← Book details Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 27

Sashe 9

Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

barci, amma bata da password din da zata yi amfani da WiFi din gidan. Sannan bata da kudi a wayar ma balle tayi kira na kai tsaye, kwarai take son kiran Nenne da Ummanta ta gaya musu yadda ta sauka lafiya. Son samu har Dade mai sonta da son kwanciyar hankalinta ta kira don ya tabbatar ta kwantar da hankalinta. Anan kan kilishin da tayi sallah da waya a hannu barci mai nauyi ya dauke Aisha Siddiqah Yunus a gidan Prince Abdulrasheed (Kehinde). Barci take yi na gajiya da tsamin jiki wanda zaman jirgi na awanni masu yawa ya haifar mata, ba ita ta samu farkawa ba sai asubahi. Ta saba ji a jikinta idan asubah tayi, ba tareda kowa ya tasheta ba ko taji kiran sallah. Yau dinma jikinta ne ya bata cewa asubah tayi, Siddiqah ta bude ido a hankali tana salati da mika. Ta fadawa kanta; “Kwana na farko a gidan Bayeraben miji na!”. Tun daren jiya ta yi wa kanta alkawarin bazata kara kuka ba, ta karbi auren Prince a matsayin kyakkyawar kaddararta. Ta amince babu nadama kuma babu kaico a cikin bin iyaye kowanne iri. A can dakinsa Prince Abdulrasheed shi ko baccin ma bai samu ba, yadda ya ga rana haka yaga dare. Bai samu mafita ta yadda zai mayar da Aisha Lagos ba, in yaso shi ya takura kansa ya dinga zuwa akai akai. Babu mai yarda da wannan shawarar tasa tsakanin Nenne da Dade don sun san bazai jure zuwan ba, su basa rabuwa da juna sai dole don haka suke so shima ya mayar da Siddiqah abokiyar rayuwarsa. Don haka ya qudurce raino zaiyi musu in sun gaji sun san nayi da ita don shi kalubalantar lafiyarsa ma yake yanzu akan mace. Da talatainin dare yace bari kawai ya gayawa Allah, yafi shi sanin yadda zaiyi da Siddiqah a cikin gidansa da rayuwarsa. Ya dauro alwallah yayi cikakkiyar nafila raka’a biyu ya roki Allah ya sassauta zuciyarsa akan tsanar da yayiwa mata, idan yarinyar nan alkhairi ce a gareshi, rayuwarsa da addininsa, ya roki Ubangiji ya bashi juriyar zama da ita, don maganar mayar da ita bata ma taso ba, ba idea bace karbabbiya wa iyayensa illa wadda zata tarwatsa zaman lafiyarsa da su. Don haka koda wasa ba zai yi ganaganci ko kuskuren mayar da ita Lagos nan kusa ba. Sai da yayi sallahr asubah da mintuna kusan talatin kafin ya samu barci, bai kuma farka ba sai wajejen karfe goma na safe. A sannan ne ya tuna da mace cikin gidansa, kuma bai bata breakfast ba. Don ko Pareto ya kawo bazai buga masa kofar ba sai ya tashi don kansa. Prince ko dabbobinsa da tsintsayensa baya so a bari da yunwar safe, balle Dawakansa, balle kuma mutum dan adam mai amsa sunan matarsa. “Ya salaam!” Prince ya furta a fili, a gurguje yayi wanka da brush, da riga da wando three quarter na barci a jikinsa ya fito zuwa kitchenette, yana tunanin me zai bata taci mai sauki kafin yayi order a kawo breakfast. In yaso zuwa yamma sai yasa Pareto yayo mata cefane ta dinga dafawa da kanta, in tanada ra'ayin hakan, don ya san mata bisa al'ada su suke girkin abinci da kansu, ko daga mahaifiyarsa wadda duk matsayin ta na sarauta, bata bari a yiwa iyalinta da ita kanta abinci bata