Sashe 24
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gefe tana kallon yadda al’amuransu ke gudana tsakanin Saheeb da mai kula da shi, tamkar saheeb wani dabba ne mai tarin hikima da baiwa, duk mai kula da shi ya sanshi farin sani. Kadan-kadan Saheeb ya fara gane fuskar Siddiqah, watarana cikin dari-dari ta kai hannu ta fara shafa jikinsa da kyakkyawan gashin wuyansa, har Pareto ya tsorata ya zo da sauri zai hanata, sanin halin Saheeb da yayi, na ba ya barin kowa ya zo inda yake bai yi harbi ba. Amma abin mamaki sai ya ga Saheeb ya kwantar mata da kai kasa tana shafa shi yana dada kwantar da kai. A haka a haka har karambani ya sa rannan ta ce da Pareto tana so ta hau bayan dokin. Pareto ya gaya mata cewa ba ya bari a hau bayanshi in ba mamallakinshi ba. zaiyi tutsu a ita. Aisha ta dage cewa she wants to give it a try. Dole Pareto ya kyale ta ya saka mata sirdi ta hau Saheeb, ya rike mata linzami suka shiga zagayawa cikin Ranch din. Sune har kofar fita ‘ranch’ da wajen BQ din Pareto, daga nan suka juyo suka dawo stable dinsa. Siddiqah ta sauko lafiya. Sai hakan yasa ta kara sabawa da Saheeb sosai, kullum nan ne wajen wuninta. Kusan ba ta da damuwa a yanzu, don Saheeb ya debe mata kewar kowa da komai. Siddiqah na nan tana fama da Saheeb, Prince yana Ilorin jikin Kakansa Sarki Abdulrashed Akanni ya rikice. Likitoci har uku ne ke tsaye a kansa a gidansa na masarautar Ilorin, tare da ‘ya’yansa (Ten Akannis). Ciwon cikin wuni uku daya firgita zuri’ar Sarki Abdurrasheed gabadaya. Prince kwana yake tare da Kakansa a turakarsa don ko matansa na aure basa bari dashi. Yau da dare jikin nasa da sauki sosai, don an masa allurar barci, amma cikin dare ya farka ya ga Prince a zaune a gefen kansa yana gyangyadi, lokacin kowa ya je ya kwanta. Sarki Abdurrasheed Dan Abdullateef Akanni, ya ce da jikan nasa Prince. “Kehinde! Barci kake yi a zaune?” Kamar cikin mafarki ya ji muryar Kakan na kiran sunansa, tuni ya wartsake ya matso daidai kansa. Sarkin ya kamo hannunsa ya rike cikin nasa, ya ce cikin harshen yarbanci, “Kehinde Jikan Sarkin Ilorin, jika mafi soyuwa a gareni, me yasa baka zo min tare da matarka na hada ku na sa muku albarka ba? Ina fatan zuwa yanzu komai ya daidaita tsakaninku yadda muke fata? Ka karbi zabin mahaifiyarka da hannu bibbiyu? Nan bada jimawa ba zaka ajiye min mai sunana? Wanda zai gaji gidannan tunda ba kwa son gadona kai da Ubanka?” Prince rasa amsar da zai baiwa Emir ya yi, sai cewa yayi cikin yarbanci “tana lafiya Allah ya ja zamaninka, na baro ta lafiya cikin koshin lafiya, kuma maimartaba na dade da karbar matar nan da kuka zaba min da godiya da yabawa. Tana da attributes na matan kwarai da ban san su a tare da ‘yammatan wannan zamanin ba”. Sarki Abdulrasheed ya gyada kai cikin gamsuwa da jin dadi, sai kuma yace. “A yadda nasan ka kullaci mata, da yadda giyar mulki ke hanaka sakewa, ina da yakinin har zuwa yanzu ba ka dora mata idda ba. Ko Qur’ani zan dafa akan ba ka dabbaqa sunnarka ba har yau, me yasa? Donni in za’a shekara ana cewa ba ka da lafiyar aure ba zan taba