← Book details Afnan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 10

Sashe 4

Afnan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaisuwar tayi masa dadi a yadda na fahimta,
yace.

Alhamdulillahi da sauki wallahi, na je
ma gida amso masa karin kumallo ne.

Ina
dawowa na tarar har ya gama cin wani abinci
ta baiinsa mai dadin gaske, wai an kawao
masa daga gidan abokina shi ne nakr neman
wannan dan iskan in ji ko shi Abdul amma ba
wanda na samu.

Shiru na yi tare da mijewa na
kwashe kayan, ga mamaki ya cinye komai.

Ya
kalle ni yana murmushi.

Kr ni fa na lashe
abincin, kin dai ci naki ki?

Nayi yar dariya, Eh Dariya na baki?

Ya fada
cikin wata irin siga mai nuna matsanancin
farin ciki.

Ni dai na yi gaba abina in
murmushi.

Abin da na fara yi shine gyara kaza
na wanke na jajjaga dan tarugu da albasa
sannan na daka thyme da citta da tafarnuwa
na hade wuri guda na kawi mai na zuba ciki,
sannan na zuba maggi da gishiri na motse na
shafe kazar nan da su ciki da waje, na saka
gefe na dauko albasa davtumatir na yanka
fyalen fyalen, na yanka kabeji kanana na ajiye
gefe.

Na dauki kazar na sa a oven tare da
timing mintuna arba'in da biyar.

Na wanke
shinkafa da ma na dora ruwan zafi sun tafasa
na zuba, sannan na barta ta dan dahu, sannan
na sauke na wanke na tsane.

Na yanka wani
kabeji, karas, kokumba, koren wake da peas
na tafasa hanta na yankata kanana da yar
albasa.

Na zuba mai a tukunya kadan yana yin
zafi na juye vegetables dina da hanta sannan
na zuba zuwa kadan na kawo shinkafar na
zuba tare da motsawa, ruwan suka hau kanta
kadan yadda zan ida dafata na rufe.

Ina cikin
gyara kayan miya Yarima ya shigo ya sha
uban ado da irin kayansu na sarauta nan da
nan jikina ya dauki rawa na kasa ci gaba da
yankawa.

Ya matso tare da shishige min.

Me
kike dafawa haka gida ya rikice da kamshi??

Zaka fara ko?

Na fada a zuci, amma a fili na
ce Abinci.

Zan sami kamar na mutum hudu
zuwa biyar?

Insha Allah.

Na bashi amsa.

Ya
rungume ni very good my princess.

Zamu zo
around 2:30 mu ci , kaya na nan su za ki canja
kinji?

Nace To.

Duk na kagara ya tafi.

Ya kai
hancinsa a wuyana.

Inason wannan turaren
very sexy.

Na dai yi shiru saboda na riga na yi
mutuwar tsaye, ko me ye sexy kuma?

Na
tambayi kaina.

Gobe dani za ayi girkin nan
gaskiya, yau ma don am busy shi ya sa.

Ya
sake ni, sai mun zo cin abincin.

Yana fita na
saki wata ajiyar zuciya jikina gaba daya ya
bige da kamshi turarensa.

Da hanzari na kara
gyara wasu kajin uku tunda wankewa ce
kawai, akwai a firij na yi musu hadin ta farkon
na kunna dayan oven din nasa su a ciki.

Daidai
shinkafar ta dahu na kwashe a katuwar kula
kafin na gama na san ina zan zuzzuba.

Muna
da lemuka kala kala don haka ban wahalar da
kaina wajen hada wani juice ba gani har biyu
da mintuna biyar.

Na sami babban kwando
na zuba abinci na shirya wa maimaryaba
komai na ajiye gefe, sannan na je na shirya
wa su Yarima nasu a fako a kan table abin
mamaki naji ana buga kofa.

Na san ba Yarima ba ne sabida yana da
makulli, na hanzarta isa sai na ga wani dogari
da kwanonina, na bude ya durkusa.

Maimartaba ya ce a yi godiya sosai.

