Sashe 4
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baki yanzu ne zata yi miki rana, ki fiddo ta sarari kiyi amfani da ita a gidan aure, ki fahimtar dashi cewa ba duka mata ne a cikin rigar da yake kallon su ba, komai lalacewar da zamani yayi, har gobe akwai mata masu kyawun hali. Na san bazaki samu cimma wannan nasarar a lokaci guda a tare dashi ba, sai kin yi HAKURI mai dimbin yawa Siddiqah, na dameki da kalmar hakuri ko? Kada kiyi mamaki, shi hakuri baya yawa, ribarsa ce kawai mai dimbin yawa. Ki kauda kabilancin nan naki da kika bari ya samu muhallin zama a zuciyarki, in har kinason a zauna lafiya, ina kara gaya miki Abdulrasheed Bayerabe ne, ki maida al’adarsa taki, shima sai ya maida al’adarki tasa. Aure babu cikin kabilar da baya kai mace a addinin musulunci, ni dinnan na isheki misali, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi Aishatu-Siddiqah, ya albarkaci aurenki da zuri’a salihah, dayyibah”. Nani Oummana tace “kisa himma kinji ko Indo wajen kula da mijinki, Aishoshi himma garesu ta wannan fannin. A fannin iya kula da shimfidar miji ma basu dana biyu, sannan a komai sai kinga sun zama zakaran gwajin dafi a wurinsa saboda albarkar sunan NANA AISHA, sannan ababen buga misali ga mazajensu a duk inda suka shiga. Ina fatan Allah yasa shekara na zagayowa in ganki goye da magajin sarkin Ilorin, ko mai sunan marigayi Uban kasar Gombe, kinji ko Indo Aisha?” Siddiqah sai ta soma hawaye. Ko dai su Nenne sun gaji da zamanta tare dasu ne saboda tana musu halin kabilanci? Shine zasu kaita inda suka san bazata taba iya zama ba, don kabilancinta bazai barta ta iya zama da Bayerabe ba. Zuciyarta na tunasar da ita kada ta taba yaudarar kanta, da tunanin ko mijin nata ne ya bukaci zuwanta, Hamma Abdulrasheed, (Prince), mai sunayennan guda uku, bashi ya bukaci ta je inda yake ba. Nenne bata iya cigaba da tsayuwa a dakin ba ta yi maza ta fice, ganin tashin hankalin da ya bayyana baro-baro akan kyakkayawar fuskar Aisha-Siddiqah karara. Princess Firdausi ta yi kamar bata fuskanci halin da Siddiqah ta fada ba, saboda tausayin da ya kamata, ta kama hannunta zuwa (parking lot) na gidan inda Dade da Seun ke zaune cikin mota suna jiran fitowarta. Firdausi ta bude mata kofar bayan motar, jiki a salube Siddiqah ta shiga. Firdausi ta rufe kofar motar tana cema Dade dinsu. “A dawo lafiya Dade”, cikin harshen Yoruba. Dade ya daga mata hannu kawai. Princess Firdausi na daga mata hannu itama haka har suka fita gate din gidan. Seun, ya zaburi mota ya bar shiyyar Banana Island da Siddiqah Yunus da mahaifin mijinta kwance a bayan mota. **** **** **** Suna tafe Siddiqah na tuno tun farkon zuwanta Lagos, daga zuwa ganin likitan Asthma ace komai ya jirkice mata haka, sai kaddarar aure wannan na tarad da waccan. Aurenma na masarautar Yarbawa, yarbawa da bata so tun bata san meye ma’anar kalmar Yoruba ba. Rayuwarta ta juye rana daya (upside-down) ta kutso cikin ta gaggan kabilar yarbawa din. Zamanta a birnin Lagos ta san daga yau ya kare kuma. Yanzu ne zata fara rayuwar reality da bayeraben miji, wanda shine hakikanin abinda ya kawota cikinsu, ya rabota da kowa nata. Ko wace sabuwar kaddarar ke jiranta? Ko wadanne sababbin abubuwan kuma