← Book details Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 28

Sashe 19

Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda suka shiga har alokacin Baba be farkaba sun iske Sa'a ta'iso, *SEERAJ* yace yauwa sa'ade aikinki yayi kyau ta gaida shi ya'amsa tareda cewa Ina Hajiya Inna wuro rigimanmiya?..tace tana gaida kai wai yaushe kazo?..yace jiya kice mata ina nan zuwa anjima,tace toh" ni zan tafi yace OK" Sa'ade nagode tayiwa inna Sallama tafita sai kusan 2:00pm Sannan *SEERAJ* yabar asibitin saidai har wannan lokacin Baba be farka basai dai Likita yace karsu damu zaya iyafarkawa "a kowani lokaci.

💘💘💘💘
Washegari tunda 7:30pm saboda zayakai *SAJEEDAH* school,ta shirya tana zaune gaban baba, hannun shi taga yana motsi can kuma saitaga yabude idanu, dasauri ta'isa gurinshi cikin fariciki tace sannu baba katashi yajiki?..

"Ahankali Yace da sauki dai-dai lokacin da *SEERAJ* yashigo ita kuma inna tafito toilet, dasauri tace inna *yah SEERAJ* Baba yafarka suma dasauri suka isa gurinshi sunayi masa sannu ya'amsa, tareda cewa *SEERAJO* yaushe kadawo?..

shekaran Jiyabari nakira doctor yaduba ka dasauri yafita cansai gashi tareda doctor, *SAJEEDAH* tace baba kayimani Addu'a yau zamu fara jarabawa,yacetoh" *SAJEEDATU* Allah yabadasa'a Cikin farin ciki tace ameen baba.

doctor yace kudan fita don Allah zandu bashi sukacetoh *SEERAJ* yace baba zanje nakai *SAJEEDAH* school amma yanzu zandawo insha'Allahu Baba yace toh" sai kadawo sannan suka fita harda Inna,suna fita dasauri baba yakalli doctor yace?..

Muje zuwa

A

💘Zuciyata ce💘

Tareda Alkalamin

✍🏽

💘Lufhat ce💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

💘ZUCIYATA CE💘

_Based on true life Story_
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

2⃣5⃣

WRITTEN BY

💘©AMEENA UMAR FARUQ💘
OR
💘MEENAT💘

________________________

*_®PEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*

✍🏽

"Likita "Ina fatadai baka fada masu ciwon dayake damuna ba?.. yace "a ah baba ban fada masu batukun na amma yanzu dai idan nafita zanfada masu," da sauri baba yace yauwa likita toh" don Allah karka fada musu.

Cikin matsananci mamaki doctor kamal ya kalli baba saboda jin kalaman shi, "ahankali yace baba meyasa baka San afada masu" Sannan kasan ciwon dayake damunka ne?

"Ahankali Cikin sanyi murya baba yace nasani likita dasauri yace toh" wani irin ciwo ne keda munka?..yace koda KO Likita?..yace baba ya'akayi kasani ko dama ka taba zuwa asibitine aka fada maka kafin "akawoka nan?..

"Ahankali Baba yace "eh likita kwana ki naje general asibitin suka fada mani saida ban fada musu ba, saboda gudun tashin hankali su" nikuma "abunda natsan arayuwata shine tashin hankalin iyaliya shiyasa banaso kaima kafada masu.

Cikin sanyi murya Dr yace baba meyasa kaki fada masu, kasan rashin fadin abunda yahaifar kuwa?..
Kai baba ya girgiza cikeda tausayin kanshi, yace Likita kona fada masu basuda abunda zasuyi mani Wanda UBANGIJI Na bazayayi munshiba, koma nace tuni yariga yayi Mani shi.

domin wannan ciwon jarabawace Wanda UBANGIJI Na tabbatar zani iya dauka shiyasa yadora Mani, saboda haka kagasu" basuda "abunda yasuyi Mani baya ga Addu'a Allah yabani ikon cinye wannan jarabawa idan kuma natafiyane Toh" Allah yabani ikon tafiya ciki salama KO?...

Cikin tausayin baba Dr kamal yace' hakane baba amma dasai kafada, kagada sai "arubuta maka maganin ta kana siya kanasha kaga yanzu rashin fadin da bakayi ba yahaifar da babban matsala,
kuma saboda narashin shan maganinta ne da bakayi kaga sikainin din damukayi maka jiya yanuna gabadaya kodarka ta lalace Wanda dole za'ayi maka dashen ta.

