← Book details Afnan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 10

Sashe 8

Afnan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" na rantse da
allah ta fada tana yar dariya. shiyasa nace
maki wlh ki daina wannan furucin , yarima
baya taba iya rabuwa da ke. da yayi maki
fada yanzu har yai fushi ai da sai kiyi tunanin
cewa inna fa mahaifiyarki ce amma ya nuna
damuma fiye da taki, ke bama abin
alfaharinki ne ma kina in a wanna zamanin
akeyin fito na fito da surakai? to wallahi ki
gaggauta zuwa ki bada hakuri sannan kada
matsalar gimbiya ta sanya kiyi watsi da
masoyinki, baraka ta shiga a sami rauni
wannann shine babban burinta. nayi kasa da
murya " amira nagode allah ya bar zumunci".

Amin amin, na gode sai munyi magna. na
dafe kaina tsananin tausayin yarinma ya
mamaye zuciyata kmr kaina zai bare. a
hankali na mike ,rabi na goge wasu zannuwan
gado nace "ina yarima ne ko ya fita?" "A'a
yana dakin chan" ta nuna min da hannu na bi
sirdaden da ta nuna na sa hannu na murda
gaa mamakina naji ta bude. na shiga sai na
ga tankamemen falo ne daa yaji kayan gayu
irin na zamani. na hango kofa daga yamma
alama nan dakin yake na hanzarta isa tare da
budewa. jin an bude kofar yasa shi dagowa
da sauri na lura da idanunsa sun yi ja matuka,
shi dai kam bacin rai na haddasa masa jan
idanun, na fada a zuci saboda yadda na san
idanunsa farare tar har wasu ruwa kake gani
kwance saboda haske. ganin nice sai kawai ya
maida kansa ya
kifa kamar yadda yake kwance ruf da
ciki.tausayinsa ya kamani ,naji kamar na dago
shi na rumgume a yadda naji sonsa ya karu a
raina. sai dai miskilancina bazai barni aikata
hakan ba, na zauna bakin gadon gab da
kafafuwansa ko motsawa bai yi ba. na rasa
inda zan fara, toh me zan ce masa? daraba ta
fado min.

"amma yarima wannan kwanciyar
ce fa aka haramta saboda ta yan wuta ce
babu kyau yin ta" a hankali ya juya amma sai
ya bani baya ya kalli can. raina ya bani fushi
yake yi." allah ya baka hakuri" na fada a
hankali. bai dai ce komai ba bai kuma motsa
ba, nan da nan kunya ta baibaye ni naji duk
na tsani kaina. na tuna irin dizgi da wulakanci
sa da gimbiya ta sha, ba shi da wuyar dizgi ai
sai na raina kaina.

Na yunkura zan tashi gwiwa
sake ina
nadamar kawo kaina, sai kawai naji an ruko ni
ta baya."ina zaki je kuma? haka ake lallashin
maigida idan yayi fushi?" na sunkuyar da
kaina, ya buga tsaki "ni di wanna kunyar
wallahi tana kwarata....zo na koya maki yadda
ake bawa maigida hakuri" ya shiga yimin
cakullulo tun ina zillewa har na hau kyalkyata
dariya sai kawai ya kura min ido, nayi saurin
rufe idona shi kuma ya kai bakinsa ga nawa
nan da nan yaren ya sauya.******** Cikin
kwana uku ya bude min ido ya koya min son
sa da tarairayarsa muka bude sabon shafin
soyayya.na yi nadamar rashin sakin jikina da
nayi tun farko na gane cewa lallai ba karamin
so yarima ke min ba, ban da shagwaba babu
abinda yake zuba min , duk yadda na wasance
dole wani abun idan yayi min shi sai naji kunya,
shi k
uwa banda
zagi babu abinda yake yiwa kunya, wai kunya
na kwarar sa (mata a rike kunya domin ita ce
adon mace, wallahi duk yadda kuka dade da
miji ki rika nuna kina jin kunyar sa wasu
lokutan musamman lokacin da kuke kebe
kudai yana karawa mace martaba da kima a
idonsa).

