Sashe 25
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gaskiya bata cika expectations din iyayenshi a kanta ba, da yardar da suka bata dari bisa dari na zata iya, zata kawo kyakkyawan canji a cikin bahaguwar rayuwarsa. Cikin watannin data yi tare da Hamma Abdulrasheed wane abun ku zo ku gani ta kulla a zaman nasu, wanda in aka tambayeta progress na zaman su zata iya adarwa da babbar murya? Idan da ta bi shawarwarin da Kiki ta bata, duk da ake cewa Kiki bata da nutsuwa, in aka dauka a tsanake aka dubasu za’a ga cewa shawarwari ne masu kyau da za su taimaka a rayuwar aurenta. Tunda auren nan ya riga ya zama rubutacce daga Allah! Wanda babu yadda za ta yi ta guje wa kaddarar kasancewarta mata ga Prince Abdulrasheed jikan marigayin sarkin na yarbawa. **** **** **** Daga wannan lokacin Siddiqah ta yi kyakkyawan kudiri a zuciyarta na in Prince ya dawo daga ranar zata canza irin zaman da suke yi, zuwa zama mai armashi da ma’ana koda bazai bata hadin kai ba. ta fannin ta zata yi kokarin sauke nauyin duk da iyayensa suka dora mata, sama da komai Ubangiji ma ya dora mata. Zata koma kyautata aurenta dashi iyakar kyautatawa. Kiki ta kira a lokacin da take tsaka da wannan juyayin, Kiki na cikin alhinin babban rashin da suka yi don itama Emir yana sonta albarkacin son da Abdulrasheed ke mata. Yau sai ta ji hatta Kiki din abin kunya ne babba ta tambaye ta lambar Hamma. Amma har gara ta murje ido ta tambayi Kiki, a kan dai ta tambayi Nenne. “Kiki am, nace ba, ko zaki ba ni lambar Hamma don Allah, ina cikin damuwa, tunda ya tafi ya kirani sau daya bai kara kira na ba, ni ma kuma nayi wani kuskure da ban kira shi ba, na dauka nayi saving no. din tun a lokacin, ai yanzu na duba ban ganta ba, a tsammanina zai kira again, sai inyi saving to amma yanayin da yake ciki nasan shi ya hana bai kira din ba”. Kiki was shocked da wannan ganganci zata ce ko childishness na Aisha. Ta ce, “Aisha me ki ke cewa? Sati biyu ba ki ji motsin mijinki ba, kuma ba ki kira shi ba ke? Sannan ba ki da digits dinshi a wayarki? To kenan ashe duk shawarwarin da na bata lokacina na baki ma babu wanda ki ka dauka kika gudanar kenan? Aisha me ke damunki har haka na tabbata ba kiyayya bace. To menene? Kin san girman hakkin Uncle AK da ke wuyanki kuwa? Haba Aisha, kankantar shekaru da rashin soyayya ba hauka ba ne, domin bayan dukkansu akwai abin da ya kamata mace ta yi la’akari da shi a zaman aure, shine sanin yakamata da sanin girman hakkin mijin duk da Allah ya rubuta shi ne mijinta”. Jikin Aisha duk ya idasa macewa, dama kuma ko kafin ta kira Kiki Rukayyat, duk ta yi wadannan hasashen itama, Kiki ta ce, “Lallai ne yanzu Uncle ke bukatar kulawarki da soyayyarki Aisha. Ya yi rashin masoyin da bai da kamarsa”. Nan Kiki ta shiga bai wa Aisha labarin irin kaunar da ke tsakanin Sarki da Hamma. Ta gaya mata hatta dokinsa Saheeb data gani yana matukar so, da daya matashin ‘Criollo Horse’ din, duk kyauta ce ta musamman daga Emir zuwa gare shi. Abubuwa da yawa da bata sani ba a kan rayuwar Prince, a ranar yau duk ta ji su a bakin Kiki. Aisha daga karshe kashe wayar tayi tun kafin suyi sallama da Kiki, saboda zuciyarta tayi rauni, tausayin Hamma Abdulrasheed Prince, hade da wani sabon ni’imtaccen feeling da ke sauka a kasan ranta a kansa. Kiki ta turo mata lambobin ta hanyar text message, ta kara da turo mata sakon text. “Text him. And call him tonight’. A take ta rubuta sakon text ta tura wa Prince. Sakon ya kunshi ta’aziyyah zallah a kan rashin da ya yi, da fatan Allah ya bashi hakuri da danganar musulunci, ya kuma jikan Maimartaba Sarki. A kasan sakonta ta rubuta sunanta; “Aisha-Siddiqah Yunus”. Prince bai bude wayarsa ba sai da ya zo kwanciya barci, bayan fitar Taiwo kenan daga masaukinsa, yau ne aka yi sadakar bakwai, kuma har ya soma shirin komawa Argentina. Yanzu Taiwo ta bar masaukinsa tana masa wasu maganganu da suka ba shi haushi da mamaki, ko dai Taiwo ta manta irin rashin da yayi ne da ta zo tana masa wannan shirmen? “Kehinde, yanzu saboda Allah don zubar da aji da barar da kima, yarinyar nan mai kama da kazar mayu ka dau hoto da ita ka dora a status? Ka san iya mutanen da zasu bude? Me kake nufi da kalaman daka rubuta a kanta? Abu daya ma yanzu ni nake son sani, tunda aka tura maka ita ‘have you ever touched her?” Dan bude idanu ya yi a hankali wadanda duk sun kankance, yana kallon ‘yar uwar tagwaitakarsa Taiwo Akanni, his very own twin sister Taiwo. Sai ya rasa amsar da zai bata, domin