← Book details Afnan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 10

Sashe 4

Afnan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kauda kai
tace Allah ya kaimu suka amsa ameen.

Mama ta mike zan bar mace 2 ta dinga kula
daku zuwa sanda za'a sallameku zasu dinga
siyo muku abnci da duk abnda kuke bukata,
ta dora bandiran kudi akan gadon inna ga
wann ko zaku bukaci wani abu, Allah ya
bada lfy
Har ta fito bai motsa ba Inna ta kalleshi
tace tashi ka bita Allah ya bada sa'a.

Saura
kadan kwalla ta zubo masa ya kalleta yace
inna banida lfy zuciyata na min zafi ga
humaira tana fushi dani bata kaunar kallona
tun jiya bata min maggana.

Ya kara
langwabar da kai inna laifi na ne?

Cikin
tausayawa tare da mmkin soyayyarr da
yake min tace ba laifinka bane humaira
kuma kada ka damu wann halinta ne nima
tana min irin wann.

Yace inna in bata
waya?

Tace a'a bazan taba amincewa ka
bata waya ba kayi hkri kamr yanda nasha
fada maka to yau ma kalmae ce.

Ya sauka
kasa ya durkusa.

DonAllah inna ki taimakeni
kinga gobe
nisa zanyi daku.

Tace kayi hkri wann
sharadin mahaifinta ne idan ka aureta saika
bata.

Jin wann batun yasa ya mike kamr
me koyon tfy haka yabar dakin.

Wani
dunkulallen abu ya tokare min wuyana shi
bai wuce ba shi ba fito ba na runtse ido a
cikin raina ina fadin Innalillahi
wa'innalihirraji'uan.

Motsin su Aisha yasa
na bude idona na dauka ko shine ya dawo
da sauri na maidasu na rufe ruf a yau na
tabbatar yayi min nisa.

Anya zai dawo
gareni?

Na dafe kaina cikin ikon Allah sai
kwalla suka zuraromin makar famfo inna ta
kauda kanta.
na fara
rokon Allah ya cire min tunanin yarima
kuma Alhmdllh na fara ragewa sosai.

Da
marece bayan mun gama awara ina zaune
inna taje gidan kawu auwalu su Aisha sunje
islamiyya kamr daga sama naji sallamar
amira da gudu na tarota muka rike juna
cike da murna na kalleta a lokacn data
zauna
Inna bata fada miki inata zuwa ban
iskeki ba?

Ta dan bata fuska wllh humaira
inajin sakonki matsalar bana zama kullum
nayi dariya sannu agogo.

Ta kai min duka
na kauce ta mike dama lbr nazo na baki
sannan nayi miki albishir kiyi min murnar
abnd ya sameni safiyar nan kuma muyi
bankwana amma tunda.......

Haba kawata
yi hkr, da kinjawa kanki yarnya ta kara
gyara zama humaira yanayi miki wani irin
so wanda bazan iya fassara shi ba domin
abnd ya faru lokcn da za'a tafi da gimbiya
motar mu daban amma ni ya hanani nabi
cikinsi ya sanyani a motarsu.

Nida shi ne a
baya tunda muka tafi kansa yake a duke har
muka bar garin nan zuwa can ya dago ido
jajur don saida na tsorata.

Inason kawarki
amma son bayada amfani gareni.

Na
sunkuyar da kaina kawai ina wasa da
yatsuna wanda ke tukin motar ya juyo
kaidai akwai dan iska yaushe muna kan
layin raka matarka gida amma kana zancen
wata?

Shiru yayi kamr bada shi yake ba
kinsna miskilancin mutumin naki.

Yaja
guntun tsaki daga nan bai kara mgn ba har
muka isa.

Humaira naje karshen mulki a
sarauta naga inda ake takama da sarauta
ashe su gimbiya basu iya komai ba?

Motarmu na tsayawa wasu gardawan sarki
suka zo wani ya kwanta saman shi ya sauka
biyun kuma sukayi sama dashi bisa wani
dan gaka suka daukeshi sukayi ciki dashi
daga nan ban kara ganinshi ba sai washe
gari.

