Sashe 5
Afnan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina xaune falo
ya dawo da qa2war leda.
"sorry humaira,
kadaici ya dame ki ko?".
Ya qaraso inda nake.
"wallahi 2n fitarmu ina kasuwa don samo miki
abin kore kadaici".
Yana maganar yana
bude ledar tare da fiddo littatafan hausa da
fina-finan hausa sabbi, masu kyau.
Dadi ya
kama ni, da ma in taba kara2n hausa ko a
gida, musamman littattafan jamila ibrahim
kankia, naja'atu haruna 'najnoor nasimat', da
kuma na xainab dahiru wauwo 'xeedee'.
Ya
miqo min littattafan kusan guda 20, a sama
wani sabon littafin mu2niyar ne, wato xeedee
wai shi 'INA XA MU JE?' daga jin sunan littafin
nasan dole ya yi dadi.
Na yi murmushi "na
gode qwarai".
"ga kuma hausa films xo in
koya miki hada kayan kallon yadda xa ki ringa
sauyawa daga DVD xuwa satelite wataqila ba
xa ki iya gane connection din ba duk da a
hade suke ko da remote sai ki sauya".
Nace
"to".
Tare da matsawa cikin doki da murna,
saboda gaskiya xaman kadaici ya ishe ni kam.
"abin ma ba wuya".
Na fada ina yar dariya.
Ya yi murmushi.
Gare
ki mai saurin fahimta ba......
Akwai sairan
abinci?
Wallahi yunwa nake ji.
Eh na dafa
wancan babu na ga ba ku rage komai ba.
Yauwa bari na watsa ruwa, hada min kafin na
fito Na shirya masa hadadden farfesun 'yan
ciki da fried taliya, sai kemon kuskus mai
madara da kwakwa a ciki.
Ya kwashi girkin
nan da kyau, da ma kadan na yi daidai ni da
shi, ya cinye nasa duka.
Na yi yar dariya tare
da kallon empty kwanonin da farantin, sai ya
kyalkyace da dariya.
Me kike son cewa?
Na
kwashe kawai na wuce kicin.
Ya ci gaba da
cewa.
Ko fiddo maganarki yarinya, so kike
kice ina da ci ko?
Kin manta garinku kenan
lokacin da kike ba ji abinci halan?
Daren ranar
mun yi hira da kallon wani fim na Hausa mai
ban dariya na dan Ibro.
Washegari kuwa
tunda ya fita da safe sai yamma ya dawo, sai
ga shi da uwar tsaraba kayan daddawa,
kuka,kubewa sauran tarkace wai in ji Inna.
Na
yi ta murna, tamkar Inna ce gabana.
Goma na
safen washegari ya bar gari da alkawarin bai
wuce sati daya ko biyu.
Nanji dadin tafiyarsa
saboda na sami damar sakewa in yi karatun
littattafan da ya sawo mini da fina finai.
Maimartaba ya bada kayan itatuwa kwando
kwando aka kawo tare da dumbin godiyar
dawainiyar da ake da shi.
Kullum idan Yarima
bai kirani sau hudu biyar ba, ya kira ni sau
uku karanci.
Kamar daga sama ranar wata
asabar, sai ga mahaifiyarsa da wasu barorinta
guda biyu.
Na ji dadin zuwanta sosai, saboda
itace wadda ta fara kawo m8n ziyara daga
bangarensa.
Na zubo mata abonci dankayan
makulashe, abin mamaki ta ci komai tana yi
tana mini nasihar na rike mijina, kuma na
dage da addu'a.
Da za ta tafi na zubo mata
dambun naman kaji cikin wata katuwar
samira, sannan na kunso mata snack na ba
daya daga cikin barorin na ce ta rike mata.
Ta
dinga yi min addu'a sannan ta tafi.
Kwanan
Yarima goma da tafiya ya yo mini waya ga shi
nan zai hau jirgi yau zai dawo.
Nan da nan na
fara shirye shiryen tarbarsa.
Ga mamakina har
kusan karfe biyun dare ban yi bacci ba ina
sauraron zuwansa, amma shiru!