Na ce
yauwa tsaya ka tafi da wannan.

Na hanzarta
na dauko lemuka kansa na sanya masa kusan
kala takwas.

Na kwashi nawa na yi daki na
tarar ya ajiye min wata danyar shaddda galila
ta sha aiki sosai, na yo alwala na saka,
sannan na fara gabatar da sallah.

Ina
kabbarawa na ji motsin shigowarsu, wani
dadi ya baibaye ni.

Ya leko Au sallah kike yi?

Ya fice.

Koda na gama naci gaba da cin
abincina a tsanake tunda su ma na ji suna cin
nasu ne.

Na gama nayi lamo ina jin hirarsu
sai faman santi suke yi, sunabyi wa Yarima
sharri.

Wai da man don ya kwashi girki yasa
ya haukace kaina.

Na yafa gyalena na leka
muka gaisa, za su fara tsokanata nayi saurim
komawa ciki.

Muryar wani na ji yana cewa,
shege ina ka samo wannan shuwa arab din?

Dole Gimbiya ta haulace bala'in nan alkur'an
yarinyar tsoro ta bani......amma da ita zaka
tafi jibi ko?

Dadi ya ziyarce ni, ashe tafiya zai
yi jibi?

Ni dama gobe ko yau ne.

Baka jin
maganar Yarimaan saboda kasaita da jan
girma wannan mutumin akwai isa.

Yaushe ne
ta ke haihuwa Gimbiyar?

Ciki gare ta ashe?

Na fada a bayyanr.

Suka dai gama hirarsu ina
ji suna amarya mun gode amma na yi shiru.

Tunanina da shi aka fita sai kawai na ga
mutum ya shigo alkyabba a hannu.

Ya miko
min.

Ungo ki kai min daki.

Na mike na isa tare
da mika hannu sai kawai naji mutum ya
rungume ni.

Haba irin wannan delicious ai sai
da tukwicin hug.

Wallahi kwakwalwarki na ja,
na san
ko ita malamar taki da ta koya miki
girkin yanzu ba zata hada kanta da ke ba.

God bless u my princesss.

Ya sake ni, zan je
na amso wa maimartaba abinci, Umma har ta
kai ga yi min waya.

Nace to kawai.

Har ya
juya ya dawo Zo ki yi min rakiya.

Ya fizgo ni
muna zuwa bakin kofa ya mamayeni ya kai
bakinsa ga nawa, sannan ya saki ji tare da yi
min gwalo, sai kawai abin ya bani dariya
sosai.

Shi ma da dariyar ya bar gidan, na
gaya shiga wani farin ciki mara misaltuwa,
Yarima Hameed kenan.

Karfe shidda na
marece naji ana kwankwasa kofa, na hanzarta
tare da tambayar waye?

Yace kwanoni ne aka
kawo na abinci.

Na hanzarta budewa da man
da hijabi a jikina.

Kamar jiya ya risina.

Maimartaba yace, ayi masa godiya mai tarin
yawa, Allah ya albarkace ku ya azurtaku, ya
rufa muku asiru duniya da lahira.

Nayi
murmushi cike da jin dadin wadannan
addu'oin nace.

Amin ya rabbi.

Na karbi kayan
ina shirin juyawa gida, sai ga Yarima kamar
daga sama.

Gabana ya fadi jikina yayi sanyi,
ya kalli dan sakon da tuni ya zube kasa yana.

Allah ya taimaki Yarima!

Ya daure fuska, ya ya
dai?

Na maido wa matar abokinka kwanoni
ne, kuma maimartaba na dada godiya, Allah
ya bar aminci.

Tashi ka tafi.

Ya fada a
hanzarce.

Ni kuma nayi ciki da sauri.

Ya biyo
ni har kicin.

Dama Humaira ke ce ke aikawa
da abincin da maimartaba ke faman yabawa?

Ke ce matar abokina da yake faman fada wa
duk wanda ya ziyarce shi?

Waye ya baki
wannan shawarar?

