← Book details Afnan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 10

Sashe 6

Afnan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai
maganar bata wani dame ni ba idan Allah
ya nufe ni da ilimin bokon nan na tabbatar
da kudin da ya bamu zasu ishe mu har
zuwa wani lokaci ko da bamu sanaa balle
ma muna awara ga cek bayan sati 2 na
dayaye dr ibrahim yaci gaba da zuwa kusan
kullun kwatsam rannan yazo ya ce zai tafi
karo karatu an tura shi singapore kuma
shekaru 4 zai yi inna ta nisa ta ce to Allah
ya tabbatar da alkhairi amin ya fidda
sabuwan waya mai kyau da tsada ya bani
yace inna ga wannan zamu rinka gaisawa
kusan kullun don Allah tace to bata angode
kawai raina ya baci watau ya tabbata inna
bata son tunda kiri kiri ta hana ya bani
waya ya miko mani dalleliyar blackberry
sabuwa dal na amsa fuskata babu yabo ba
fallasa, Inna ta hararoni nayi kmr ban gani
ba yana fiata ta jefoni da murfin kwano zaki
bishi kuyi bankwana ko kuwa?

Na mike
idanuna cike da kwalla na bishi yana tsaye
jikin katanga ya hada kaida bango mostina
kawai yaji da alama ni din yake bukatar gani
yayi saurin dagowa idanunsa sun dan yi ja
abnd ban taba gani ba nayi saurin kauda
kaina sbd wani abu da naji yana bakuntar
zuciata ya dubeni yace humaira zan tafi
amma bakin cikina bansami wata
kwakkwarar amsa daga wurinki ba.

Jikina
yayi sanyi zuciata tayi kunci haka kawai
nakasa fahimtar abnd ke damuna.

Ya kara
kwantar da murya na kasance ma'abocin
son zama da mace kwaya 1 a rayuwata
amma burina ya rushe lokacin da nayi
katari da matar da muka sami babbancin
akida.

Wllh humaira ba don ina kaunarki
nake kushe matata ba na rantse miki
banajin dadinta ko alama.

Kadan daga cikin
abnd tayi min kuma shine mafi karanci data
mari mahaifiyata agabana......

Da sauri na
kalleshi yayi murmushi irin na takaici yace
kuma ta hanani na saketa, ki taimakeni ki
sanar dani matsayina a wurinki wllh
humaira bazan taba wulakantaki ba magnrki
taje ko ina a danginmu mamana kullum sai
tayi zancenki babana kuma ya rasu.

Kuma
nayi promise bazan hadaku gida 1 ko
unguwa 1 ba believe me humaira pls.

Tunani yazo min idan nayiwa ibrhm
wulakanci koban amsa masa ba banyiwa
kaina ba kuwa?

Wa nake jira wa kuma nake
dashi a
hannu?

Idan har abnd yake fada gsky ne ai
nayi dace amma matsalr nayita jira har
4yrs?

Kamr ya karanci zuciata naji yace kada
kiji nace 4yrs ki dauka ko zaki ta zaman
zuwana ne a'a ISA duk year zan dinga zuwa
inaso ki tabbtr min da mgnta ne ni kuma a
yau din nan zan gabatar da maganata zan
bar komai in yaso da nazo hutu ayi biki idan
da hali mu tafi tare if nt saina barwa broda
na komai daga baya sai ki bini idan kuma
kina ganin akwai matsala donAllah ki sanar
dani.

Nayi shiru ina nazari shin idan nace
baiyi min ba wa zai min a dunia?

Ko haka
zan zauna ba wan ba kanin?

Kirjina yayi min
nauyi idanuna suka ciko da kwalla har
yaushe zan manta da yarima a rayuwata?

Ko in baki tym muyi magana a waya?

Nayi
saurin daga kai na alamar eh.

Yayi
murmushi to shikenn sai munyi magana.

Na daure nace Allah ya kiyaye ya bada sa'a.

Yanayinsa ya nuna min yaji dadi nagode
humaira thank U so much for ur prayers, na
yi murmushi na juya na shiga gida.

