Sashe 11
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Horse din mai ciwon kafa an duba shi? Pareto ya amsa cike da girmamawa cewa tun jiya ya kira vetrenary doctor dinsu ya duba shi, kuma ya bashi magani tun a lokacin ya fara warewa. Pareto yana so ya tambayi ubangidansa ko matarsa ce wannan din ya auro daga Nigeria? Don dai bata yi masa kama da irin masu biyo shi har gida ba, haka bata yi kama da mutuniyar banza ba, ko ‘yan uwanshi mata dake zuwa wadanda duk ya sansu farin sani. Amma Prince kaman ya san haka, sai ya hade giran sama dana kasa ya daure fuska sosai, ta yadda babu fuskar ma da zai jefe shi da tambaya akan Siddiqar, don shi a wurin shi karshen abin kunya nema yace da Pareto wannnan ‘yar kankanuwar yarinyar da bata fice ‘yarsa Kiki ba; matarsa ce. Prince ya isa ga Saheeb yana masa gaisuwar yammaci irin yadda ya saba da yarbanci, ta hanyar yi masa hira cikin native yaren nasu, yana yi yana shafa kwantaccen gashin wuyansa, dokin yana haniniya yana zambarwa irin yadda ya saba in yana tareda Prince. Daya bayan daya yake duba lafiyar sauran dawakan dake cikin stable. Pareto na biye dashi a baya suna zaga tsakannin Dawakan suna maganarsu kadan-kadan cikin yaren kasar Argentina, ya gaya masa zai tafi kasar France yin Wani tournament kuma zai dauki akalla sati acan kafin ya dawo. Pareto da karambani da wuce gona da iri sai ya jefo masa tambayar data fado a ransa. “Boss, bakuwa fa? Yaushe zata tafi ko tare zaku wuce kasar France din?” Wata harara da Prince ya juyo ya zabgawa Pareto tasa ba shiri Pareto ya kai hannu ya rufe bakinsa yana bada hakuri. “Amma ka san abinda zai kai ni can tournament ne ko? Tukunnama meye business dinka da zaman bakuwa a gidannan? Ko akanka take zaune? Na yi maka zancen ka taimaka mata da wani abu ne? Kayo mata cefanen duk wani abu da zata bukata, final. Inma akwai abinda babu cikin kayan daka sayo tayi magana sai a karo". Pareto ya amsa a ladabce da "an gama Master". Ko ba’a ce ta fara girki ba ta yanke shawarar daga gobe zata fara dama. Don da daren ranar tazo cin abincin dare again ta ci karo da Ekele, Moi-Moi da Akara. Koda dai ta iya ci duka a Lagos, to fa tana ci ne ba don ra’ayi ba, sai don ta samu yayi mata maganin rama da cikowar kasusuwa. Amma a nan kam bazata ci ba sai dai yaci abinsu shikadai, abinda ranta yakeso zata dinga dafawa na kasar haihuwar ta. In yaso tunda Nenne ta koya mata yawancin girke-girken da Prince ke ci din kuma tayi mata guzurin kayan girkin duka, to zata fara gwada yiwa Uncle AK girki da kanta, ko don ta gwada kwarewarta a iya girkin yarbawa data samu gun Nenne. Washegari Siddiqah data fito kitchen cefanen da aka jibge mata kowanne a muhallinsa da wadanda ke cikin freezer ta fara zuwa tana duddubawa, ta sha mamaki da taga kusan duk abubuwan da aka sayo din kamar ta bada list, don yawanci ire-iren abincin da Hamma yake ci dinne aka kawo kayan dahuwarsu. Bata san cewa restaurant din da yake karbar abinci Pareto yaje ya karbi lissafin komai ya sayo mata ba. Ta maida komai inda ya dace ta canza daga yadda Pareto ya ajiye shi, tazo da guzurin spices dinsu na yarbawa da sauran kayan kara