ke kiranta yanzun Allah masani. Bayan ta riga ta fara sabawa da duniyar Yarbawan data fado ciki rana daya, wadda zuwa yanzu ta dade da bin jikinta. Ta na sunsuno cewa wata sabuwar rayuwar ce ta dumfarota, wato rayuwar aure gabagadi. A baya tana amsa sunan auren ne ba tareda taje cikinsa ba, yanzu kuwa kacokam an daukota ne an cuso cikin rayuwar Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni, ta karfi da yaji ba tareda ya bukace ta ba. Ko wacce irin tarba zata samu daga PRINCE ABDULRASHEED din? Ko zai yarda ya hada rayuwarshi da ita? Ko zaiyi maraba da zuwanta cikin rayuwarsa? Akan karan kanta shin ko zata iya sakewa ta rayu da wani da namiji a duniya ba Ishaq ba? Wadannan sune tambayoyin da Aishatu-Siddiqah ke yiwa kanta a kan hanyar su ta zuwa Airport, ba tareda ta san amsar ko guda daya ba. Sannan bata kuma da wanda zai amsa mata. “Bashi da lokacin kowa a duniya irin Dawakansa. Ba abinda ya baiwa muhimmanci a duniya bayan ibadah irin hawa Doki. Abdulrasheed yana matukar son Dawakansa, lokacin shi nasu ne. He enjoys riding horses more than anything in his life!”. Siddiqah ta tuno wasu daga cikin kalaman mahaifiyarsa akansa, a lokacin data ke yawan gaya mata ko wanene dan ta Prince Abdulrasheed Kehinde da halayensa, wannan har mijin da yake da lokacin mace ne a rayuwarsa, balle ita karan kada miya Siddiqah Yunus? A wancan lokacin da Nenne ke yawan bata wadanna labaran nasa, ta kan zama bored da sauraronsu, har ta tambayi kanta ko meye alaqarta da labaran da Nenne ke yawan bata akan shi da rayuwar shi? Yanzu ta gane cewa Nenne na bata labarannan ne don ta san cewa ko ba dade ko bajima, tana raye ko bata raye tunda aure ya riga ya shiga tsakaninta da Prince, watarana irin wannan na zuwa, wato ranar da rayuwarta zata shige sukuf! Cikin ta Dan Nenne wato Hamma Abdulrasheed (Prince), a daidai lokacin da bata zata ba kuma bata shirya ba, shima kuma ta tabbata haka tarewar tata zata zo masa bagatatan. Bata gushe ba tana ta wadannan tunane-tunanen har suka iso iyafot din Murtala Mohammed. Seun, shi yayi tsayuwar tsayin daka akan kayanta, har aka gama checking aka aunasu a jirgi. Ya rage dan lokaci jirginsu zai tashi, sannan ne Dade ya bata tikitinta da Fasfo dinta a hannunta. Yace da ita “nan da awanni 22 zaku sauka a kasar Argentina. Kada ki damu, na riga na gaya masa karfe nawa zaki taso, da lokacin saukarki. Kina sauka zai zo ya daukeki da kansa a filin jirginsu. Inji dai zaki gane kamannin Yayannaku? In ma baki gane shi ba na tura masa hoton ki, na jikin pasfo dinki, na tabbata shi zai gane ki”. Siddiqah ta gyada kai, tana fakar kallon Dade tana hadiye hawaye har wasu suka ballo kan kuncinta suka ki hadiyuwa, ta sharesu da gefen gyalenta. Dade ya lura kuka Siddiqah take yi kasa-kasa, yaji babu dadi a ransa, nan yaji duk guilt ya kama shi da bazai kama hannunta ya kaita har gaban Abdulrasheed da kansa ba, ya hada su yayi musu nasiha ya bashi amanarta, amma Emir ne ya ce masa kada yaje, ita kadai ya yarda a tura, in yaso a gaya masa ta taho, yaje ya dauketa da sun sauka, dattijon Bayeraben mai ran karfe shi kadai yasan hikimarsa ta yin hakan. Amma anya ba Prince din ya kamata su takurawa ya tako ya zo ya dauketa da kansa