← Book details Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 27

Sashe 15

Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 1 min read

girkin nasu. Kiki da Aisha har suna hada baki wajen yi masa barka da zuwa. Ya amsa yana cewa Kiki su dauki ledar can ice-cream ne a ciki kada ya narke. Ya samu waje kusa da Kiki ya zauna cikin gajiya, yace a ransa dashi wani maigidana ne na hakika tausa zai so ayi masa. Dan murmushi ya subuce masa, yana dago kai ya ga Aisha na satar kallonsa, yayi bala’in kyau cikin ‘casual wears’ marassa nauyi ruwan toka dake jikinsa. Kayan sun maida shi yaro mai tashen talatin da biyar. Kiki ta karya kai tace, “your dinner is ready Uncle, Ewa Egoyin and Ofada rice, tuntuni kai muke jira kazo mu ci”. A hankali ya dubi Aisha jin ta ki magana ita, yace “Kiki kun min jagwalgwalo dai”. “Wallahi ba jagwalgwalo bane, try us, sai an gwada akan san na kwarai”. Ta fada tana serving kowannensu a faranti daban, sai ta hada nashi dana Aisha a plate daya, tace “Uncle wannan ma ai ba yi bane, kana da mata a gida kana shigo da takeaway, me ka dauke mu ne?” Dariya Kiki ta bashi sosai, sai kace irin manyan matan nan, a hankali Hamma ya ce mata.
Chapter 15 · 0% Book details