aroma din girki. Nenne har yajin borkono da tasan bata rabo da cinsa ta sa an daka mata ta hado dashi cikin kayan ta, sai ta dauko su duk tayi musu mazauni a ma'adanan kitchenette din. Daga nan Siddiqah ta zage ta hau girki. Tana yin abinta cikin dadin rai domin sosai take jin dadin aikin da take yi din. kafin awa daya ta kammala duk abinda tayi niyyar yi ta taimakon injinan saukaka girki. Ta ajiye masa nasa anan kan dining da yake zama yaci. Ta debi wanda zata iya ci ta shige dakinta ta rufe. Prince sai sakkowa yayi ya tadda breakfast mai rai da lafiya an shirya masa, plantain, chips, da moi-moi, sai kunun acca da yaji madara wanda shima Nenne ta koya mata. Bayan ya san ba abunda ya baiwa Pareto order kenan ba. Amma wannan din ya bashi sha'awa sosai don haka ya zauna da kyau ya soma ci. Har yaci ya gama bai san ita tayi ba, saidai tabbas yaji dandanon abincin ya canza a bakinsa, sannan kunun ya bashi mamaki, tunda bai taba odarsa anan ba. Nenne ce kawai take yi masa, kuma wani ikon Allah bai tambaya ba. Yaci yayi nak, with excitement ya mike, tana hangoshi daga bayan curtains din dakinta sanda yake cin abincin har ya gama ya fita jogging din safe cikin gidan gonar inda acan zaiyi excercise dinsa. Aisha da tayi wanka wajen karfe 10 na safe wata riga t-shirt mara nauyi da dogon siket baki ta saka ta haye gadonta ta dauki wayar da ya bata tana danne danne. Kamar yadda Prince yaki bata lokacinsa ya koya mata amfani da wayarsa ta yarda komai sai in baka sa kanka ba, amma yanayi (condition) na bukatuwarka da abin zai sa ka koya komai wahala ko rashin wahalarsa. Don kuwa a hankali tana bin umarnin wayar sai gashi ta gane yadda zata saka lamba tayi kira, da yadda zata yi chatting ta whatsp da sauran social media platforms. "Umman Siddiqa" wato Ummanta Haj. Zainab Yunus ita Siddiqah ta fara kira (with nostalgia). Haj Zainab ko da taga lambobi rankatakaf na kasar waje data kasa gane ko daga ina suke jikinta ya bata matafiya an sauka lafiya a kasar Argentina. Tun tafiyar Siddiqa take ta binta da addu'a tun komawarta Lagos daga sallamar da taje musu kan duk inda ta samu kanta a gidan aure Ubangiji ya zama gatanta, ya huwwace mata tausayin mijinta, tarbiyyarsu ta zame mata jagora. Tana dagawa din kuwa sai taji muryar Petel dinnata. Tana fadin “Ummana kina ina? Petel dinki nata kewar ganinki tun jiya. Na sauka lafiya a Argentina Ummana”. “Petel dina am miyelwa mi, kada ki damu da tunanin kowa, duk muna lafiya cikin alkhairi, aure neya gaji haka kinji ko Petel dina?” Kukan shagwaba ya zo. Aisha ta soma sheshsheko shi, Umma tayi maza tace “lala-lala Petel, in haka ne zan daina daga kiranki, Petel din Umma. Ko bangon duniya suka tura ki kije ki zauna da mijinki lafiya kinji Petel dina. Banda rashin karar nan taki da nasanki da shi da keke da kekenki, watarana ‘ya’yanki zasu yi miki fiyeda wannan biyayyar da kika yi mana in sha Allahu”. Da kyar ta samu Petel ta hadiye kukan shagwabar suka koma hira. Ta tambayeta ya ta samu bakon wurin da maigidan nata?” Siddiqah ta soma magana cikin tsananin gaskiyar dake ranta cikin fulatanci. "Uncle AK yanada kirki Umma. Kinga har wayarsa ya bani, don in sake in ji dadin zaman gidan, kuma in nayi masa magana yana amsawa. Amma Umma idan na tuna shi din bayerabe ne, duk kyawunnan nasa irin na Nenne, sai inji wani iri a raina….”