saka hannu wajen girkawar ba. Kasancewar shi ba ma'abocin ajiye abinci bane. Yana saya ne a sanda yake da bukata kawai yaci ya tashi. Ko Pareto ya karbo ya kawo masa gida. Ya tuna cakes dinsa da baya rabo dashi a firinjinsa da choculate doughnut, sai ya jona ruwan zafi a butar dafa shayi ya hada duk wasu kayan shayi na kasaita akan tray, ya juye ruwan zafin a karamin tea flask ya hada cakes din da doughnut din waje daya, yana aikin yana gayawa kansa rayuwa mai juyi, yau shi Abdulrasheed (Kehinde) ne ya zama boyi-boyin mace. Siddiqa ta ko kasa hawa gadon dakin ta kwanta tun bayan idar da sallarta take zaune a inda tayi Salah din, kwarai take son yin magana da Ummanta da Nenne har da Dade da Firdausi, ta gaya musu tazo lafiya tana cikin kewarsu. Idanunta suka yi tarwai bata ko jin komawa irin barcin safennan da Prince ya samu don bata saba komawar ba, anan kan kilishi ta kishingida tana latsa wayar hannunta tana karanto azkar din safiya daga cikin (Muslim Muna Application). Sai taji alamun ana taba mata handle din kofa. Da sauri ta daga Ido ta dubi kofar, kasancewar ko kwan lantarkin dakin bata kashe ba, haka ta kwana cikin tsananin haske abinta. Prince ya murda kofar kadan, ya fara shigowa ya aje tea flask, kafin ya koma ya shigo da tray din hannunsa, ba tareda ya kalli inda take ba ya dora farantin kan centre table. Yana dagowa daga sunkuyon ajiyewa da yayi suka hada ido ta cikin hasken kwan fitilun da suka dallare dakin. Kwarjinin Prince da kamshin turarensa da ya cika dakin yasa Siddiqah bata iya ta amsa masa daga kwance ba, with respect ta tashi zaune daga kishingidarta, tana amsa sallamar da yayin. Irin dan durkuson su da Nenne ta koya mata na gaida maigida ko Uba tayi daga inda take zaune, tana ambatar kalmar gaisuwa da ake yawan amfani da ita a gidansu Nenne, har itama yau da gobe yasa ta tsinta wasu daga cikin kalmomin Yarbanci masu sauki ta rike wato tace dashi. “Ekaaro”. Don dai ita Hamma din, ko kusa bai yi mata kama da mai jin harshen Hausa ko fulatanci ba, kamannin sa basu nuna ya san kalmar “Zo” ba, ta san dai zai kasance daga native language sai kuma turancin nan nasa mai sarkakiya da yayi tayi mata jiya. Shima ya mayar mata, fuska babu walwala, sannan babu yabo ba fallasa. “Yaya gajiyar hanya? Thank you, and good morning”. Sannan yace mata “please manage this tea, (yi maleji da wannan shayin kafin a kawo karin kumallo)”. Ya juya ya fice ba tareda ya jira amsawarta ko ya dubeta ba. Har ransa tausayin Siddiqah yake ji. Aisha sai ta samu kanta da bin umarninsa, ta tashi ta shiga toilet ta kunna famfon wanka (shower), tayi wankanta fes da kalkale jiki da sabulu, kasancewar akwai sabulai na ruwa (bath gels) kala-kala a wurin wankan masu tsananin kumfa da dadin kamshi. Saida tayi wanka ta ji ta sakayau ta zauna shan tea din da ya aje mata. Ta ci cakes din sosai da dadin rai, kunnenta har motsi yake don dadin dandanonsa. Domin cake ne na musamman da Prince ke sawa bakery suyi masa mai dan yawa, sai ya aje a firji yana ci kadan kadan in baya son cin abinci mai nauyi. Zaka samu Sau tari yana cinsa da yamma haka yana korawa da ruwan gahwah mai zafi (hot