← Book details Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 27

Sashe 19

Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Ranar da Uncle zai dawo Argentina bai gaya musu ba, kuma ranar Kiki ta tuna ba su je ‘Hiking’ ba. Don haka ta kwashe su a motar Prince suka tafi Hiking (long walks na hawa duwatsu).
Ranar daga Kiki har Aisha ‘sport wears’ suka saka na mata, cikin wasu kayan Kiki ne, shaf Kiki ta manta da gargadin Uncle na dawowa da wuri, kuma dai bata da masaniyar yau Uncle zai shigo Argentina ta aza sai jibi.
Aisha da Kiki suka sha ‘sport wear’ abinsu riga da wando sakakku, suka zama tamkar tagwaye don kayan iri daya ne sai kala da ta bambanta, gasu tsaho daya, saidai kasancewar Kiki baka ce mai jiki, Aisha fara siririya maia mugun shape. Kodayake yanzu Aisha ba ta a layin siraran mata, tunda bazamu kirata mai kiba ba, haka ba za mu kira ta siririya ba, saboda samun diet na kabilar Yoruba mai kyau.
Suna can suna ‘hiking’ Uncle AK ya dawo gidan tun azahar. Bai taddasu ba. Har zuwa la’asar shiru ba su dawo ba, kuma bai ga sun shirya masa wani abu da zai iya ci ba. gashi sun koya masa kyankyamin takeaway. Ya kuma ki kiran Kiki a waya don ya ga iya gudun ruwansu.
Ashe dama dare suke kaiwa haka a gantalin nasu?
Aisha dama bai taba gwada kiranta ba, tun tafiyarsa, sai dai ya ce da Kiki ta gaishe ta.
Chapter 19 · 0% Book details