yarda ba, na san lafiyarka kalau, baka samu wadda kake so bane, kuma bazaka iya hada jiki da matar da baka so ba shine babban dalili, tunda na san yaya halittar sarakuna take a kan matan da suke so. Kada ka manta na so Kakarku Murjanatu kamar raina. A lokacin da take raye ban taba zaton zan tsufa ba, kullum sabuwar samartaka take kara min saboda soyayya, ina gaya maka kayi gaggawar dabbaqa sunnarka kafin ranar da wankin hula zai kaika dare, wato ranar da zata gane tana son ka tayi maka bore ta hana ka kanta”. Prince ya hau zufa daga goshi, ga kunya da ta kama shi. Ya kasa cewa komai. Amma da zai iya da yace da Kakansa sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba, amma ya fara jin sauyi a zuciyarsa da gangar jikinsa sosai a kan Siddiqah. Sun kwana suna hira shi da Kakansa abin gwanin sha’awa, inda ya sa shi yi masa alkawarin zai kula da aurensa, zai kuma kula da Siddiqah kwatankwacin yadda Dade yake kula da Nenne. Ya kuma tabbatarwa Kakan nashi cewa shi lafiyarsa kalau ba kamar yadda mutane ke kuskuren fahimta ba. Yana jiran ya ga yadda Allah zai yi dasu ne shi da Siddiqah. Emir kuma ya ce masa “ka yi amfani da dama a lokacin da ta ke hannunka”. Har aka kira asubahi idonsu biyu, Kawunsa Malami Ubandoma, da mai bi masa Mufti of Ilorin suna daga shigifar farko a nan suka kwana, Prince ne kadai ya kwana tare dashi da asubah yayi masa alwallah yayi sallar asubahi daga kwance, sai ya ce da Prince yasa masa bargo sanyi yake ji. Kuma ya kunna masa Suratul Mulk a radiyonsa. Prince yayi duk yadda Kakan ya ce cike da kauna da kulawa, sannan shi kuma ya tada tashi sallar. A nan inda ya yi sallah kasancewar ya yi kwanan zaune barci mai nauyi ya yi awon gaba da shi. Har gari ya soma haske Abdurrasheed bai farka ba. Ashe sallamarshi kenan da Kakan nasa Emir Abdurrasheed Akanni. Abinda ya faru yana barci shine Kawunsa Mufti ya shigo kawo karin kumallon Sarki, a lokacin da aka kawo daga cikin gida, shi ya gane cewa ran Emir ya yi kaura zuwa ga mahaliccinsa. Sai ya tashi Prince daga barci ya yi masa nuni da abin dake faruwa. Prince ya isa ga Emir ya tallafo kansa ya tabbatar wannan ruhin da ya rayu shekaru sama da shekaru arba’in da biyu yana lelensa yana kula dashi yana kyautatawa rayuwarsa yau babu shi. He is more than shocked. Don ko kusa bai kawo wa Emir mutuwa yanzu ba, don ya saba ciwo fiye da wannan ma ya girgije ya tashi. Shi ya san ya yi rashin da ko iyayensa ne suka fadi yau suka mutu suka barshi iyakar kukan da zai yi kenan. A wayewar garin ranar labarin mutuwar sarkin Ilorin, Sarki Abdulrasheed Akanni, ta riski al’ummar kasar Najeriya, labarin yayi tambari ya riski duk wani jininsa, kafin kace meye wannan kafatanin zuri’arsa na garuruwan Najeriya da wajenta sau bubbugowa suke yi Ilorin. Akannis sun gigice sun dimauce baki daya, amma babu wanda ya kai Prince AbdulRasheed gigicewa, su Nenne ma da su Princess Fatima, duk a ranar suka taho Ilorin, Taiwo da ke nan Ilorin kuma akan idonta aka yi wa sarki suttura, duk a ranar suka taho masarautar, haka dukkan ‘ya’ya da jikoki na nesa da na