Na kira
wayarsa sau wajen uku a kashe, hankalina yayi
matukar tashi.
Baccin da ban sami yinsa ba
kenan har garin Allah ya waye.
Da safen ma har kusan karfe sha biyu ba wani
labari.
Haka na ci gaba da aiki kamar wadda
kwai ya fashewa a ciki.
Ina cikin harhada
kayan abincin maimartaba na jiyo alamun
budewar kofa, da hanzari na fito.
Ya shigo a
hargitse kamar ba shi ba, gabana ya fadi,
kada dai ace maimartaba ya rasu?
Ya kamo
hannuna idanunsa jawur, muka zauna bisa
kujera.
Humaira tare muka zo da Zarina,
kuma yau maimartaba zai koma fada.
Na saki
ajiyar zuciya a hankali.
To mene ne abin
damuwar a nan?
Na fada a zuci.
Ya karkace
kai kamar mai shirin yin kuka, ya ci gaba da
cewa.
A dalilin kyautatawarki da abin da kike
aika masa tun zuwansa yanzu haka ya ce zai
zo a yi miki godiya, kuma har da Zarina yanzu
haka...
Na dafe kirji tare da zaro ido ina
shirin yin magana muka jiyo bugun kofa.
Da
sauri ya mike tare da lekawa, ya dawo da
gudu.
Wallahi su ne!
Take na ce Innalillahi
wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma laa sahlan
illa maa ja'aktahu salan, wa'anta tij'alik hazna
iza'shi'ta sahlan.
Na je na bude ina kara
karanta adduo'in neman sauki a kan duk wani
tsanani a zuciyata.
Su Umma ne a gaba kafin
wasu dattawan mata gudu biyu, sannan shi
maimartaba wasu manyan mutane hudu na
bin bayansa.
Sannan dogarawa, a bakin kofa
dogarawan suka tsaya.
Rakube nake jikin
oofa, ban da kyarma babu abin da nake yi
kaina kas.
Kutumar uba!
Aka biga wannan zagi
da karfi, a firgicr na dago kaina.
Ganin
Gimbiya na yi kusa da ni da alama ita ce
karshe wajen shigowa.
Munafuka!
Algunguma!!
Kowa yayi cirko cirko tare da kura mata ido,
amma ban da Umma da ta sami kujera ta yi
zamanta.
Da ma ke ce matar abokin Yarima
yar iska?
Makircin da kuka hada ke nan ke da
uwarki?
To wallahi ba ku isa ba, ina Yarima?
Na rantse da Allah yau sai ya sake ki.....
Ke
wai lafiyarki kalau kuwa Zarina?
Duk wannan
cin zarafin da kike wa yar mutane na mene
ne?
Shin ko kin san dalillin zuwanmu wurinta
kuwa?
Cikin dattawan matan nan daya ta
katse ta da fadin haka.
Ta hankado keyata na yi
taga taga zan fadi,
kawai na ga mutum ya tare ni na fada jikinsa.
Da sauri na kalle shi sai kawai muka ga
maimartaba ya zauna a duke.
Ganina jikin
Yarima ya kara harzuka Gimbiya, ta fara
zubda ruwan rashin mutunci ba tare da ta yi
la'akari da wadanda ke wurin ba, tana fada
wa dattawan kobji wace ce, saboda suna da
masaniya kan maimartaba ya haramta aurena
da Yarima ko bayan ransa.
Sau biyu tana
kawo harin za ta dake ni yana tarewa, ni kuwa
banda kuka babu abin da nake yi, saboda
tashin hankali.
Ni ba na Gimbiyar ya fi
damuna ba, irin hukuncin da maimartaba zai
yanke a kaina kawai na ke ji.
Wuri ya
harmutse, fada tsakanin Yarima da Gimbiya
su kuma dattawan wasu na goyon bayan
Gimbiya su kuma dattawan wasu na goyon
bayan Gimbiya, wasu na nuna cewa ba ta
kyauta ba ta yi rashin kunya sosai, tunda ta
aibanta Yarima gaban iyayensa.