Ko zama
banyi ba inna ta hau fada wllh humaira
banajin dadin halayenki da kika tsira har
yaushe zaki daina tunanin yarima a
rayuwarki?

Wllh inna ni.....

Zaki kaffara don
kin isa yinta kibar rantsuawa.

Wannan
kunge-kungen da kikeyiwa wann bawan
Allahn na menene?

Kwata kwata kin daina sauraron kowa,
wallahi kiyi nesa da kanki, iyayenki sun
hanaki karatu saboda wata manufa tasu
daban, shin auren kuma sai kihana kanki
wanda shine mutumcin kowace ya mace?

Humaira asirinmu kike son tonawa?

Kin
mance abinda mahaifinki ya fada akan
soyayyarku?

Gabana ya fadi saboda yanayin
yadda naji inna tayi maganar kamar zatayi
kuka.

Kinyi dai dai, kuma Allah yabaki sa'ar
kin sauraron ibrahim, yaron arziki bna ki
tunanin Allah ne yakawo miki madadin....?

Tunda shima gwargwado yanada kyawunsa?

Ilimin nan yana dashi, sannan ga arzikinsa
na rufin asiri?

Anya ba maganar mutane
bane Humaira kwadayi ke fizgarki ba?

Haba
inna.....

Rufe mini baki mara kunya to me
kike nufi in ba kwadayin SARAUTA ba?

Ga
babanki Auwalu can yadauki alwashin sai ya
cusa mana bakin ciki ni da ke, bansan
abinda yake nufi ba, yana korafin jin zafin
yayansa na auren masu kudi, shiyasa kike
wannan sakarcin, to yasan maganinmu.

Ko
dan wannan ma bakya yiwa kanki fada ba?

Kiyi fatan Allah ya baki nagari mai kaunarki
da danginki..

Ta kawar da fuska amma ba
komai kije kiyi abinda kika ga dama..

Na
sauko kasa, Inna kiyi hakuri, in sha Allah
zan sanar da Ibrahim cewa na amince da
shi...

Da sauri ta kalleni to shikenan ya
wuce Allah yamana jagora nace amin...

Kwalla suka zubo min narasa na menene ni
kuma haka Allah ya taaro mini rayuwa??

Baniga karaty baniga aure tunda shi
Ibrahim......koda yake yace idan nayarda
zai dawo a yi biki.

Sallamar yaro muka ji
inna tace ya shigo.

Wai humaira ta zo
anbugo mata waya daga kasar waje Ina jin haka
na miqe zumbur na . gane
ameera ce.

Ya miqo man lokacin da muka
isa nida aisha.

Na koma gefen shagon
kusada bedi na kanga a kunne 'Hello' amira
kun isa lafia?

Lafia qalau, baki lafia ne naji
muranki kamar kinyi kuka?

Na girgiza kaina
kamar tana kallona, lafiata lau ina fama da
mura ne.

Nima kuwa nayi waya.

Don Allah?

Ta fada tana murna.

Walhi kuwa zan sanya
a turo maki lambar se mu dinga magana da
tawa.

Yauwa to yayi kyau nagode.nace
nima nagode qawata se na kiraki.

Haba
yaya me ya hanaka qarasawa gdan?

Yayi
murmushi hakanan.

Na miqa masa wayata
turamata lambata nima ka sakaman tata.

Yace to humaira manya wannan irin babbar
waya?

Nayi murmushi 'Ni don Allah gobema
idan kanada lokaci zan zo gdan kadan
gwagwada mani yadda take kasan sabon
shiga, kuma ka turamani qur'ani da adu'o'i.

Yayi dariya yayi ustaziya karfe nawa zaki
shgo?

Lokacin da kake nan, ni gobe ba inda
zan je.

Nace to zan shgo wajan goma zuwa
sha daya.

Muna bin hanya zamu koma gda
wayar ta hau kuka nayi saurin latsawa na
dauka a tunanina amira ce dan ko suna ban
duba ba Assalamu Alaikun kinga lambar ta
shigo?

Yayi murmushi wacece har an fara
rabawa qawaye lamba?

Nayi jim, to me
tafiya ne ya bugo yace maki gashi a cikin
jirgi, nace au walhi ban duba bane kayi
hakuri, Allah ya saukeku lafia.