tambayarta ta fi kama da crossing limit da shiga personal marital affair dinsa. Taiwo ta ce, “Don in baka tabata ba in ba ka shawarar amfani da kwararon roba, tunda naga alama ta fara samo kanka, na san it will not be easy for you to be using condoms, yadda ka dauki lokacin nan ba aure, ace ka daure ka iya hakan. Amma Kahinde ka sani ba ta isa mu hada zuri’a da ita ba, make her your sex slave kawai, Allah ya gani ba zan taba son yaran da za ta haifa ba”. Abdulrasheed sai ya bude idanunsa gaba daya yana kallon ‘yar uwar tasa da mamaki da tsoro. Da kyar ya iya motsa bakinsa da yayi masa nauyi, don magana ma wahala ta ke masa tun bayan rashin Emir, yace, “Maman Kiki, bana son yadda ki ke min maganarta. Alaqata da ke daban, wadda ke tsakanina da ita daban”. Ya hadiyi wani abu da kyar da ya tsaya masa a makoshi, a dalilin dacin da ke zuciyarsa na rashin Kakansa, ya dubi Taiwo sosai ya kauda kunya yadda itama ta iya kauda kunya ta yi masa wannan zancen. Yace. “Shin Maman Kiki in tambayeki please. Zaman zina nake yi da ita da zan yi amfani da kwararon roba a kanta? Ko Concubine (kwarkwara) aka kawo min itaba matar aure uwargida ba I will never do this. Kamar na wofintar da umarnin Nenne da Dade ne. Kin ce bazaki taba son ‘ya’yan dana haifa da ita ba don kawai diyar talakawa ce. Ni kuwa kin ga ko da ‘Kare’ ki ka haifi su Kiki bama mutum dan Adam mai kima ba, banida kamar su, ba zan taba kin son ‘ya’yan da na tabbatar daga jikinki suka fito ba”. Da wannan Prince ya maida bakinshi ya dinke. Ya ki kara kallonta. Ya maida hankali ga kunna wayarsa dake kashe tun safe. Taiwo sai ta ji kamar bakar magana ce Kehinde yau ya gaya mata a kan mace. Macenma wannan mara aji irin Siddiqah, wadda ba diyar kowa ba. Wato Kehinde ya fara sanin dadin mace har ya dube ta yau ya gaya mata baqar magana irin haka akan Siddiqah? A take Taiwo taji ta kara tsanar matar dan uwanta. Kwafa ta yi ta mike tana cewa, “Kehinde maida wukar I came in peace in dai akan ‘yar Malam Shehu ne. Abinda ya kawo ni gareka ma ba zancenta bane rabon in samu rabon bakar magana ne. Inata so in gaya maka tuntuni cewa I met Hasina coincidently. She explained to me all what happened between she and Tukumbo. She made a mistake and she realized it. She is haunted. How much she hurt you had been haunting her. Tana ta neman yadda za ta ba ka hakuri but to no avail. Daga baya ta yi aure har sau biyu a UK ta fito, ta ce min ta tabbata alhakinka ne ya hana ta zaman aure. Ina rokonka ka yafe mata, ta ci albarkacina”. Prince ya ce a dan hassale, “Maman Kiki ba ni da say a kan wannan batun da ki ka zo da shi, sai dai in ce, please! Please!! Don’t mention that bitch again to me, idan kin yafe mata is okay ni ma na yafe, domin kada ki manta abin da ya yi Kehinde shi ya yi Taiwo”. Da sauri Taiwo ta ce, “A da ba… kafin ka samu abun hutawa, amma a yanzu kana neman canzawa ne completely daga Kehinde dina”. Kehinde din sai ya yi shiru har Taiwo ta yi tsaki ta wuce yana mamaki. Me ya shiga kan Taiwo dinsa ne? Tunda aka yi masa auren nan ta ke acting kamar ta samu tabin hankali a kan matarsa. Ya yi nafila raka’a biyu ya sha zazzafan chamomile tea, ya kunna wayarsa kenan sai ga sakon Siddiqah ya shigo. Ya karanta ya maimaita, sai ya samu kansa da tura mata reply da kalmar, ‘thank you’, a fili kuma ita ma haushi ta bashi. Ko da ya san ba auren so aka yi musu ba amma fisabilillah yana iya kokarinsa wajen kyautata mata a gidansa. Bai tsangwame ta ba, bai kuma rage ta da komai ba. Amma ace ya yi tafiya irin haka har tsahon sati biyu Siddiqah ko sau daya ba ta kira shi ba, sai da ta ji ya rasa Emir? Saboda shi Prince a mulki irin nasa matarsa ce ya kamata ta dinga kiransa don yana son respect mai yawa daga matarsa. Kusan wannan dabi’a ce ta mazan Yoruba, suna da tsananin son respect, musamman daga matan su. Musamman a wannan lokacin da yake ganin jinyar Kakansa ya zo, ita ya kamata ta dinga kiransa don jin ya jikin Maimartaba. Amma ba ta yi hakan ba sai yanzu? Bai san cewa ita Siddiqah ko digits dinsa bata yi saving a wayarta ba, saboda bata dauki auren nasu da wani alkibla a baya ba. Bayan zama na biyayya. Amsar da Hamma ya bata nan take, duk da a gajarce ne, showing nothing, shi ya ba ta kwarin gwiwar kiransa. Kirjinta da zuciyarta baki daya suna harbawa a cikin kirjinta, don yau ji ta ke Hamma na samun wani special reception a gunta, data dangata shi da tausayinsa. Yana kallon lambobin Siddiqah suna shigowa da mamakin kiran kamar ta san