Sashe 2
Afnan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na fada a raina.
Wai mai yasa kike mun rowar
maganarki Humaira?
Ko don kin ga tana kara
kayata zuciyata ne?
Na rufe idanuna ko ya za
a yi in san haka?
Baza kiyi min magana ba?
To bari na cije bakin da ke yi min rowar
sai......
Nayi saurin bude idona.
Yayi
murmushi yace Matsoraciya goge wadannan
hawayen muyi magana.
Nayi saurin kallonsa
alamar ya sake ni.
Ya
kashe min ido daya.
Ki goge da jikina mana?
Bansan lokacin dana balla masa harara ba, ya
kyalkyace da dariya.
Wannan irin horo?
Ya
sake ni, amma yayi saurin sanya hannusa
yana goge min fuska.
Hankalinka ya kwanta
yau hannunka ya taba fuskata.
Na fada a zuci.
Na yunkura zan tashi ya dakatar dani.
Tsaya
gimbiya, ai yau sarautar hannunki ta ke.
Ya
mike tare da zama kasa daidai kafafuna.
Wallahi bani son irin wannan abunda yarima
keyi mini.
Na kara daure fuska tamaubabu
alamar fara'a ko kadan.
Ya kwantar da murya
a nutse yace.
Humaira kina da tsoro?
Tambayar tasa tazo mini a hagunce kamar ya
fahimce ni, sai yace.
Ma'ana kina iya kwana
gidan nan ke daya?
Nayi saurin daga masa kai
alamar iyawa.
Tsakaninki fa da Allah kina iya?
Bana son ki
kwari kanki idan baki iyawa na samo maki yar
kwana.
Ina iyawa, na fada da kyar.
Abinci fa
kin iya dafawa ko a kwao mai koya miki?
Kamar zance na iya amma kuma wata zuciyar
ta gargade ni dana ce a kawo., saboda
yanayin abincinsu da namu lallai akwai
bambanci mai girman tazara.
Na ce Aa.
Ya
kalle ni da fadin.
Ban gane ba?
A kawo na
fada a hankali.
Da kyau ya fada yana
murmushi.
Kina son mai share share ko za ki
iya da kanki?
Allah sarki Inna ita mai lalura
yanzu wa zaiyi mata share sharen?
Na girgiza
kai, zanyi da kaina.
Lokacin idonuwana suka
ciko da kwalla.
Ya matso kusa dani, kiyi
hakuri.
Yarima ya ishe ki da tambayoyi, ke
kuma ba kyason tambaya ko?
Na dai yi shiru
kawai.
Wadda zata koya miki abinci ita zata
nuna miki komai na gidan nan.
Koda wasa
karki nuna mata ke matatace.
A firgice na
kalle shi.
Ya kawar da fuska yace Zan sanar
da ita ke matar abokina ce Haka sauran
wadanda ke nan shiyyar saboda gudun
matsala kafin Allah yasa mu daidaita da
maimartaba.
Wayyo ni Humaira na shiga uku!
Kwallan da nake kokarin mayarwa suka fito
day bayan daya.
Kiyi hakuri Humaira, wallahi
duk saboda kwanciyar hankalinki zanyi haka
Kada ki damu Allah na bayan mai gaskiya
kinji ?
Yau zan wuce mu tafi da maimartaba
Eygpt idan an dace muyi kwana hudu zuwa
biyar Idan kuma an sami akasin haka to sai
yadda Allah yayi.
Take kwalla suka karu ni kuma haka Allah ya
tsaro min tawa rayuwar??
Ya kalle ni, Don
Allah Humaira kada ki sanya wa kanki
damuwa kinji?
Da na dawo zamu je Kano ki
gano su Inna kiyi kokari ki kwantar da
hankalinki yadda za su ga cewar ba ki cikin
matsala.
Kuma insha Allah idan komai ya
daidaita ina son dawo dasu kusa damu
Saboda Inna na bukatar kulawa.
Naji wani
sanyi a raina tare da goge kwallan da ke
fuskata Ya miko mini sabuwar waya yana
cewa Akwai lambata da ta Inna a ciki Kada ki
saka lambar kowa sai da izinina kinji?
