Sashe 2
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Aisha-Siddiqah-Petel 'yar Ummanta, wadda tayi mul-mul da ita don kyau da koshi, na abincin yarbawa mai gina jiki, wanda ya hade da samun gyaran jiki na subulai da mayuka masu kyau da gyara fata, tana lafe jikin Ummanta sai zuba sassanyar kamshi take irin na matan manya, ko minti daya taki sakin Umma ta tashi, duk kunya ta ishi Umman, in tayi korafi sai Nenne tace.
"Don Allah barta kusa dake taji duminki Zainaba, ai Aisha tayi kokarin da ban zata ba, wata nawa rabonta dake? Kin yi tsammanin zata iya wannan kokarin data yi? Petel ce fa! Kuma Siddiqahr nan ‘yar Ummanta!
Yanzu kuma gashi kasar bakidaya zata bar miki, ai ta cancanci a barta taji dumin data yi kewar ji".
Hajiya Zainab abin ya bata dariya sosai saida suka dara a tare. Petel ta sake sunne kai jikin Ummanta.
Bayan wucewar su Nenne fadar Gombe, Malam Yunus ya dawo daga aiki ya tadda babbar bakuwar tasu AISHATU INDO SIDDIQAH, shima Abban na Aisha ya hau tasa murnar, yana cewa,
"halan cusa ake miki da tebar yarbawa da Amala da Iyan, wannan kumari da kikayi a ina kika samo shi Indona? Keda kike kamar a bushe ki".
Dariya suka sa itada Umma, ya mikama Aisha kunshin balangun da yayo mata guzurinsa, mai zafi da ruwa-ruwansa, yaji yajin balangu irin yajinnan mai citta, da yankakkiyar albasa da kabeji abin sai wanda ya gani ko ya dandana.
Da doki da kewa Aisha ta karbi balangun Ayuba mai nama ta soma ci tana fadin, "kowa ya bar gida Umma gida ya barshi.
Nayi kewar balangun Ayuba sosai, nayi kewar Arewa gabadaya".
Yau dai Aisha da iyayenta kwanan farin ciki sukayi, sun sha labarin Lagos kamar ba gobe, itama ta sha nasu labarin. Na surutun da aka yi tayi akan aurenta. Musamman da Ishaq ya dawo daga bautar kasa ya tarar an yi mata aure. Abba yace Ishaq kuka yayi tayi a gaban su kamar karamin yaro kuma ya gaya masa bashi da laifi da yadda suka yi da mahaifinsa duk ya gaya masa. Yace tun daga lokacin Ishaq ya bar Gombe don yayi bakin ciki da abinda Babansa yayi masa, ya koma zama hannun Kawunsa a Kano. Shikuma ya saka shi a harkar kasuwancin da yake yi a Kantin Kwari, na sayarda atamfofi. Yace zuwa na karshe da Ishaq yayi Gombe kayan abinci ya kawo musu turum! Yace yana jin dadin zaman Kano kuma yana neman aiki acan sannan kasuwancin da yake taya kanin Babansa yana garawa sosai.
Aisha taji wani irin yanayi na tausayin Ishaq na ratsata, amma bazata ce komai ba kada Abba ya daina bata labarinsa.
Tun a daren Umman Siddiqah ta dama tukudi mai kyau ta soma baiwa Aisha da sabaya don nononta ya kara cikowa.
Auren ne yazo mata ba shiri. Amma tuntuni tanada niyyar bata ‘sabaya’ in za'a yi mata aure don nononta data bige don ya tsahirta ya cicciko. Kwanciyar hankalinta da Aisha bata tare ba har lokacin ashe, tun lokacin karatu take yi. Koda Nenne tace zata yiwa Aisha gyara irin nasu, ita tafison ta bata tukudi da sabaya shine nasu na gado.
Umma ta gaya mata da kyakkyawan lafazi cewa da sun koma Lagos zata tare gun mijinta, sukayi mata nasiha mai shiga jiki kuma mai ma'ana. Suka bata kwarin gwiwa mai yawa suka karfeta. A karshe suka nemi yarda da amincewarta kan hakan.
Cewa ta yarda zata tare? Ko tukunna bata amince ba su gayawa Haj. Sappa a kara mata lokaci kan wanda aka bata?
Aisha taji dadi a ranta iyayenta basu yi mata dole ta tare ba, basu tursasata ba kamar da, yanzu lallabata suke, don haka ita kuma tayi kudurin zata kasance mai biyayya ga dukkan umarninsu.
Ta yarda zata je duk inda aka umarceta don tayi zaman aure, ko bangon duniya ne zata je ta zauna da wanda bata sani ba, bata san halinsa ba. sannan take da tabbacin Bayerabe ne kabilar da bata so din.
Duk da cewa tasan in ta tafi yes, tabbas zata yi kewar Ummanta da Abba, zata yi kewar Nenne kuma. Kai har Dade dinsu Firdausi ta san zata yi kewarsa, mutum mai kirki, mai sake mata da janta a jiki kamar surukuwarsa ba, shi dasu Fatima da Firdausi ba wanda bazatayi kewa ba. Duk da ba shiri suka cika itada Fatima ba, amma sun zauna tare tsayin lokacinnan da dadi ba dadi sun zauna tare a gida daya, ta san zatayi kuka na barin gida da sabon data yi da gidan Nenne da daukacin mutanen cikinsa su Femi chief cook, Seun driver da sauran ma'aikatan gidan data saba dasu duka.
Amma hakan bazai hana reality na cewa su duka ba zamansu take ba, zaman aure na wanda zataje wajensa.
Kwanan su uku suka juyo Lagos, tareda tsohuwar Nenne wato Nani Ummana.
**** **** ****