Amin ya Allah
humaira zan kiraki idan na sauka.

Na bawa
qanena lambarki duk sati zaya dinga sako
maki kati kinji?

Ban san lokacin da nace
haba harda wahala kuma?

Yayi murmushi 'a
wurinki yake wahala' hmmm to na gode.

Zan kashe wayata sena kiraki idan mun
sauka.

Nace to masha Allah.

Dai dai lokacin
da muka isa dak, 'keda wa kuma ko kin
turamata lambar ne?

Nace a'a ibrahm ne
tayi murmushi yayi kyau, nayi yar daria 'kai
inna na lura kina cikin gwamnatin mutumin
nan.

Ai dole humaira yaron daya so naka ba
don wani abu ba sbd Allah kuma dangi da
yan'uwansa basu nuna kyama ba dole a
soshi Kema harda yarinta ke damunki
bazaki abnd nake nufi ba sai nan gaba.

Bakina yayi SUBUL DA BAKA nace ina fa?

Inna gurin shi daban yake a zuciata wanda
yayi sanadiyar rabuwata da ciwona ai
alhairnsa bazai gushe ba a zuciyata.

Cikin
raina nace kema kenan inna ni kuma nace
me?

Wanda ya cusa min soyayyarsa da
karfin tsiya ba tare dana farga ba.

Wayyo
Allah wayyo sarki ya samu cikin damuwa.

Na maida kwallar data zubo min. **
N9,035 muka kirga cinikinmu na awara na
yau inna ta kalleni tana yar dariyar jin dadi.

Kai Alhmdllh humaira mungode Allah ya
taimaki yarima ya rufa masa asiri shine silar
wannan rufin asirin da muke samu.

Nayi
murmushi inna kullum sai kin min fadan na
manta dashi gashi ke har yau kinsa
mantawa dashi shin kin kasa mantawa
dashi inna yaushe nima zai gushe a raina?

Ni kuwa kinsan shawarar dana yanke mana?

Nace a'a tare da smiling don na kula zancen
nawa zata kawar.

Kinga muna da yan
kudinmu na sana'a da wadanda ke ajiye me
zai hana musa a gina mana daki babba daga
can gurin tukwanen ruwan can mu koma
wann kuma ya koma kicin sbd damuna?

Na
buga tsalle kwarai inna kin kawo shawara
amma a gina mana ciki da falo yafi sirri.

Ai kudi
na keji humai, inna In
Shaa Allah zasu isa har ayi rara dayawa.

To
shikenan dama inaso mu fara siyan kayan
aurenki d an gama kada muji kunya ISA
inna bazamu taba jin kunya ba Allah daiya
kara rufa mana asiri tace amin.

Kullum
adduarmu kenan kuma Alhmdllh muna
ganin budi.

Babansu amira inna taba kudin
siminti da yashi washe gari aka fara aikin
da misalin 1pm nakaiwa masu ginin abnc
kenan mukaji sallama kallo daya nayi mata
nagane ta jikina ya mutu murus wani
yanayi ya dawo min sabo.

Tunda ta shigo
idonta yake kaina da sauri na nufi daki inna
mun shiga 3 ga innar......

Tsaye tabarni tayi
waje da gudu cikin rudu, mashaa Allah jiki
yayi kyau, ta fada tana murmushi.

Inna tayi
ajiyr hrt ta karasa tana yar dariya tace
maraba lale sannunku da zuwa.

Na fito
daga dakin bayan sun zauna narakasa na
gaidasu kaina kasa.

Humaira ya jikinku ya
bayan kwana 2?

Nace ya warware Alhmdllh
ina sunkuye da kai kasa.

Na mike ina
kokarin kawo musu ruwa da abnc tace
zauna humaira ina zakije?

Kaina kasa naceabnc
zan kawo muku da ruwa, tayi yardariya tace
Allah sarki wllh a koshemuke mungode
Allah ya bada ladarniyya.

Kowa na dakin
yace ameen, nakoma na zauna kamr yanda
ta bukata.Hameed ya turoni yace inji lfy kia
barkaratun?
Chapter 6 · 0% Book details