← Book details Afnan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 10

Sashe 8

Afnan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya karkatar da wuya wllh inna
bazaki gane ba amma bakomi ni yanzu ki
taimakamin da yar taki donAllah...

Kafin
inna tayi magana ninayi ina mike nace kayi
hakuri anyi min miji.

Ban jira wata mgn ba nayi waje cikin
fushi.ko zaure ban fita ba wayata ta dauki
kara kmr abin jira, alamun kira ne ya shigo.
sunn Ibrahim ne alamar shi ya kira, na lafe
bakin kofa sbd na tsani tfy ina waya kmr
wata sabon shiga.sllm nayi kafin ya amsa,
sai da yayi wata ajiyar zcy na yi dan
murmushi sbd inda sabo na saba da jin
hk.A hkl yake maganar kmr mai tsoron
furta kalmomin, "Humaira zcyta Zata fashe
kaunar ki ta hanani aiwatar da abinda na zo
yi, ki taimakeni na turo a daura mana aure
ckn satin nan a kawo min ke ko na sami
sukuni".ban San lkcn dana kyalkyace da dry
ba nima ckn zolaya na ce, "to na taimake
ka".

Ya yi murmushi mai fidda sauti wani
abu ya taso min wnd nake ji kullum idan na
kasance ina irin wnn hirar, na runtse ido
kawai.

Ya kara narkar da murya, "wlh da
gsk nake na takura mata nake so kusa
dani".Na bude idona ina jin alamar kwalla,
amma na daure na maida su tare da
kokarin kawar da damuwar da nake neman
shiga, na ce.

" Ibrahim ka zamo m
ai adalci,
shin mai zai hana ka tafi da matarka don
Allah ka yafe mata mana".

"Baza ki taba
gane abin da nake nufi ba ynz matata ta
wuce muguwa, wlh shaidaniyace, ke dai ki
dage da addu'a Allah ya tserar da ke daga
sharrinta".

Gaba daya jikina ya yi sanyi, gaba na
ya fadi, tsoro ya kama ni, amma sai ban
nuna masa hakan ba, sbd ina son jin tushen
mgnr.

Ina 'yar dariya nace.

" Nima abin ya
shafeni kenan?" "ku san haka, sbd wai ta ji
ana mgnr neman aure shi ne ta bugo mini
waya jiya da daddare cewar wlh sai ta gano
ko Wace ce, km sai ta kashe ta ko ta yi
sanadiyar nakasata kin ji muguwa".

Ckna ya
bada wani kululu.

Na zaro ido tare da dafe
kirji.

Ya yi murmushi, " kin san wnn ai
haukane, ni dai sai kawai na bi ta da karya
ne dona zauna Lfy.

Ibrahim da na daure na cije ba don
ina sonsa ba, kawai gudun bacin ran inna,
shi kuma ga Inda tashi matsalar take. shi
kansa yana tsoron sharri da tuggu na
matarsa ina ga ni karabiti? shin in fadawa
inna ko in yi shiru?

Fadar babu abinda zai
janyo mata sai tashin hkl da rashin
kwanciyar zcy. wayyo ni Humaira ga 'yan
uwan ubana sun tasoni a gaba, kr2 ma sun
hana mini sbd jin zafi da bakin ciki,
Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un. kai dole in
sanar da inna, domin itace mai yi mini
addu'ar da Allah zai amsa da gaggawa.

A kfr
gida na tarar da su tsaye kallo 1 nayi musu
na gane 1 daga cknsu shine muka hadu
wurin biya wa su Aisha kudin makaranta na
farkon zango
Ni sai da ma na ganshi na tuna ban kai kudi
an aka sanyo musu baje ba jikin uniform
din.

Da fara'ata na karasa sbd ban mance
taimakon da yayi mana ba, na cika mana
#30 sbd babu canji a lkcn, ya ce mu bari zai
bayar.