Kwana akayi shagali washe gari da
misalin 12 akazo nemana na gane hakan ta
yadda akayi kwatancen wacce suka shigo
mota 1 da yarima cikina ya dinga kadawa
sbd tsoro kada ace ko cigiya sukeyi.

Munyi
tafiya sosai kafin muje inda suke ya nuna
wata kofa ki shiga ba tare da bata tym ba
na shiga mazane shakare a falon duk
gimansa sun cikashi na duba amma nakasa
gane kowa a cikinsu da alama basu damu
da shigowata ba.

Keni sai tsoro ya kamani
nayi saurin juyawa kamar daga sama naji ya
kira sunana ashe yana kishingide cikin
kujera yana kallona Hmmm miskilanci da
kasaitarsa yana ba mutane tsoro, a tsorace
na karasa inda yake ko kallona bayyi ba ya
miko min wata rantsattsiyar wayarsa, ungo
kisamin lamabr da kike gani zan iya magana
da kawarki nakasa karba sbd kinga banida
lamabar kowa a kaina wllh kota sadan
gidanmu ban rike ba.

Murya na rawa nace
wllh banida lambar kowa akaina Allah ya
taimakeka.

Kallon da yayi min na rantse saida
guntun fitsari ya zubo min idanunsa sukayi
wani irin ja har wani ruwa ruwa ya kwanta.

Tunda ya dauke kao bai sake kallon inda
nake ba saida na kusan 1hr a haka nagaji
iyakar gajiya har kafafuna sukayi sanyi,
dogarawan dake tsaye suna masa firfita sai
kallona suke na raina kaina a wurin ranar
naji na tsani abotarmu dake.

Da Allah ya
taimakeni saiga wani abokinsa ya kalleni
yace wann fa?

Naga bakuwar fuska, ya
kalleni da wann yatsinar tasa yace ki tafi
mana.

Simi-simi nabar gun kamar na bude
kasa na shige don kunya.

Bansan wace
amsa ya bashi ba.

An gama shagulgula
amarya ta tare a gidanta wann sashe daya
kirani gida yasha kayan kwalliya dukiya
tasha kuka.

Abnd ya bani mmk har yanzu
basu bar al'adar nuna kwanan amarya ba.

Sbd washe gari gida ya rude da gimbiya
bata cika budurwa ba
Abun kunyar gimbiya ya nemi komawa
fitina da tashin hnkl.

Ga yarima an nemeshi
an rasa tun safe gimbiya ko sai kuka take
sharbawa kamr ranta zai fita tana rantsuwa
tana sharbewa wai bai kwanta aure da ita
ba.

Magana har gaban sarki gida ya sake
rudewa duk inda ake zatonsa an aika amma
ba'a tadda shi ba, hnkln gimbiya ya kara
tashi mai martaba ya kara fusata ita kuwa
mahaifiyarsa ko gezau saima fada data
kamayi ita bata ga amfanin auren dole ba
shin tunda yace bayaso bayaso a kyaleshi ya
auri wacce yakeso mana.

Aiko magana ta
komawa sarki, ta kalleni Humaira munga
tashin hnkl bana fatan sake ganin fushin
babba idan haka yake.

Maganar na zuwa
wajen sarki kuma sai aka sami wayar sarki
yace duk inda yake wllh ya bashi 3mins ya
gurfana agabansa sannan ya aika aka kira
sauran matan gidan
cikin yan dakikai falon me martaba ya
cika da ahalin gidan gimbiya na tsakiya har
lokacn bata daina kuka ba zuwansa kawai
ake jira.

Shigowarsa ke da wuya ga mmkin
kowa sai mai martaba ya mike ya dinga
kwada masa mari har sau uku hancinsa
kuwa ya balle da jini amma wllh ko gezau
baiyi ba.

Ni zaka kawowa raini?

Ni zaka
tozarta ka kunyata a idon dunia?

Ka kwanta
da matarka ko kuwa?

Jinin dake zuba a
hancinsa har ya fara bata gaban rigarsa fara,
ya sunkuyar da kai a'a ban kwanta da ita
ba.

Ya fusata kayi hakane don ka nuna ban
isa dakai ba?

