← Book details Afnan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 10

Sashe 1

Afnan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Subul da Baka 3 page 1
Posted by ANaM Dorayi on 05:11 PM, 21-May-15
Under: Subul da Baka
Inna ta yunkura ta shiga daki suku ma suka yi
hanyar waje,Ashe zaman tabarma ne nake ga
bai mata ba.A firgice ya shigo babu ko
sallama yana fadin inalillahi wa inailaihi
raji'un daga ni har inna maka mike tsaye cikin
firgici inna take tambayarsa lafiya ibrahim?

Sai
kawai ya durkushe kasa idanun sa jawur inna
ya aka yi haka! cikin rashin fahimtar inda ya
dosa tace da akayi me yace inna waye kuma
hameed.yarima ne hameed meya faru mutuwa
yayi?

A'a da ransa shine mijinki yanzu an
daura muku aure,inna ta dafe kirji wa!

Tirkashi
inalillahi wa inailahiraji'un Nayi saurin
karasawa kusa da ibrahim na
rushe da kuka ina fadin ka rufamin asiri kaje
kace kaine zabina zan iya jure ko wace wahala
amma banda ta gimbiya da mahaifin yarima
wayyo ni humaira na shiga uku !

Ke bana san
shashanci da hauka ina ma yazo kasar yaushe
yasan abinda ke faruwa.

Wannan abun yi Allah
ne saboda haka na
fawwala masa komai Allah yasa haka shi ya fi
alkairi a gare mu baki daya ya mike tsaye
yafita muna zaune muka jiyo sallama wa
yarima zai shigo kanshin turarensa ne yafara
yimin sallama.

Daga kurya nake cikin duhu,shi kuma ya zauna
daidai inda aka ajiye fitila na qura masa
ido,ya qara haske da qiba,yayi kyau har yau
kasaitar nan tasa na nan,sai faman basarwa
yake yi,yana 'yar yamutse fuska. takaici ya
qara kama ni na harareshi,nan ma SARAUTAR
zai nuna?

Cikin girmamawa ya gaida inna. tun
kafin yayi magana inna ta jero masa
tambayoyi."Haba yarima? don me zaka yanke
hukunci ba tare da shawararmu ba? talauci
haukane? yarinyar nan marainiya ce meyasa
zaka nemar mata tashin hankali fiye da
kwanciyarsa? ya zatayi da mahifinka? humaira
na iya kishi da Gimbiya?" Ya dago kai
fuskarsa a washe yace"Inna ku kwantar da
hankalinku,wallahi. billahi ba ni da niyyar cuta
ko yaudararku maganar mahaifina yanzu haka
yana kwance rai a hannun Allah kuma ina da
yaqinin insha Allahu zanyi amfani da wannan
damar mu daidaita dashi,tunda har yana
ganin ya hore ni da yin biyayya gareshi,kuma
na aikata hakan zan lallabashi ya yafemin,ya
janye maganar ko bayan ransa." Yanzu haka
ana zargin 'yan uwana ne suka jefa shi cikin
wannan halin,domin su gaji sarauta. akwai
rikici da muke ciki inna,amma hakan bazai
taba shafar Humaira ba da iznin Allah.

Kafin
inje ga maganar zamanta da Fareeda
(Gimbiya),ina son ki sani cewa,mahaifan
Humaira suna son ganin cewar sun
wulakantaku ko ince suna son ganin kun
wulakanta. dalili kuwa,nayi bincike sosai a
kansu. yanzu haka da muka je maganar
neman aure,ban nuna musu vewar ni din dan
sarauta bane,asali ma na kasance mai
qasqantar da kaina tare da nuna ni din talaka
ne mai neman taimako matuka.

Sunyi SUBUL
DA BAKA mai tarin yawa a cikin jawabansu a
inda suke nuni da lallai basu son Humaira ta
fi 'ya'yansu wadatar dace da miji mai rufin
asiri.

Maganar Ibrahim shima nayi bincike a
kansa
lallai mutumin kwarai ne kuma ya fito daga
gidan manya masu mutunci.

Matsalar matarsa
inda ake nuni da cewar,tafi karfinsa fiye da
tunanin kowa,yana tare da muguwar mata
wacce tana iya yin ko wane irin ta'addanci,da
mugun abu akan duk abin da ta ga zai kawo
mata cikas a rayuwa.

