Sashe 3
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nani Oummana ta iso gidan surukinta Engnr. Idris Akanni lafiya, saboda soyayyar Kaka da matar jika ko kuwa soyayyarta da Prince Nani yi take kamar ta hadiye Aisha-Siddiqah, tsohuwar mai ran karfe komai takeso bata saka kowa a gidan tun isowarsu saidai kaji tace. “Indo jikata miko min kaza, ko yimin kaza”. Da daddare kuma da Nenne tasa aka gyara mata dakin ita Nenne inda ta saba sauka in tazo gidan, aka zo daukar kayanta za’a shigar dasu dakin Nenne. Ummana tace “ai kawai ki rufe dakin ki, ki tafi turakar mijinki, ki barni nida Indo-Siddiqah zan kwana”. Siddiqah taji dadin son nan da Oummana ke gwada mata. Don haka gladly ta barwa Nani Ummana gadonta tana murnar yau taga na gida bayan Nenne (bafullata) ita kuma ta shimfida Dunlop a kasa ta kwanta. Har dare ya raba suna hirar gida Gombe, Aisha ta samu kanta sosai da sakewa da tsohuwa Oummana, tana bata tarihin masarautar Gombe. Aisha kuma tace tun suna yara suke zuwa kallon hawan sallahr idi gidan sarki. Nani Oummana an sosa mata inda ke mata kaikayi don lokacin da Aisha ke fadi lokacin mulkin maigidanta ne uban kasar Gombe Sarki Ahmadu Jalloh Umar, nan ta hau baiwa Aisha labarinsa da irin girman abokantakar dake tsakaninsa da Sarkin Ilorin, wato Sarki Abdulrasheed Abdullateef Akanni, har da bata labarin yadda taki yarda da auren Sappa da Waziri Idrisu a baya, saboda a ganinta Yarbawane, tace “amma Uban Kasa Allah ya jaddada rahma agareshi bai saurareni ba”. Oummana tace, “sai gashi yau kaf! Cikin zuri’ar sarkin Gombe da ‘yan uwan Sappa da suke uba daya babu wanda yayi dacen aure da soyayyar miji irin wanda Sappa tayi. Tace “Bayeraben mutum akwai rikon aure akwai iya soyayyah”. Daga nan ta koma bata labarin gwagwarmayar data sha da kishiyoyi da kwarkwarori. Daga nan ta gangaro ga baiwa Siddiqah labarin yarintar Prince Abdulrasheed a matsayinsa na jikan farko a lIorin Emirate, da son hawa Dokinsa. Anan ma Siddiqah ta kara gane cewa Hamma Abdulrasheed, favourite jika ne again a gurin Kakarsa ta wajen Uwa da Kakansa na wajen Uba. Washegari ta raka Nani da Nenne wajen finger print na visar tafiya aikin Hajjinsu, akasa itama tayi a wani wurin daban bayan an gama nasu. Siddiqah ta soma tunanin da tarewar da akace zatayi gidan mijin dama aikin hajjin suka tafi da ita don ta kula da Nani Oummana, kasancewar komai ita take mata a gidan tsohuwar bata da kwari. Har ta fara hango kanta ta sako hakorin Makkah ta dawo Gombe da tsarabar Umma rankatakaf! Makwabta nata shigowa barka da zuwa bayan ta dawo. Sunanta ya tashi daga Siddiqah zuwa Hajiya Aishatu-Siddiqah Indo. Ashe dai duk hasashe take yi, kuma bata hasaso daidai ba. Domin an yi haka da kwanaki kadan rannan da daddare Nenne ta shigo mata da manyan trollies guda biyu babba da karama da zata tafi dasu, tace ta hada kayanta da duk abinda ta san zata bukata a gidanta a cikin jakunkunan data kawo mata dinnan. Da mutuwar jiki mai yawa Aisha ta karba ta mike ta hau hada komai nata a trollies din, hatta brush da soson wankanta bata bari ba. Amma dai kwarai taso aje da ita Hajjinnan, ta dade tana fatan ziyartar Shabbakin Ma’aiki SAW. Da kuma Masjid