Kullum cikin zabga karya yakeyi a
asibiti cewar yayi tafiya ne maimartaba ya
aike shi.

Washe gari ya kama zai koma gidan
gimbiya kamr kar ya tafi nice me kwarin
gwiwar bashi magana, da kyar ta tafi wajan
karfe biyar na yamma. kullum yana zuwa da
safe mu gaisa da marece kuma ya dawo yi
min sai da safe, ina lura dashi sam
walwalarsa ta sauya amma sai kawai na share
na san shi da mutuniyar ne ni dai allah ya min
alamnashara.

Rnar da zai dawo ina ta shiri
sai ga shi ya shigo da sauri ina zaune bisa
kujerar gaban madubi.

Humaira am sorry kano
zanje yanzu aka
aiko maimartaba baban gimbiya bashi da
lafya har zaa fidda shi waje shine zan kai su
umma suyi masa allah ya kiyaye hanya yanzu
haka gasu chan suna jira na. nan da nan halin
namu ya motsa wato KISHI wani kallo na fara
jefan sa da shi tukun kafin nace "duk gidan ku
a rasa direba sai kai?" abin mamaki sai naga
kamr ransa ya baci.

"haba humaira ina laifi
dana ma zo yi maki bankwana da kiji cewar
na tafi ba?" yanzu haka na fada maki ga su
maimartaba can a waje suna jira na idan ba
ke ba wazan wa haka?" ai naga kana ta faman
kyarma ne zaka gdan surukai" kema haka ake
kyarma idan zaa gidan naki.... maganar ta
maqale daga karshe alamr SUBUL DA BAKA
yayi. in shirin maida masa sai kawai ya fice,
wani gululu ya taso min.

Banyi barcin kirki ba
ranar, kagara nake
ya dawo na amayar masa ta cikina. haka
abinci ko ruwa na kasa sha. har yarima ya is
aya wulalantani abinda kawai nake nanatawa
araina kenan. kwance nake daki naji shigowar
sa na mike tsaye tare da rike kugu yana
shigowa ko rufe kofa beyi ba na hau masifa
daman ance me shiru-shiru be iya fada ba.

"da zaka fada min magana kan wata banza na
taba aiken ka zo?" ko kuwa na taba aiken ka
wajan uwata....." haba humaira wai maganar
bata wuce ba?" toh kiyi hakuri ni da wasa na
fada."eh din ai da wasan daren ake fadawa
wawa magana.

"duk naji kiyi hakuri dan allah
wai dole sai ka zuna da ni ne?nace bana yi ko
dole ne? ya kyakyale da dariya dama na lura
sai gumtseta yake yi.

Raina ya kara baci wato
ya maida ni mahaukaciya sai naga ya fara
rawa yana waka 'ashe ana kishina ana kauna ta,
a'a lallai yarima taka-taka' Ban san lokacin da
nima na kyalkyale da dariya ba,saboda ko
waye sai ya dara idan yaga yadda yarima ya
dage yana kwasar rwa. ya daina rawar tare
da daure fuskar nan irin ta shagwaba.

"gaskia
ni dai a cigaba da fadan bana so a daina " ni
dai na cigaba da murmushi, yana matso yana
yar dariya "muguwa na gane ki ashe haka nan
ake wani basar wa kaunar yarima tayi katutu
a rai?" nayi murmushi "eh din an ji" ya
rungumo ni "me aka ajiye min?" ina shirin
bashi amsa wayar sa tayi kara ya zura hannu,
sai naga ya sake ni da sauri ya latsa tare da
sanya handsfree yayi kasa da murya "Allah ya
taimake ka" "zancen banza zancen wofi, yanzu
nake
jin labarin ka raba gida, wannan ai shirme ne
lallai ka hanzarta hade matanka waje guda tun
kafin raina ya baci,yaushe zaka iya adalci
matukar basa tare? anya kai jarumi ne yrima?
ba ka iya daidaita matanka?oh allah wadarai
a yau nake so ka maida wacce ka ware maza-
maza. yana gama fadin haka ya kshe wayar.