Nace to
Wayarsa tayi kara ya dauka Hello!..........ok
Ina kan hanya gani nan isowa Ya dawo da
dubansa gare ni Ya shiga wani daki kusan
mintuna hudu Ya fito rike da wata leda Ina
kallonsa ya bude wata dirowa ua dauko wani
dan kwali karami ya gama yar diminiyar sa ya
fita.
Na kwanta dabas kan kujera.
Allah gamu
gare ka Har kusan karfe daya ina nan zaune.
Kofa naji
ana kwankwasawa na leka sai ga wata
katuwar mata tsaye.
Na bude mata sai fara'a
take yi.
Yanayin gaisuwar da muka yi da
yadda ta ke magana na gane cewar ba
cikakkiyar ba hausa bace.
Tace nice wace zan
koya miki abunci.
Ta fada tana mai fata'a
sosai.
Nima cikin sakin fuska nace mata.
Ba
matsala.
Na kawao mata lemu a firij din da ke
falon mai sanyi da ruwa Sanana na kalle ta
Don Allah ki bani mintuna kadan zan yi sallah.
Ta risina cikin girmamawa har mammaki ya
kama ni.
Tace As u said Madam no problem
Toh ai kinji fa ni fa bana son turanci yayi yawa
a magan Ko kuma ayi shi cikin sauri domin
karatun nawa yanayinsa akwai da rauni.
Lokacin dana fito nayi mamakin ganinta dana
yi a bakin wata kofa.
Tayi hanzarin karasowa
kusa da ni.
Yauwa madam muje.
Na bi
bayanta sai na ga ashe kicin dinne To ya akayi
ta sani??
Ban sami damar samu amsa ba Ta
katse ni da cewa Yallabai kwana biyar ya
bamu Saboda haka ki dauko biro da takarda
ki ringa rubutawa Saboda gaba rana daya kina
iya mantawa da wani abun Na kalle ta sosai
nace Bani da biro gashi ni bakuwa ce a gidan
Tayi murmushi tace Ayya bari na baki Ni ina
dasu.
Nafisa A.
Mamawa
Tabude jaka ta fiddo wani dan book da biro
tamiko min, A kullum zamu ringayin abubuwa
uku zuwa hudu, ko fin haka idan akwai time,
tabude wani katon firij dake kicin din, shakare
yake da kayan lambu da naman kaji dana
dabbobi, wani kuryar daki dake kicin din
shima cike yake da kayan abinci na
buhunhuna dana kwalaye, ga doya, dankali,
kwai, da sauran tarkacen, ta debo dankali
tace hajiya zan ringa yimiki bayani kina rubuta
wa, nikuma inayi a aikace kina gani, na ce to.
GIMA POTATOES ABUBUWAN DA AKE
BUKATA, dankalin turawa, tattasai, Attarugu,
Tumatur, albasa, gishiri, curry, thyme, karas,
pies, green beans, green pepper, alayyahu,
kwai.
A fere dankalin turawa kar a yanka, a
barshi haka da girmansa sai ki daka tattasai,
attarugu, tumatur da albasa, kisoya sai kisa
ruwa kizuba dankalin, kisa su maggi, gishiri,
curry, da thyme, ki yanka kayan lambumki irin
carrot, pies, green beans, green pepper,
alayyahu.
Sannan ki fasa kwai kamar biyar ko
fin haka kisama masa curry da albasa da
maggi kisoya shi.
Kiduba dankalin inya dauko
Dahuwa sai kijuye soyayyen kwan da sauran
kayan lambun.