Har Kasa na durkusa don gaida su.

Ina murmushi nace, "Mun fa gode ".

Ya yi
murmushi, " wai ni har ynz gdyr nan bata
karewa?

"Na yi 'yar dariya kawai.

Abokin
yace ," Nan muka zo gurin musbahu tun
dazu muna nan unguwar sai ga kannenki
(su sumayya) za su tafi islamiya, abin
mamaki yaran nan suka ganeni. shi ne suka
gwada mini gidanku nace bari
"Eh wlh nan baya na je kai wani sako
".

Abokin yace, " to madallah, mu zamu
wuce sai wani lkcn ".

Na ce, " to nagode ".

Na wuce gida Ina kallo ya Kai masa duka da
harbi na yi kmr ban gani ba, na yi ciki
abina.

" wai lfy kika dade hk? ko lbrn ne
naku ya tashi ke da innar taki?

" Ta karasa
mgnr tana murmushi, na ce.

" Humm bari
inna na zauna tare da ba ta lbrn duk abinda
ya faru hr wayarmu da Ibrahim ". sai na ga
tana dry.Na bata fuska." to me zan yi?

"
"Duk ciki banga abin dry ba sai na kuka kika
gani?

" " wlh ba komai ke dai ki ci gaba da
addu'ar Allah ya warware mana, wlh nasa
Allah ma ji rokon bawansane, ba zai ki
amsar mu ba, wataran sai lbr, INA lkcn da
Zaki tuko zukekiyar mota ki zo kina alfahari
da mijinki".

Na yi murmushi, " waye inna?" " Allah
kadai ya sanshi".

Mafarkina suna nuna min
mijinki sai dai har yau banga fuskarsa ba, ni
na San..." sllmr su Baba Auwalu ne da wasu
dattawa guda 4.

Ckn ladabi na gaida su tare
da yunkurawa zan tashi ya dakatar da ni.

Inna ta mika musu tbrm 3 suka zauna, Baba
Auwalu zakakke shi ya fara mgn.Abu 1 ya
kawo mu nan mgnr Humaira gabana ya
fadi.

Wani ma'aikacinmu ne yaga Humaira
yana so shi ne ya turo abokansa su ji masa
mgn, to na fada musu gsky yrnyr ba ta aje
kanta nan ba mai kudi take so, ko dan
sarauta ko kuma likita mai kwasar albashi
da tsoka. wnd ta sami daurin gindi daga
uwarta aka maishe da iyayenta maza
banza.
ko da Allah ya azurta 'ya'yanmu da
auran masu kudi ba tallarsu mukai ba, sune
suka biyo su har gida, muna kora suna
likewa don hk nace gwara mu zo su ji daga
bakinku.

Tashin hnkl ba'a sa masa rana,
wnn cin mutunci da wulakancin ya isa.Na
kalli dattawan akalla kowanne zai yi 55-56
yrs wai abokinsu ne ke sona, Yaushe ya
ganni, km a Ina? wnn abu daga ji tsarine km
salon wulakanci da tozarta ne.

" ku nake
saurare shin akwai wnd kuka fidda mata ko
mu je a amshi sadakin wdnn?" Gabana ya
fadi, ni da inna muka yi kallon-kallo sai
kawai naji kwalla na bin kumatuna.

" Allah
kai ne gatana" Abinda kawai nake fada a
zcyta
Inna ta yi Kasa da murya, " Alh. akwai
wnd suka daidaita da shi ynz hk mu yake
saurare sbd hk a yi hkr za a turoshi".

Nan
da nan ya fusata, " kin ji ko? me na fada
muku? ku tashi mu tafi idan sun san wata
ai basu san wata ba".Ya kalli baba jamilu, "
ka zama shaida mun baku nan da kwana 7
idan babu wnd yazo, to wlh mlm Datti zan
bawa".