Wannan dalilin ya qara
tsorata ni,ga shi na ji hirarsu da Amira.

Kuma
da alama kamar Ibrahim din shi ne wanda
yake tsayayye a gareta.

Nazo don Allah mu
warware matsalar wallahi har ga Allah banzo
da niyyar auren Humaira ba,amma sai ta qi
saurarena wanda ya nuna min tamkar rike ta
ke dani a zuciyarta,tana ganin kamar nine sila
ta duk matsalarta.

Mahaifiyatace ta bani
shawarar nazo wurin magabatanta na kawo
kaina,ba tare da mun san cewar za'ayi
maganar daurin aure ba.

Munyi haka da
niyyar daga baya sai ta sami wani ta aura ni
kuma na janye.

Saboda haka kada muyiwa
Allah
shishshigi,hakan ya rubuta sai muyi fatan ya
zamo alkhairi agaremu inna.

Kada hankalinku
ya tashi,ni ke cikin rikici,amma duk da haka
bana cikin rudani.

Na farko yadda zan shawo
kan Maimartaba.

Na biyu rudanin da muke
ciki da 'yan uwana.

Na uku ya zanyi da
rigimar Gimbiya idan ta sani,bazan sanar da
ita ba sai na sasanta da mahaifina,in ba haka
ba tabbas zata raba mu har abada!" Na
runtse ido cikin radadi ina hango rayuwar da
zan shiga saboda na tabbatar auren Yarima
ba hutu bane a wurina.

"Maganar zamansu
da Gimbiya ba matsala bane,domin ni ke iko
da gidana duka qarqashina suke,wallahi inna
ba zan taba amincewa da takura,zalunci ko
tashin hankali a gidana ba." Ya tsagaita da
bayanin nasa kamar yadda dakin ya dauki
shiru.

Na kalli inna,sai naga tana zubar da
kwalla.

Hankalina ya qara tashi.

Ya muskuta
da fadin"Inna kuyi hakuri don Allah,gobe a
bada mata hudu zuwa shida wadanda zamu
tafi da su,domin su ga gidana hankalinki ya
kwanta.

Idan kuma zaki bi ke ma to mu tafi da
ke..." "Kai bana son sakarci!" Sai naga yayi
'yar dariyar nan tasa ta qasaita.

Ya mike
tsaye"Inna ayi ta hakuri,sai mun zo su shirya
gobe da wuri za mu wuce,wajen karfe takwas
zuwa tara domin mu isa da wuri,kada muyi
dare."
Tafiya muke yi, amman idanuna na gefen titi,
Sumayya da Aisha sai faman tsalle suke yi.

Motar su yarima ke gaba tamu na biye dasu,
Babban abinda ke damun zuciyata shine, idan
mun isa wace tarba za,ayi mana?

Ya za a
karbi wannan al'amari?

Ina tsoran tashin
hankalin Gimbiya, musamman idan mukayi
tozali da ita ga cewar na aure Yarima a
matsayina na na BAIWARTA.

Munyi tafiya mai
nisan gaske inda ake dauke hanya muka kutsa
cikin daji, nan ma munyi tafiya mai dan nisa
wanda su baba har sunfara korafi sannan
muka isa wani gidan gona katton gaske.

Acikin
gidan gonar ma sai da mukayi tafiya
mai nisan gaske kafin ya tssaya gaban wani
tankamemen gida, Goggo Huraira matar Baba
imrana kadai ta biyo daga bangaren babana,
itama ganin kwaf yakawo ta.

Mata hudu muka
tarar gidan, babu abinda babu na more
rayuwa a gidan, aka kaini wani daki mai
dauke da gado kawai sai mudubinsa, ga kuma
wata kofa a rufe wacce nake kyautata zatton
bandaki ne.

Abinci aka dinga shigowa dashi
kala kala cikin wasu manyan kololi, Goggo
huraira ta dinga raba idano tana yaken dayafi
kuka ciwo.

Hannu baka hannu kwarya suka
ringayi abinka
da sabon shiga ga farfesun kaji dana kifi, suna
gamawa wasu maza suka shigo da katon
gasasshen rago bisa wani dogon tebir, Goggo
Huraira tazare ido, bayan fitar su, takalli su
inna karsum wai wane ne wannan yaron?