Haraam da Masjid Nabawy, wato dakin Allah mai alfarma da hubbaren ma’aiki SAW. Tazo shigowa daki taji Nenne da Nani suna magana kus-kus, bata so ta katse su, sai ta dan dakata, da nufin su gama sannan ta shiga ba da nufin yi musu labe ba, duk da kuwa har sunanta taji ana ambata ga alama very sensitive magana suke yi akanta. “To haka zaku aikata baku shiryata da komai ba? Ina nufin bakiyi mata shiri irin naku na yarbawa ba, ga shiri namu na Fulani da ya kamata duk a hada ayi mata a samu a Abdulrasheed ya karbeta da kima? Wannan da ya tuzurance ba aure sai hawa Doki ai matarsa sai an shiryata da kyau”. Nenne tace cikin jin kunya “Nani! Nifa babu ruwana cikin sha’anin nan ‘yar kallo ce, rigimar Dade dinsu ne tafiyar Aisha fa, amma ni tuni na zare hannuna daga lamarin nan wanda nasan bazai taba haifar da Da mai ido ba, in dai aka yiwa Abdulrasheed kutse da mace cikin rayuwar Polonsa. In don ta ni, Siddiqah ta gama zaman Kehinde a gidannan. Ina mata addu’ar samun wanda ya fi shi komai da komai ne, ba za’a lalata kuruciyarta tayi zaman gadin gidan gona sanadina ba”. “Akul!” inji Nani Oummana, kada in kara jin wadannan kalaman sun fito daga bakinki Sappah! Masu nuna kin yi fushi dashi yaje ya cigaba da abinda ya ga dama. Kin sani zuciyarki kadai Allah zai kalla ya hukunta shi da fushin cikinta. Ki sani Abdulrasheed yana cikin jarabawar ubangiji akan sha’anin aure, ba yin kansa bane ba jifa bane, sannan ba shafar jinnu bane, amma da yardar Ubangiji ya kusa cinye jarrabawarsa. Dade dinsu ya fi ki gaskiya. Ki tura masa matarsa daga nan ki fita sha’aninsu, in yaso ko gunduwa-gunduwa zai yi da ita ya kawo muku ruwansa, idan ta shekara babu ciki shine zamu tabbatar aljana ta aureshi da gaske, ko mu yarda babu lafiyar mazantaka a tare dashi. Amma nima bana bayan ki bata komai na mata yanzu, kada a bar 'yar mutane da ciwon mara. Don ba lallai ya kulata tashi guda ba wannan uban kasaitar da bunkasar. Barta taje haka yanzun, can gaba in kin fahimci komai yayi daidai a tsakaninsu sai kiyi mata babban shiri na yarbawa ". Aisha duk ta rude, ta rikice don bata dai gane takamaimai shirin me Nani da Nenne suke ta magana akai ba, sannan ta kasa gane inda rabin wadannan zantukan nasu ya dosa, data gaji da tsayuwa a wurin kuma taga basu da niyyar saka aya a maganganunsu, sai kawai tasa kai a dakin gabagadinta, bakinta dauke da sallama. Sai duk suka yi shiru suna amsa mata. Ta karasa gaban Nenne jiki a sanyaye tace “Femi tace an gama WARA din da kikasa aka yi miki". Da far’a Nenne tace "Kai madallah da Femi sarkin masu Himma. Warar ai taku ce, kice ta yi packaging dinta da kyau, ki karba ki sata cikin kayanki,". A zuciyar Siddiqa tace “Allah ya suttura taci Wara, wannan sai asalin yarbawan Ilorin. Har gobe ita sai fura da nono. Kowa ya bar gida gida ya bar shi”. Tun kafin kwana biyu tafiyarta Nenne ta gaya mata komai na shirin tafiyarta ya kammala, ta gaya mata jibi zata tashi, kuma tace tayi hakuri cikinsu babu mai rakata. Haka Dade da Emir suka tsara tafiyar tata. Duk kokarin Siddiqa na boye rashin son tafiyar nan yau ta kasa boye karayarta cikin idanunta, jin cewa ita kadai ma zata tashi daga Lagos zuwa wata