Ya kalli dattawan, " ku ce masa ya
zauna ckn shiri don baza mu yrd a yi mana
abin fada a dangin ba, duk take-takenta ta
lalata mana 'ya".

Idan da sabo mun saba da jin wnn klm
dk muka yi shiru ni da inna. suka bar gidan
ckn korafe-korafe, shin me muka tsare wa
su Baba? wnn amsa har yau na Kasa
samunta.

Hnkln ya tashi na dinga risgar
kuka shin wa zan fiddo ni Humaira?

Abinda
kawai nake nanatawa kenan, inna dai tayi
shiru abinta.

Zaune nake bakin kofa ruwan
koko kawai ke cikina, sai 'yar madarar da
na sanya masa gaba daya na rasa inda ke yi
mini dadi.

Ni kadai ce a gidan inna ta tafi
gadon kaya barka, Sumayya kuma sun tafi
mkrnta.

Hnkln ba kwance yake ba domin bani
da tudun dafawa, Ibrahim ne hnnna km ynz
ba na ko san jin mai sunan, dama a dosane
muke gashi km ya billo da matsalar
muguwar matarshi har abin na niyar
shafata.

Ya zan yi?

Ban sami amsar tmbyr
ba wayata ta yi kara, shi din dai ne naji kmr
kar na dauka.

Yau ma kmr Klum ya fara
rokona da hr zan ki fada masa, amma sai na
ga 'kara na sanar da shi wata kila shi yana
da dabara tunda inna tayi shiru tun jiya
bata ce min kala ba.

Na kwantar da murya
abinka ga Wacce ta sha kuka, ta kara
raunana.

Na kira sunansa, gaba daya naji ya
kidime sbd ban taba ba.

Ina saurarenki
Gimbiya ".

Ya fada ckn zumudi.

Na had iya wasu hawaye da ke shirin zubo
mini na fara mgn a hnkl.

" A gsky ina cikin
matsanancin tashin hnkl, iyayena sun tasoni
a gaba akan yin aure shi yasa aka
tsaidamini kr2.

Yau ya zo mini da tsoho
cewar ya bani 7 days na turo wnd zan aura,
ko ya aura mini shi, to a gsky Ibrahim a ynz
Ina tunanin auren tsohon, domin ba zan
boye maka ba, a gsky ban taba jin sonka a
raina ba, amma ina tausayinka tare da bin
umarnin mahaifiyata don faranta mata rai,
wnd har na fara jinka a raina.

To sai da da
mgnrmu ta jiya tasa na hkr da ki, sbd tsara
da raina, da kuma lfy ta.A gsky kmr ydd
kake jin tsoron sharrin matarka nima hk
nake tsoro.
sbd hk ni dai ga ni ga Allah, sai na fashe da
kuka a hnkl.

Iyakar tashin hnkl shima ya
shiga, ya rude."saurara Humaira, dan Allah
kiyi hkr, saurare ni mana".

Na dan tsagaita,
"wlh.. wlh Humaira babu abinda zai same ki
ynz hk sbd ke nake neman aiki nan kasar,
wlh ba zan zauna da ke ba a Nigeriar
ballantana ma wani abu ya faru, amma ki
kwantar da hnklki, na rantse da Allah
Humaira duk na fadawa dangi da iyaye don
a yiwa tufkar hanci. kin san kuwa bazan ta
gifta raina akan kry ba don Allah ki taimaka
mini".

Na dan ji sanyi, amma duk da haka
na ce.

"To shikenan ba komai ke nan zamu yi mgn
zuwa jibi idan mun gama shawara da inna ".

Ya ce, " Ba matsala ".

Ya dinga lallashina
yana ba ni 'yar dry snn muka yi sallama.

Har lkcn dai kaina bai warware ba yana
daure ckn rudani na yi shiru.

Rayuwa mai
daci, wayyo maraici yau da mahaifina yana
da rai, wa zaiyi min wnn musgunawar?
Chapter 8 · 0% Book details