"ba kya tsoron hakan xai iya
janyo a yi
saurin fahimtar tsakaninmu 2nda kin nemi
wannan kusancin har an san da ke?

Kin ji?".

Ba tare da na kalle shi ba, na ce.

"ka yi
haquri".

Ya matso kusa dani "ba laifi na ce kin
yi ba, shin kina ganin ba wata matsala ko ba
kiyi 2nani ba kafin ki yanke hukunci?" a qagare
na ce da shi "ba wata matsala in sha Allah".

"kin tabbata?" "eh".

Na fada ina shirin gifta
shi na fita.

Ya janyo ni jikinsa.

"Allah ya yi miki
albarka humaira".

Bai qara fita ba, ya ce muje
na taya shi harhada kayansa, sai wajen 9
muka gama, saboda mun yi sallar magariba
da isha'i sannan tambayoyi da yawan
maganarsa suka ringa bata mana lokaci.

"wai
humaira don Allah sai yaushe xaki saki jikinki
da nawa?" murmushi kawai na yi "kin san
shawarar da na ke yi yanxu?".

Na
ce "a'a".

Ya ce "so nake yi idan na dawo na
san yadda xan maida ki makaranta, ko ba ki
so?".

Na fadada murmushin kusan xuwa 'yar
dariya "wallahi ina so saboda ma 2ranci".

Ya
kalle ni sosai "2ranci kuma?".

"eh wallahi, ina
son iya 2ranci sosai".

Ya qyalqyale da dariya
"to ko london xan kai ki qasar 2rawan?".

Cikin
'yar dariya na ce "da ko ka kyauta".

Wasa-
wasa hira ta barke tsakaninmu, nan da nan ya
fahimci lallai ina son ilimi 2nda ga shi ina hira
da shi cikin sakin jiki, abin da ba taba ba.

Da
yake hirar ta yi min dadi ban damu da yadda
muka kwanta gado 1 ba, muna ci gaba da
hirar har sai da na lura da irin shige min da
ya yi tare da yadda salon maganarsa ke...
sauyawa nan da nan tsoro da kunya
suka kama ni, amma ina lokacin da na farga
na makaro, 2ni yarima ya kasa sarrafa kansa,
yana faman salo...

Ya rasa ta inda xai billo
min nayi shiru, ni kaina na san kukan ba wai
na ciwo ba ne, tsabar kunya ce ya sa na kasa
tsaida shi, saboda ina 2nanin ta inda xan
tashi, ga shi a dakin ya kasa ya tsare.

"don
Allah humaira ki yi haquri".

Kalmar da yake ta
nanatawa kenan 2n tashinsa.

Ganin ba wani
sauyi sai kawai ya dauke ni cak xuwa bandaki
ya hada min ruwan dumi da komai sannan ya
fito.

Na sami damar dago kaina daga qasa ina
raba idanu kamar wacce ta yi qarya.

Na ma
ba kaina dariya na samu na yi wanka amma
fitowar ta gagareni.

Sai na jiyo motsinsa can
bayan daki, ai ko na yi hanxarin fitowa.

Ga
mamakina ya gyara dakin tsaf!

Ya sauya xanin
gado sai qamshi ke tashi.

Ta taga na
hango shi yana shanya xanin gadon da ya
kware, wato wankewa ya yi.

Ina cikin saka
kaya ya shigo, ai ko na yi cikin wardrope din
sai kawai na ji yana dariya.

"xan je gurin
maimartaba, ki hada abincin da ni don sai
xuwa jibi xan wuce, na fasa tafia yau".

Gabana
ya fadi, ni kam na so ya tafi yau din kamar
yadda ya tsara.

Kamar kullum na hada abinci
kala-kala, na shirya masa nasa na aika wa
maimartaba sauran.

Na sallame shi sallah
kenan na ji shigowarsa da baqi.

Har suka
gama ban fita ba, shi ma bai shigo ba, da
suka tashi kuma suka fita tare.
Chapter 4 · 0% Book details