ba? To amma basu da mafita sai wannan guda daya, don iyaka tunaninsu sun san ba zai zo ba din, duk iya kiran da zasu yi masa in dai akan mace ne. bazai ce bazai zo ba amma zai yi ta zamewa ne cikin hikima ba tareda ya bata musu rai ba har sai sun gaji sun rabu dashi. Dade ya dafa kafadun Siddiqah a hankali yace “Be strong my daughter. Allah yana tareda ke kin ji, addu’o’inmu na tare dake, daga tashin ki har ki sauka ba matsala. In sha Allah. Ki fuskanci mijinki da karfin zuciya kada ki karaya da komai zaki gani akansa, kullum ki tuna cewa zaman jihadi ne zaki yi babba, na gyara rayuwar Abdulrasheed ya karbi rayuwar iyali. Ke ce kadai zaki sa ya goge tabon da yayiwa mata daga ransa, ko yaci gaba da yi muku kallon da yake yi muku bakidaya. Siddiqah ke kadai zaki sa Abdulrasheed ya gane ya kuma banbance cewa yana missing wata rayuwa mafi girman daraja daga wadda ya baiwa amanna a rayuwarsa; wato tsakanin rayuwar aure da tara iyali da kowanne dan adam mai lafiya ke yi, koko ta neman duniya babu wadanda zasu taya shi ci da morar duniyar, ke zakisa ya yarda akwai abinda zai bashi pleasure in this life fiye da hawa Dawakansa. Wuce ki shige ana kiranku, Allah yayi muku albarka bakidaya”. Da baya da baya take tafiya tana kallon Dade, mutum mai tarin karamci da kulawa a gareta, hawaye fal idanunta, shikuma Dade bai bar wajen ba, haka bai gushe ba yana aika mata murmushin karfafa gwiwa har ta shige cikin boarding passengers. ***** ***** ***** Lokacin da jirgin Argentinian Airways wato (Aerolineas Argentinas) ya daga da SIDDIQAH YUNUS tana daga zaune jikin tagar barin dama na jirgin, idanunta a lumshe, tayi kukan har ta gaji, sai ajiyar zuciya take yi yanzu kuma, zuciyarta ta cunkushe da tunaninninka marassa dadi; muhimmi cikinsu shine ganewa data yi iyayen Abdulrasheed bakidaya sun dora hope din daidaituwar rayuwar tilon Dan su a wuyanta, wato samuwar farin cikinsa da canzuwar rayuwarsa ta hanyar aure. Dade da Nenne, Sun bata dukkan ‘trust’ dinsu, da duk wani fatansu nagari na cewa ita din a yadda take da kuruciyar nan (in her teens) zata ita iya canza Prince Abdulrasheed mai shekaru sama da arba’in daga rayuwar data sameshi a ciki, ya kuma karbeta ya bata gurbi tare dashi ko yanaso ko baya so. Gashi tasan bata taki komai ba, bata da idea bata da wata fasaha akan zama da Dan su Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni, wanda alamu sun gama nuna ba ita Siddiqah kadai ba, baya maraba da kowacce mace cikin rayuwarsa balle ita diyar Mallam Yunusa. Ko abubuwan nan da Kiki tace su suke gigita maza su so mace, ita Siddiqah bata dasu bata mallaki ko dayansu ba (frontward-backward) ta bakin Kiki. Taji da kunnenta sanda Murjanatu (Taiwo) take kusheta, Ya Allah! Murjanatu ma kenan wadda tafi kowa kusanci dashi, tafi kowa saninsa, ta san abinda zai iya so da wanda bazai taba so ba, balle ita Siddiqah da ba sidi ba sadada! Tsabar tunani irinna rashin self-confidence, lack of motivation da inferiority complex da suka bi suka dabaibayeta yasa har aka ajiye mata abincin jirgi a gabanta bata sani ba. Abu daya take da kwarin gwiwa akansa har gobe, idan ta tuna cewa ita bafullatana ce a kansa, tanada wannan ego din na cewa kabilar data fito tafi