Baba yace hmm Likita kenan ninan dakagani talaka ne wanda bayada komai sai kudirar Ubangiji, kudin dazan siyan magani banida shi toh" balle kudin da za'ayi Mani dashen koda Wanda kuma na tabbatar dashen kodar za yaci kudi masu yawa KO" Likita?..

Yace "eh baba maganar kudin siyan magani bayada matsala Na tabbatar Oga *"SEERAJ* zaya siya maka kamai tsadar shi, koshi kudin daza "ayi aikin baida matsala nasan duk zaya iyabiya kama, saidai inda matsalar take wanda zaya bada kodar shi "adasa maka.

Da sauri baba yace don Allah likita kabar maganar dashen kodar nan, tunda dai ba'abunda zayayiyu bane kaini kodama zayayiyu toh" nidai bazan yarda "a dauki kodar wani "asamani ba domin inaji "ajikinta
wannan ciwon bazaya barniba saboda haka kadaina wannan maganar karsuji hankalin su" yatashi.

Idanu Dr kamal yatsurawa baba cike da tausayin shi yace toh" yanzu baba yakake son ayi,?.. tunda kaga jiya nafara fadawa Oga *"SEERAJ* cewa ciwon koda ne yafara kamaka, shuru baba yayi nadan wani lokaci sai yace toh" shikenan Likita badamuwa saika cemasu shedin ne "amma dai beyi mani yawaba dazaran nafara shan magani zanji sauki kaji KO?..

Saidai don Allah kayi mani "alkawarin bazaka fada masu cewa sai Anyi mani dashen koda ba kaji?.. ahankali yace toh" shikenan insha'Allahu zanyi yadda kace, baba yace nagode nan dai Dr yayi mai abunda yadace yamasa Sannan yafita dakin jikinsa bakwari.

💘💘💘💘💘💘

Bayan *SEERAJ* yasauke *SAJEEDAH* a school, asibitin yakoma direct office din Dr kamal yanufa kamar yadda baba ya bukata haka Dr kamal yayiwa *SEERAJ* bayayi, tareda rubuta masa magunguna masu tsada yace yaje ya siya yakai wa baba yafara sha insha'Allahu za'adace, dasauri yafita daga office din yana yiwa Dr kamal godiya.

Kai tsaye gurin sayar da maganin yanufa bayan yasiya Sannan yanufi dakinda baba yake, da Sallama yashiga dai-dai lokacin da Inna take taya baba saka Riga kasan cewar fito warsa daga wanka kenan, atare suka amsa masa Sallamar. yace sannu Baba yajikin?..cikin sakin fuska yace dasauki *SEERAJO* kadawo yace "eh tareda mikewa Inna maganin yanayi mata bayani yadda za'aringa sha, takarba tana tayi masa godiya tareda samashi Albarka.

Kujera yaja kusada baba yazauna Cikin farinciki yace Baba yajikin?..dariya Baba yayi yace jiki kam Alhamdullah sannu *SEERAJO* dako kari nagode fa nagode sosai Allah yaimaka Albarka, yasaka gama da duniya lafiya, nan dai sukai tasamashi "albarka shidai bece komai, ba asalima cewa yayi Inna kawo magani "akwai wanda za'a bashi yanzu,

tace toh" tareda mika masa yacire wanda zaya cire yamika mata sauran sannan ya ballo, yamika wa baba Inna kuma tamika mashi ruwa yasha, dai-dai lokacin da 'akai Sallama. Sa'ade ce tashiga hannun ta dauke da dakayan abinci suka amsa mata bayan ta ajiye abinci, sannan ta gaidasu suka amsa bata, Dade batayi masu Sallama ta tafi.

*SEERAJ* ne yakalli inda Sajeed yake kwance yana bacci, yace Inna yau Jeed bazayaje makaranta bane?.. tace yaukam Inagani dakyar idan zaya iya zuwa makarantar nan saboda zazzabi kedamun shi, *SEERAJ* yace Ayya tareda karasa wa gurin Sajeed din zama yayi bakin gadon tareda taba jikin Sajeed din, jiyayida zafi sosai, yace Ai kuwa jikin nashi da zafi sosai tace' "eh Ai tunda asuba jikin nan yake dazafi,

Sajeed ne yabude idanu tareda cewa *yah SEERAJ* my friend kazo?,. yace nazo my friend mekeyi maka ciwo?..kamar zayayi kuka yace *yah SEERAJ* JIKINA ne yake ciwo, yace toh" kar kayi kuka tashi ka wanke baki kaci abinci sai muje "Dr ya rubuta maka magani da kasha zakaji jikin ka yabar ciwo kajiko?. yace toh' tareda tashi. haka kuwa akayi shiya taimaka mashi yakwanke baki, bayan yaci abinci sai sukaje Dr kamal yaduba shi, tareda rubuta masa maganin maleriya ce keson kamashi.