coffee). In kuma da dare ne yafi shan chamomile ko lavender tea. Ta gayawa kanta bazata ke tambayar Prince ya koya mata amfani da wani abu a gidannan mai sha mata kai ba kada yaga kauyancin ta. Da kanta zata koyi amfani da komai ta hanyar amfani da basirar ta, na yadda zatayi surviving in this amazing and wonderful Ranch House. Wanda ya hada da budewa kanta kofar fahimtar amfani da komai na gidan, ko in ta samu ya hada mata wifi ta dinga tambayar google yafi mata sauki akan ta dinga yawan tambayar sa watarana yace mata 'yar kauye. Aisha saida ta tabbatar ta koshi, kafin ta zauna ta fidda kayanta daga cikin jakunkunan da ta zo dasu tana mayarwa tana jerawa a wardrove, zuwa lokacin in ka ganta kamar ba itace mai kuka face face da hawaye jiya ba, ta samu duk wata damuwa ta bar ranta. Self-confidence ya maye gurbin ta. Ta yanke hukuncin karbar kaddarar ta da hannu bibbiyu, na reality din rayuwar ta kenan, wato rayuwa da Bayeraben basaraken mijinta Hamma Abdulrasheed (Prince), wanda shi Allah ya ga damar su rayu tare. Iyayenta kuma suka ga dacewar shine mafi alkhairi a gareta akan Ishaq data qallafawa rai, shikuma ya wahaltawa soyayyarta da jiki da zuciya da aljihunsa. Bata so take tuna Ishaq ko kadan, (he's her past), Ishaq wanda basa taba haduwa su rabu batare da ya gaya mata adadin son da yake mata ba, ba tare da ya gaya mata muhimmancin da take dashi cikin rayuwarsa ba, ba tareda ya gaya mata tanadin soyayyar da yayi mata in sunyi aure ba. Kalaman Ishaq kadai da kulawarsa gareta ke sawa take dada ninkaya a sonsa kullum a wancan lokacin, har zuwa lokacin da Allah yaga damar raba su. Bata sanin lokacin da tunanin nasa yake sadadowa cikin kwanyarta ba, tana kwatanta shi da Prince. Sai taga ma kwatantawar bazata yiwu ba, domin ratar dake tsakanin comparison din auren ta da Prince da soyayyar ta da Ishaq mai yawa ce. Tunda Prince bashi yaje har inda take ya ganta yace yana son aurenta ba, ba da kwabonsa ko darinsa ya aurota ba, a'a auren gata aka yi masa da ita. Don haka kada ta tsammaci komai daga gareshi bayan cin darajar iyayensa a gunsa. Itama kuma bata saka aka ba. Babu komai a ranta game dashi banda girmansa da take gani saboda kwarjini da kamalarsa mai sawa taji shi kamar wani kanin Babanta. Duk da Siddiqah ta san bazata taba samun mai sonta a duniya kamar Ishaq ba. Prince ba ajin aurenta bane ai wutsiyar rakumi ne da tayi nesa da kasa. Wannan tunanin data soma in bata yakice shi ba yana son bata mata juriyar ta da yakanarta data riga ta kudurta na karbar kaddara, don haka da karfin tsiya ta yakice tunanin Ishaq ta jefar, ta cigaba da ninkewa da jera kayanta a wardrove din dakin ta jikin bango. Tana cikin fidda kayan ne ta ci karo da sakon Nenne da akayi packaging a leda da kyau, wani nau’in abincinsu ne wai shi WARA da Nenne ta ce mata na Hamma dinne, sai ta fitar ta ajiye gefe da kayan girkin da Nenne ta hadota dashida kwalaben turaren wuta masu daraja sosai. Aisha ta fiddo wata gogaggiyar atamfarta super Holland cikin dinkunan da Nenne tayi mata riga da zani da kallabinsu ta saka, ta yafa mayafin da ya shiga da atamfar wato orange
Chapter 9 · 0% Book details