Banda alayyahu, shi ki samasa ruwan zafi ki
tsane shi, saiki sa namanki ko kifi ko kibarshi
haka, kibar kayan lambun suyi laushi ruwan
kuma yayi kauri, sai kisa albasa da alayyahu
kirage wuta, tayi dariya tace yanzu zakiji shi a
bakinki, a time din data gama yawuna har
tsinkewa yakeyi domin yunwa nakeji nakuma
na cika flet na kuma gefe, gaskiya yayi dadi
wannan gima potatoes din, tayi dariya tace to
kidai rage wuri ga abinci na biyu mai suna,
KABBANI RUS RICE, abinda ake bukata
nama, albasa, maggi, kayan lambu,
tafarnuwa, Cinamon, Cadamon, mint,
Attarugu, Yogot, basmati rice, ki yanka nama
kanana sai ki tafasa, kidan soyashi sama
sama, kiraba shi biyu, kidauko basmati rice ko
kuma wadda kike amfani da ita kidafata
ruwan naman sama sama sai ki yanka karas,
garlic, pies, albasa, ki hada su guri daya, sai
ki daka attaruhu banda tattasai kisoya kizuba
su karas, nama, garlic, maggi, da dai sauran
su, ga wanda bai shan yaji ana iya amfani da
tattasai zalla cinamon, cadamon, mint, sai ki
zuba yogot cokali uku ko hudu, in kina son
zaki dayawa, idan kuma bakiso sai ki zuba
kadan, to your taste.
Idan kin gaggauraya sai
ki juje guntun ruwan
silale a ciki idan yatafasa sai ki sa albasa
kirufe ta, kirage wutar har ya tsose yadahu,
zaki iya mata sos din albasa da garlic da
attarugu ko sos din tumatir kawai ko kici
haka.
Idan kikayi wannan sai ki sami
mangwaro tunda gaki gidansa akwai manya
manya nan sai bare bayan saiki yanyanka shi
kicire kwallon, sai kizuba tsokar mangwaron
atukunya kisa citta, kanunfari, kuzuba ruwa
kidora a wuta yadahu sosai yafara fashewa sai
ki burge shi kikara ruwa kitace kisa sugar da
fulawa kisa firij.
Ta koya mata abinci da dama( na tsalake ne
saboda nasan dayawanku kun iya
musamman...inma da wadanda basu iyaba
bazasu wauce abokanainaba su kuma insunaso
sai suyimin magana prvt loz).
Bayan ta koya mata komai.
Tayi mata rakiya
har bakin kofa, nace Don Allah kiyi hakuri bai
bar min komai ba....gurin is not clear.
Tayi
dariya tace wallahi ya biya ni har da doriya, ni
ke da godiya Madam.
Naji dadin samunki mai
far'a da son jama'a wallahi domin hausawa
na cewa shimfidar fuska tafi ta tabarma.
Sorry
not clear.Amma gobe kizo da wuri don Allah
Na fada ina murmushi.
Insha Allah da wuri
zan zo yau ma akasi aka samu Na gode sai
goben.
Nace Allah ya nuna mana lafiya.
A
kujera na bar wayata na dauko ina latsawa na
ga an kira har sau goma sha uku (13 missed
calls).
Na fido ido, ina dubawa na ga Hameed
wato Yarima.
Na zauna tare da kura wa wayar
idanu saboda a gaskiya bana iya kiransa.
Na
latso lambar Inna, bugu daya ta shiga.
Tayi
sallama murya a washe.
Wa ke magana?
Inna
Humaira ce.
Sai naji tayi yar dariya.
Humaira
kuna lafiya?
Kalau Inna, su Aisha su iso lafiya?
Tace lafiya lau, ya suka barku?
Nace kalau.
To
Allah yayi muku albarka Kiyi mana godiya mai
tarin yawa wurin yarima don Allah.
Ya kira ni
dazun yace zasu yi tafiya , don haka ki kula da
kanki, ki kuma kular masa da gida Allah yayi
muku albarka.
Nace Ameen.
Mun dade muna
hira inda na lura Inna kamar ba cikin
damuwa, sannan muka yi sallam hankalina ya
kwanta.
Kamar abin jira, kiransa ya kara
shigowa.
Gabana ya fadi ba wai kiran ke bani
so ba, a'a tambayoyi na tsana a rayuwata.
Na
kara wayar a kunne tare da fadin.
Assalamu
alaikum.
Ya amsa cikin zakuwa tare da ci
gaba da fadin.
Ina kika shiga ne tun dazun ina
ta kira shiru, ni duk kin tada min hankali.
"Kicin" na bashi amsa.
Me ki ka yi a kicin da
zai dauke ki wannan lokacin Humaira?
Kinsan
kuwa yadda kika sa min damuwa?
" koyan
abinci".
Na kara fada.
Yayi ajiyar zuciya tare
da waji murmushi mai fidda sauti.