Bayan sunje yasiya masa magani Sannan suka koma daki yabashi yasha yace toh" ya kwanta.
yayinda shikuma suka cigaba da fira da baba Da Inna,
Sai gurin karfe 11:00 Am Sannan *SEERAJ* yabar asibitin don anan mayayi breakfast dinsa, bayan ya tabbatar baba yaci "abinci alokacin ma haryayi barci sannan yatafi.

koda ya'isa gida wanka yayi bayan yafito saita shirya cikin wata dakakkiyar shadda dark green sosai, kallo daya zakaiwa shaddar ka tabbatar saida "akazuba makudan kudi sannan "aka dauke ta, "abuga fari don haka sai shaddar tayimasa kyau sosai Kai gaskiya *SEERAJ* akwai kyau tubarakalla masha'allah, baisa hulaba saboda shidin bama abucin sata sosai bane saidai suman tasha gyara sai walkiyata takeyi, gata acukurkude kamar tajariri bayan yagama sai yakwashi wayoyin sa da walat tareda key mota Sannan yafito.

"Afalo ya iske Ammi da Abba zaune suna fira kallon shi sukayi cikin so da kaunar dan tilon dan'nasu, Ammi tace Ina zakaje bakayi breakfast ba kojiya mafa haka kayi?.. Abba yace' sai Ina haka?..yace Abba zanje bosso nena gaida rigimanmiyar tsohuwar nan ne yakare she fadi dayin dariya, dakuwa Abba yayi mashi tareda cewa ungo naka yanzu Hajiyar tawace rigimanmiya?..dariyayayi tareda cewa Allah Abba hajiyar takace sai "a slow.

Abba yace toh" ai shikenan saukin abun dai rigimanmun suna dayawa don gawata nan kusadani, da sauri yace Abba my Ammi sai nadawo dariya sukayi dukkansu hardashi Abba yace dan'nemakai kace inagaida ita inanan zuwa anjima Ammi matace yagaida ita yace toh tareda fita.

Koda yaje gidan inna wuro beyi wani da dewaba yabaro gidan Obasanjo complex yashiga, wayoyi yasiya guda uku tareda layinsu dukkan su sanfurdin Tecno ne saidai dayan tafi kyau da tsada kuma touch ce ita sabanin biyun daba touch ba, Bayan yafito sai yanufi wani super market kaya yake tafaman jida irin wanda yasan za'ayi "amfani dasu batareda "andafa ba, Bayan yagama sannana yanufi school Don dauko *SAJEEDAH* alokaci 12:30pm.

Yana isa wasuna fitowa bakin get yasamu guri can gefe yai parking yana kallon dalibai suna tafitowo, can saiya hangota tana tahowa.Cikin nutsuwa take tafiya idanu yatsura mata yanada yadaga ciki "abunda yasa yake kara *SONTA* nutsuwar ta da ibada, ahankali yace Allah kamallaka mani wannan baiwa taka amatsayin matata UWAR yayana domin dai *ZUCIYATA* nasonta.

_*Nikam nace toh" ameen*_

jiyayi wata murya tace *SAJEEDAH ABUBAKAR SADEEQ* *DEEQAR-JEEDART 4ever,* "ahankali yaga yajuya tana dariya dai-dai lokacin dayariyar takarasa guri,itama tana dariya tace ya exam?.. tace Alhamdullah SALMA NASIR yanaku? tace lafiya lau saikuma gobe tace toh Allah yakaimu yakuma bamu sa'a tace ameen, tareda wucewa itama tawuce hon taji agefenta dasauki tajuya dai-dai lokacin da yasauke glass din motar, Murmushi tayi tareda matsawa yabude mata kofa tashiga tareda cewa sannu *yah SEERAJ* yace yauwa me mulki *ZUCIYATA* yakike yakuma exam?..

Murmushi tayi kanta nakasa tace Alhamdullah, yace haka nakeson naji tace yajikin baba?..yace "baba yaji sauki harya yayi wanka yaci abinci yasha magani.Cikin farinciki tace Alhamdullah Allah mungode maka nandai yayi mata batayi "abunda "Dr yace cikin sanyi murya tace toh" Allah yabashi lafiya yace ameen ahaka har suka isa asibitin.
Chapter 19 · 0% Book details