Gwaram! na koma na zauna tare da dafe
kaina . ya kalle ni "kiyi hakuri sai ki tashi mu
tafi kar abin yazo da bacin ran sarki" Wayyo
ni humaira Wayyo Allah na.

Tunda muka fito
gbana yake faduwa ni na tabbatar idan aka
auna jinina a yanzu ya kai dari biyu da wani
abu. har muka isa ina rike da kaina shi dai bai
ce komai ba.

Komai yana yadda na barshi su
rabi suka shigo min da akwatuna na.

Nayi
tsaye sai zare ido nake ina kyarma ya shigo
da sauri. haba humaira duk kin bi kin tada
hankalin kan waccen yar iskar.

Bai rufe baki
ba sai gata "Don ubanki har kina neman raba
ni da shi bayan kin samu kin shigo?" Bata rufe
baki ba ya wnka mata mari uku a jere,sannan
ya kwale belt ya fara tsula mata ta duke kawai
tana kuka tana faman karewa.

Na rike shi
"dan allah ka kyale ta,wayyo ni humaira" na
fada ina kuka. bai saurare ni ba na janye shi
baya ta sami halin mikewa tsaye ta nuno ni da
yatsa "wallahi sai na rama kanki shegiya" zai
kara damko ta tayi waje da gudu. tana fita
yaranta suka boye saboda duk sunji abinda ya
auku. ya kalle ni a fusace "Haka zaki yi mata
duk ranar da ta kara zuwa miki ida yar iska"
ni dai a sukurkurce na kwana,washe gari ya
fita da wuri saboda zai je tiyata. na kulle kaina a
daki har kusan karfe
daya saura sai da yunwa taci karfina sannan
na fito.

"Rabi dan Allah kawo min tea" tace
"to" tare da juyawa. ni bana sha'awar wani
yayi min aiki amma babu yadda na iya
saboda masifar gimbiya.

Ganinta nayi kamr
an jeho ta, nayi saurin mikewa tsaye ban
ankaraba ta rufe ni matsiyacin duka na dinga
kokarin rugawa amma ta babbake ta hani ni
wucewa.

Tun ina motsawa har jikina yayi
tsami ni dinga rizgar kuka.

Sai da ta barni
kwance tukun ta fita.

Rabi ta shigo dauke da
tire duk jikinsu yayi sanyi "Sannu ranki shi
dase,sannu!" Dagwayye ta fada lokacin da ta
ke kokain daga ni ta maida bisa gado.

Rabi ta
kalle ni "Wallahi sai kin tashi tsaye gidan nan
lallai gimbiya kwararki za ta ci gaba da yi dan
bata fi karfin ki
bakawai kin sawa ranki tsoro ne" Shiru kawai
nayi masu, fuskata tayi jawur saoda duka ga
shi gefe daya ya kumbura .

Na samu na kurba
ruwan tea din sannan na sallame su. karfe
yarima ya dawo hankalinshi yayi mugun tashi.

"Himaira lafiya me ya same ki haka? na
langwabar da kaina sai kuka.

"Badai fareeda
bace ko?" me tayi maki?" nan ta shigo"?Duk
ya kidime ya rude, nayi saurin girgiza kai
"Faduwa nayi a bandaki silbi ya kwasheni...."
Subhanallahi, Rabi,Rabi!! ya daga murya kamr
ba shi ba sai gata da gudu "Don me zaku rika
wanke toilet ba ku gogewa? maza je ki tsane
duk wata lema da ke ciki". sumi-sumi ta
wuce.
Chapter 8 · 0% Book details