Duk wannan
hargitsin su Momy da Maimartaba ba su ce
komai ba Ganin abin ya ki ci ya ki cinyewa yasa
maimartaba daka musu wata irin tsawa da
kowa da ya yi mamaki.
Nan da nan kowa ya
na'abba.
Wannan ai hauka ne!
Ya fada,
sannan ya ci gaba da cewa.
Ba ku da
bambanci da dabbobi, musamman kai.
Ya
nuna Yarima.
Gabana ya yi wani mummunan
faduwa, ya kira dansa DABBA ni kuma mai
zan koma.
A matsayinka na namiji yausha
zaka biye wa mace musamman lokacin da
kishi ya turniki zuciyarta?
To kowa ya zauna
zan yi magana biyu zuwa uku, amma kafin nan
zan fara da abin da ya kawo mu.
Ya kalli
Yarima, Ya sunanta?
Kansa duke ya ce,
Humaira.
Humaira zo daga nan.
Ya nuna min
kusa da shi daga kasa, tsoro ya kama ni
saboda na san kaina kawai zai sare da adda
shi ne sakamakona.
Ina kyarma na karasa har lokacin kukan nake.
Godiyar da na zo yi miki ba zan fasa ba.
Na
gode, Allah ya yi miki albarka.
Wane ne
mijinki kuma?.saboda har da wannan
tambayar na zo yi miki, domin kullum Yarima
ce min yake yi matar abokinsa.
Wayyo duniya!
Wayyo I
na!
Wani sab9n kuka ya zo na ji
kamar na zura a guje.
Ko ba kya iya magana?
Na ce wane ne mijinki?
Wane ne fa banda
Yarima.
Gimbiya ta fada a hasale daga inda ta
ke zaune.
Cikin tsananin bacin rai maimartaba
ya kalle ta..
Kada ki yarda na gane ba ki da
da'a domin za mu bata, batawa mai tsanani.
Ta zumburi baki ta kauda kai tana gunguni,
abinda ya ba wa kowa mamaki.
Ya kalle ni,
Humaira ko zan san wane ne mijinki?
Na dukar da kai ina wani irin kuka, da kyar na
iya furta.
YARIMA NE!
Amma don Allah ka yi
hakuri, wallahi ba laifina ba ne, ni ma ba da
son.......Dakata!
Bari kukan kada ki sarke.
Yanayin yadda ya fadi maganar cikin tausayi
ya sa ni da Yarima saurin kallon juna.
Ya mike
tsaye, sai kowa ma ya mike, ni ma dole na
mike saboda an bar ni ni kadai a zaune.
Sakamakon abin arzikin da kika yi kin na yafe
wa Yarima, kuma na aminta da aurenku ko
lahira wani yana cin arzikin wani, to shi ma ya
ci arzikinki, domin tunda ya yi auren farko ban
taba shan riwan gidansa ba sai a nan.
Sai ka
tattara matanka ka hada su wuri guda, shi zai
hada kan iyalanka.
Yana fadar haka ya yi
hanyar waje, saura kuma suka mara masa
baya.
Wani yayan Yarima ya banko mini harara
wacce ta sa dole na yi kasa da kaina.
Karaf!
A
kan idon Yarima, ashe hankalinsa na gurinmu
da ma.
Gimbiya ta fara zazzaga masifa, tana
fadar maganganu har tana ikirarin plan ne aka
shirya da ma don a ci mutuncinta.
Yan baya
suka ji abin da ta ke fada, amma shi
maimartaba tuni ya fice, har ya kai a mota.
Ta
yunkura tare da shako wuyana ta makare ni
jikin bango, Yarima ya taso lokacin har ta
kwada min abin fulawa ta fasa min goshi.
Da
kyara ya kwace ni tana faman dukana da
harbi, ni kuwa sai kuka nake.
Hayaniyarta ta
dawo da su Momy, da kyar suka fidda Zarina
gidan tana ta hauka.
Jikina sai rawa yake yi
saboda tsoro duk na firgice sai bari nake.
Da
kansa ya wanke min jinin ya sa auduga ya
daure da bandeji.