kasa da bata ko sani ba. Nenne ta bar wurin da azama don bata son Siddiqah taga tata karayar. Ranar tashinta zuwa Argentina Nenne tasa Siddiqa ta fiddo trollies dinta waje, Dade na jiranta a mota zasu tafi airport, shi da kansa zai sata a jirgi. Masu aiki suka daukar mata jakunkunan suka sa a bayan mota Lamborghini wadda asalinta motar Abdulrasheed ce da yake hawa idan yazo gida Lagos. Nenne tazo har daki tace da Siddiqa idan ta gama shiryawa ta fita parking lot Dade na mota yana jiranta. Nenne da wayau taki yarda su hada ido yau, kada taga karayar dake cikin kwayan idanunta. Ta miko mata wayar hannunta dake jikin caji tace ta kula da wayarta sosai. Sannan Nenne ta matso kusa da ita kamar bata so wani yaji me zata ce, ta fadi wani abu, da ya kara daga hankalin Siddiqah. "Ki yi hakuri da duk yanayin da Zaki riski rayuwa dashi a inda zaki je. Bai taba zama da matar aure ba a gabadaya rayuwarsa tun ta samartaka har girma, he will find it difficult to cope with you at first. Idan na bata miki a hada wannan auren a bisa sani ko rashin sanina ki yafe min Siddiqah. Na yi ne da kyakkyawar niyya saboda kaunata da mahaifiyarki. Aure ya gaji haka, ba inda baya kai diya mace kada ki damu da duk inda zaya kaiki. Ki dinga yi masa uzuri kullum, uzuri na cewa duk shekarunsa shi yaro ne a hannunki tunda bai taba dandana rayuwar aure ba, ba kuma sabida mu zaki dinga yimasa uzuri ba a’ah, sai don kasancewar sa shima Dan Adam ne, ajizi, kuma miji a gareki mai tarin nakasu kamar kowanne Dan adam. Idan ya bakanta miki bisa sani ko rashin saninsa, ban horeki da gayamin ko mahaifiyarki ba, a'a ki gaya masa face-face tsakaninki dashi yanzu babu hijabi, ku fuskanci matsalar komai tsaurinta, mijinki ya zama best friend dinki, confidant dinki, ya zama ba tsoro ba shakka a tsakaninku sai yarda da cewa kowa zai iya batawa daya a bisa sani ko rashin sani. Ki kuma dinga gayawa Allah a kowacce sallahr farillarki ya huwwace miki soyayyarsa. Ki ce “Allah ga AbdulRasheed dan Idris Abdullateef Akanni, ka sanya masa soyayyata mai girama". Wata irin kunya ta kama Siddiqah. Nenne bata damu ba ta cigaba da cewa. "Sannan ki hada da yin hakuri. Sabida shi wannan hakurin da nake ta jaddadawa a auren na gani inaso ma shi ne ke tafiyar da rabin auren, balle aure irin naku da bashi ya gani yace yana so ba, mu muka gano masa dacewar hakan. Don haka hakurin da zakiyi da Abdulrasheed mai yawa ne Siddiqah, shine kuma zai zame miki ginshikin zaman auren bakidayansa. A sanin da nayi masa ko baya sonki bazai taba cutar dake ba, sannan bazai wulakantaki ba saboda mu muka kawo ki cikin rayuwarsa, amma zai iya yi miki silent protest! Saboda mummunar fahimtar da yayiwa mata gabadayansu. Na roke ki Siddiqah, kiyi kokarin da zaki share wannan mummunar fahimtar da yayiwa mata daga zuciyarsa, in kowa nasa ya rainaki saboda shekarunki da wayewarki da karancin ilminki ni mahaifiyarsa ban raina ki ba, na yarda kema mace ce kamar kowacce mace mai fasaha da hikima da iya tata kissar. Abdulrasheed ya riga yayiwa mata kudin goro, inaso ki nuna masa har yanzu akwai nagari, akwai kuma masu soyayya ta saboda Allah. Wannan tarbiyyar da Haj. Zainab ta jima tana