. Bada niyyar labe Prince yazo dakin nata ba, yazo ne ya tambayeta koda abinda babu na cefane da shoppping yasa a karo mata saboda zai yi tafiya har ta tsayin sati daya. Sai kawai ya tsinkayi tana fadar hakan ga mahaifiyarta a waya cikin harshen fulatanci. Bai fasa shiga dakin ba yasa kai ya shigo da sallama, duk kunya ta kama Siddiqah. Umma na fadin. “Akul Petel, ko Allah hoddiri fe’an, be tagu fe’an (wato abinda Allah ya riga ya rubuta mata kenan wanda babu makawarsa). Zaman aure ba ruwanshi da kabilanci. Tayi maza ta kashe wayar cike da fargabar ko Uncle yaji me take gayawa mahaifiyarta akansa? Sai kuma ta cewa kanta ai ba lallai ya zama yanajin fulatanci ba yarbanci da turanci kawai ya ke ji. Da wannan Siddiqa ta karfafi kanta ta mike daga kwanciyar, ta boye wayar a kasan filonta duk guilt ya baibaye fuskarta. Hakika Prince yaji abinda take fadi din don shi yama fi jin fulatanci sosai har fiyeda harshen Yoruba, don dashi Nenne ke masa magana tun yana yaro har girmansa haka Nani Oummana. Har ransa yaji wani iri shima, kwatankwacin abinda kanwarsa Fatima ta gaya masa kenan akan Siddiqah wato har yanzu kabilancin nata da saura. Ba tareda ko a fuska ya nuna mata yaji ba, sai kawai yace, “Madam din gidan nazo in miki sallama, koda abinda kike bukata? Zan dan yi balaguro na wani lokaci". Siddiqah wadda ke ta fama da kayan guilt dinta, wanda ya kusa nutsar da ita cikin kasa don kunya kasa amsawa tayi. Nan dai ta hau 'yan mutsu mutsu na rashin sanin abin cewa, da ya ga ta kasa bashi amsa duk ta takura da guilt, sai yayi murmushi kawai ya juya ya fita abinsa. Kai tsaye dining ya nufa, ya zauna yana kokarin hada coffee, amma koda ya hada din ya kasa kaishi bakinsa sai juyawa yake da cokali a hankali. Tambayar kansa yake ko ta yaya zaman aure zai yi dadi tsakaninsa da Siddiqah tunda ita ga alkiblarta akan kabilarsa? Ya tambayi kansa yaushe ne za’a daina nunawa juna kabilanci tsakanin hausa Fulani da yorubawa ne? Yoruba da yawa da ya sani ko a cikin Akannis akwai wadanda basa cin abincin hausawa, da an ambaci bahaushen mutum kallon wani jaki, dakiki suke yi masa. Shikuma a matsayinsa na bilingual babu wanda zai ce ya fifita tsakanin wadannan kabilun, duka yana girmama kowanne saboda Nenne da kuma Dade dinsa da suka fito daga cikinsu, don haka Hausa/Fulani da Yoruba, basu da banbanci a wurin Prince. Sai ga Siddiqah ta fito falon kamar mara gaskiya. Prince don ta saki ranta da kansa ya ja mata kujera yace ta zauna. Zamanta keda wuya ya juya harshe zuwa fulatanci gangariya, yana tambayarta me zaya zuba mata cikin kalolin abinci na kasaita da yasa aka kawo wajen dake jere bisa tebir? Shikuma Prince abinda yaji ta fada ne yasa yake son tabbatar mata yana jin fulatanci fa, ba ita kadai ce bafullatana ba, yanaso dai ta sabawa ranta da kasancewar asalinsa Yoruba ne ba canji. Yanada kyau tasan cewa Bayerabe ta aura (a proud one)!”. Abinda tayiwa kanta alkawarin ta daina