Ya kalli jakadiya saikije ki fada
mutane yarinya bata kwanta aure ba Allah
kuma zai saka mata bacin sunan dakayi
mata.
idan kuma nina haifeka wllh babu kai ba
talaka komai ya dawo kunnena yau kuma
na tabbtr da daurin gindin daka samu daga
uwarka.

Duk ranar da naji baka rabu da ita
ba to wllh na yafeka dunia da lahira
shashasha sakarai!

Wann furucin na sarki ya
haifar da zazzafar tsana da kiyayya tsakanin
gimbiya da mahaifiyar yarima shima cin
zarafin da akayi masa gaban jamaa ya kara
sashi jin tsanarta fiye da baya.

Sarki yayi
musu kaca-kaca shida mahaifiyar sbd ina
zargin ita ke goya masa baya.

Sann yace da
gimbiya dataga wani abu wanda baiyi daidai
da tsarinta ba ta sanar dashi zaiyi maganin
abun cikin gaggawa.

Ana barin fada yaje ya
zuba kankana akan habon jinin ya tsaya
muna harabar gidan mukaji karar gimbiya
sau daya.

Muka razana kar dai ace shaketa
yayi muka nemi shiga amma ya kulle kofar
Ganin ya kullo kofar tsoro ya
kamamu don munga shigarsa cikin tsananin
fushi, karima ta kalleni gsky amira guduwa
zanyi bana iya wan bala'in da
gimbiya...uhm uhm wllh duk abnd yayi
mata ita taja auren nan hadin iyayene, tun
farko ya nuna mata bayaso shin idan ita mai
wayo ce basaita lallabashi ba?

Ga rashin so
ga izgilanci da tsageranci mekike tunanin
zai haifar?

Kinga kuwa abnd tayiwa
mahaifiyar humaira da ita kanta humairan?

Wllh na tabbt gimbiya zata iyakisan kai,
amma ke bakiga yanda ya shiga da fushi
ba?

Shin koma menene aiya riga ya faru ko
kina iya balle kofar ki shiga?

Ko dukansa
yake kofa bude kina iya karbar gimbiya
hannunsa ne? (Wannan rawar kan sai SIYYA)
to wai humaira na sonsa da gaske?

Kwarai
saidai tsoro ya rinjayi son shiyasa ba kowa
ke ganewa ba amma wllh humaira na sonsa
matuka.

Nayi saurin kai mata duka ni nace
miki ina son sa?

Kai-kai-kai ni kika doka?

Baki sonsa kenan?

To bari na tafi gida dama
na dauka kina sonsa shiyasa na tsaya bata
tym dina ina baki lbrnsa.

Na marairaice yi
hkri kawata dan karasa min wasa nake miki
sorry, kina sonsa?

Sosai ni kuwa ke sonsa
zauna ki karsa min dukanta yayi?

Wace irin
fitina ce ya kara janyowa kansa?

Na
fakaiceta na mata gwalo, ta zauna idanunta
sunyi ja kwalla ta taro mata taci gaba d
acewa muna cikin wann magana humaira
sai gashi ya fito ya sha kananan kaya yana
ta uban kamshi hhar tym din acikin fushi
yake.

Dogarai suka rufa masa baya yayi
hanyar shakatawa.

Yana bacewa mukayi
hanyar daki dake kallon nasa muna jiyo
gunjin kukanta.

A hamzarce muka nufeshi
kwallan da take kokarin maidawa suka zubo
gabana ya fadi na kosa naji abnd yayi mata
ta kalleni kwallar na zuba wllh humaira duk
irin isgilancinta saida ta bani tausayi,
kwance take bisa gado yarima yayi mata
kaca- kaca jini duk ya bata zanin gadon
(wayyo Allah yarima ashe dai mugu ne kai?)
Kukanta kawai kakeji har muryarta ta dashe
amma bata iya ko motsawa hannu karima
ta dora aka ta kurma ihu ni kuma na hau
kyarma kukan yaki zuwa min hnklina ya
bala'in tashi don ko a lbri wllh ban taba jin
irin haka ba da gudu na fita zuwa sashen
mama na sanar da ita abnd yake faruwa.
Chapter 4 · 0% Book details