an Uwanmu gabanmu ba," cewar hafsat,"

"To K'aramar kunya zokidakeni nace kizo kidakeni tanan zansan kincika mara kunya, Kuma...."

"Ya isa haka kubra ta lafiyarta Yakamata mubi bawai ta Wannan hayaniyar ba muje kawai," mama tafad'a tana kuka Tareda bin bayan nurse's d'inda suka gunguro Muhseenarh kan gadon kamar gawa zuwa mota Domin kaita waje, duk rigimar da Ake dai Abbanta baya gurin Domin yaje Yanko ticket,

Motar Akasata suka wuce airport direct Basu jima ba kuwa Abunka da Manya take jirginsu ya d'aga Kuma already Abba yayi magana da Dr Sabeer dake can new York D'in,

Su hajiya kuwa jiki ba k'wari Musamman ganin halinda Muhseenarh take suka nufo waje tanan suka Had'u da Yasmin tana k'ok'arin shiga tsayawa tayi tana tanbayarsu lafiya, Husna ce Dake kuka ta tsaya tabata labarin sunwuce da ita,

"Ya sallamm Allah kaceci wannan baiwar taka kabata iKon cinye wannan Jarabawar tata,"

Dawowa baya Hajiya tayi tace"Yasmin nasan kinsan Muhseenarh sosai tinda batada wata k'awa sama Dake shin da gaskene Dr Muhayseem baidamu da itaba sai *AIKINSA*? Shin dagaske ne *AKAN AIKIN MIJINTA* tarasa cikin nata har sau 2 kuma gana 3 cikin hatsari,"?
Chapter 16 · 0% Book details