YARIMA!!!

Nabata amsa takara fiddo ido tace
amma ku munafukai ne, shine baku fada tun
wuri ba?

Su goggo suka kalleta a mamakance
kamar zasuyi wani abu sai sukayi shiru, da
dare yarima yashigo yace ko akwai abinda
ake bukata?

Suka ce a a, dare yamika, gari
yayi tsit babu abinda akeji sai minsharin su
goggo ciki yacika da kayan dadi, nikuwa nayi
lamo ina tinanin yadda wannan aure nawa zai
kasance.

Washegari aka hado kalaci mai rai da lafiya,
abin takaici Gogggo ta cika ledoji wai za ta yi
guzuri su masu Inna ganin kayan kamar banza
sai da suka diba.

Karfe goma yarima yace su
fito ga wanda zai mayar dasu.

A falo muka
tarar da shi zaune Goggo ta wangale baki
tana fadin dan nan mun fa gode kaji.

Yayi yi
murmushi yace babu komai.

Ya mika wa
kowacce bandir din naira dubu dubu yace su
yi ysaraba a hanya sannan ya dora da fadin.

Akwai buhunhhunan shinkafa, masara, gero,
dawa, sukari, gishiri, kwalin taliya, kuskus,
mahamisa, sha'iy, madara.

Akwai kuma
maggi, jarkokin mai kowacce ta dauki biyu
biyu sauran a kai wa Inna kafin muzo, sakon
kudinta na ba direba idan kun isa shi zai ba
kowace kayanta.

Mun gode.

Su Sumayya ma
suka durkusa saboda kayan da ya basu.

Washegari aka hado kalaci mai rai da lafiya,
abin takaici Gogggo ta cika ledoji wai za ta yi
guzuri su masu Inna ganin kayan kamar banza
sai da suka diba.

Karfe goma yarima yace su
fito ga wanda zai mayar dasu.

A falo muka
tarar da shi zaune Goggo ta wangale baki
tana fadin dan nan mun fa gode kaji.

Yayi yi
murmushi yace babu komai.

Ya mika wa
kowacce bandir din naira dubu dubu yace su
yi ysaraba a hanya sannan ya dora da fadin.

Akwai buhunhhunan shinkafa, masara, gero,
dawa, sukari, gishiri, kwalin taliya, kuskus,
mahamisa, sha'iy, madara.

Akwai kuma
maggi, jarkokin mai kowacce ta dauki biyu
biyu sauran a kai wa Inna kafin muzo, sakon
kudinta na ba direba idan kun isa shi zai ba
kowace kayanta.

Mun gode.

Su Sumayya ma
suka durkusa saboda kayan da ya basu.

Gaba daya jikinsu ya dauki rawa suka zube
suna faman godiya.

Ni kuma da yake nasan
wannan kadan ne daga cikin aikin yarima abin
bai zamo mini sabo ba kamar su.

Na fashe da
kuka lokacin da na ga cewar, motarsu ta bada
wuta zasu tafi.

Goggo ta leko kai daga tagar
motar tace.

"To yar banza mai kashin tsiya
kukan me kuma kike yi?

Wanna aljannar
duniya da Allah ya kawo ki har kina da bakin
kuka, marar mutunci ko zaki yiwa Allah
butulci ne ya rabo ki daga tsiya.

Hannuna naji
an kama mun yi baya.

Da sauri na kalle shi,
Yarima ne fuskarsa a daure da alamar
maganganun sunyi masa zafi.

Ni kuwa banji
komai ba saboda na saba da wadanda ma
suka fi wadannan.

Bisa kujera muka zauna
yanayin zaman yasa nayi wata irin kunya ta
kama ni.

Na yunkura zan mike ya dawo dani
na fada saman jikinsa na rasa inda zan sanya
kaina don tsananin kunya.

Ya rike hannuna
duka biyun tare da tsare ni
da wannan mayen kallon nasa mai narkar da
duk illahirin jikina.

Inason furta ya sake ni
amma na kasa sai faman motsa baki nake yi
kalmomin sun gaza fita.

Yayi yar dariya yace
Ba fa zan sake ki ba sai kince I Love You
Naku Tabdijan!

Ashe zamu shekara a haka kenan!
Chapter 1 · 0% Book details