kusa suka hallara. Sun dade basu shiga halin dimauta da gigita irin na wannan lokacin ba. **** **** **** Tun Siddiqah na zuba idon ganin Prince ya dawo a satinsa na biyu da tafiya har ya zamanto ta fara damuwa da rashin dawowar tasa, duk da ba wai shiri suke yi ba, ba kuma shakuwa ce ta sosai a tsakaninsu ba, amma mutum a cikin gida rahma ne. Kai ita yanzu ta fara jin tsoron zaman gidan ma, daga ita sai Dawakai da dabbobi. Ta yi da na sanin rashin yin bore na sai ta bishi kamar yadda Kiki ta ke so ta dinga yi, wato ko’ina Hamma za shi ya tafi tare da Aisha. Amma cikin hudubobin Kiki na arzikin wanne ta dauka? Kusan a inda ta bata su, tun tafiyarta a nan ta ajiye mata su saboda taurin kanta. Yanzu ga shi rashin Hamma a gidan ya dame ta, musamman da ko sau daya bai kirata ba. Sati biyu kenan da tafiyar Hamma Ilorin, ranar da aka yi rasuwar Nenne ta kirata, nan ta gaya mata rasuwar Kakan nasu Fatima. Sai kuma Kiki ma ta kirata suna gama magana da Nenne. Kiki tana cikin damuwa domin makarantarsu ba za ta bata excuse din zuwa gida ba kasancewar ba ta jima da dawowa ba. Nenne again a washegarin ranar rasuwar ta sake kiranta, ta ce, ta kira Abdulrasheed ta yi masa ta’aziyya. Domin kuwa shi aka yiwa mutuwa a kafatanin zuri’ar Akanni, ta gaya mata babu wanda ya kaishi kusanci da shakuwa da Sarkin. Kuma babu wanda Emir yake girmama sha’aninsa da kaunarsa cikin jikokinsa kamar Prince din, wadanda a kiyasce jikokin na Emir Abdulrasheed Akanni sun tasar ma (82). Nan fa ake yinta! Don Siddiqah da Prince ya kirata bayan saukarsa a Ilorin, ya gaya mata saukarsa lafiya ya kuma tambayi yadda take coping tace masa batada matsala, ashe lokacin ko lambar Prince din bata yi saving cikin wayarta ba, tsabar yadda bata daukeshi matsayin mijinta ba face Yayanta/Babanta, wannan abun kunya da me yayi kama? Taji kunya sosai yau, sannan da kunya ta tambayi Nenne wai lambar mijin da suke kwana gida daya. Har suka yi sallama da Nenne jikinta a salube yake, bayan ta sake yi mata tata ta’aziyyar, Nenne kuma ta kuma hadata da Dade shima tayi masa, da Princess Firdausi da Princess Fatima, ba ta iya ta tambaye ta lambar Hamma ba. Me Nenne za ta dauke ta? A yau sai ta ga cewa ma a gabadaya zamansu wanda ya ki samun daidaito da fahimtar juna har lokacin ba laifin Hamma Prince bane, laifin ta ne. Saboda Hamma yayi iya kokarinsa da ya karbeta a matsayinsa na wanda aka yiwa auren dole, ita da take mace ita ya kamata ta canza shi zuwa yadda iyayensa sukayi fata, suka kuma dora burin hakan a wuyanta saboda kyakkyawan zaton da suke dashi a kanta. Amma me ta tsinanawa Hamma na kyautatawa tun zuwanta? Hasalima bata dauki auren nasu a matsayin aure ba sai zaman biyayya. Bata shiga sha’aninsa yadda ya dace tayi, ba abinda Kiki bata ce mata ba wanda shi zai sa ta kusance shi su shaku da juna, ba abinda bata koya mata ba cikin dabarun abinda Bayeraben miji yake so daga matarsa, wanda zai sa ta kama zuciyar Hamma nan da nan, haka mahaifiyarsa ta dade tana bata training akan zama da shi. Amma a ciki wanne ta aikata baka da zuci? A zahirin