← Book details Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 28

Sashe 16

Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*SAJEEDAH* kam tana komawa gida buta tadauka tashiga bayi tana shiga sai tafara kuka, "Ahankali takeyi tana fadin yah *"SEERAJ* Ina SONKA da dukkan *ZUCIYATA* amma meyasa kaimani haka?...yanzu shikenan da gaske mun rabu?...

Da sauri tace' "a ah nasan koda gangar jikinmu sunrabu toh" *ZUCIYOYIN MU* bazasu taba rabuwa da SON junaba, hakanan dai taita kukanta tareda surutai data gama tawanke fuska tafito.

Inna ta kalleta tace tace lafiya meyasa mi'idanunki?... jitayi gabanta yafadi "ahankaci tace' Inna wani abune yafada mun "acikin ido shine nawanke, "aranta kuma tace yihakuri Inna SON yah *SEERAJ* ne yake wahalar da *ZUCIYATA*,

Inna tace' assha sannu tace yauwa toh" yanzu abun yafitakosai nahure maki?... da sauri tace yafita, tace" Allah sarki har *SEERAJON* yatafi?... tace "eh yatafi tace' toh Allah yadawo dashi lafiya tace ameen.

**💘💘💘💘**
Bayan kwana biyu *SEERAJ* tattara yakoma gurin aiki *ZUCIYAR* shi cikeda Soyayyar *SAJEEDAH*, "a Jordan kam.

*SEERAJ* fly yake kamar mahaukaci fasinjan ko'ina dauka yake shida "abokin aikin sa, aikam sukam kamfanin Na Jordan sunjidadi kasan cewar sunasan "aikin shi saboda kwarewa shi don hakane yasa suketa bulbula masa kudi "acikin account dinsa,

Yayinda shikuma "abokin aikisa yafara nuna ga jiya warsa Da wannan Aiki dasu keyi haka bahutawa, sai kace "agogo shikam *SEERAJ* ba'abunda yada meshi,

fly kawai yake, koya samu yarage jin"abinda yakeji gameda *SAJEEDAH,* saidai kam ba'abunda yaragu saima karuwa Da *ZUCIYAR* shi yakeda kaunarta,

"idan kagan shi duk yara me sai hanci gawani kasumba (saje) dayabari "abuga fari sai yakara farin sosai fatarnan shar kamar kataba jiniyafito *SEERAJ* kenan'na *SAJEEDAH* ikon Allah.

"Abangaren *SAJEEDAH* ma haka "abun yake kullum da SON *SEERAJ* "a *ZUCIYARTA* take kwana da shitake tashi itama duK tarame, sai dukiyar Fulani da hips kawai ke takama "ajikinta Wanda Da "alama basusan halinda take Ciki ba, ga kuma karatu datasa "aranta don haka sai "abun yazamar mata goma Da "ashirin,
Haka dai rayuwa tai tafita fita ga masoya yayida *ZUCIYOYIN* suketa "azabtuwa da SON juna.

******💘💘💘****
Ayau watan *SEERAJ* biyu kenan dakoma gurin "aiki, Wanda yayi dai-dai dati uku kenan da kwantawar Baba rashin labiya tun yana iyafita har yazo yanzu baya'iyafita ko'ina saboda ciwon yayi tsanani,.

Kwance yake "atsakar gida kan dan lotsatsen katifa, Inna ce' keyi masa firfita, *SAJEEDAH* nagefe kamar zatayi kuka gani yadda Baba ke shan wahala, hartana tambayar kanta wannan wani irin zazzabi ne haka da baya jin maganin?...

Maganar Inna ce yakatse mata zancen zucin datake, da cewa shin wai Malam ranan Da kaje asibiti me Likita yace yana damuka?.. idanu yarintse "aranshi kuwa tunani yake meza yace mata?...
nafada mata Likita yace ciwon koda keda mushi?...

_*Kai! Nikam tsoro yakamani dataji irin ciwon dayakama baba, KODA?.. tabdi toh Alla yakawo sauki baba*_

"a ah Saratu kiyi hakuri bazan "iyafada makiba domin fadin yananufin tashin hankalinku, nikuma "Abunda banasan gani kenan afuskarku,

"Ahankali yabude idanu cikinjin "azaban ciwo yace' kin manta nace miki yace zazzabi da taifot neke damuna ba?... Cikin sanyi murya tace' "eh hakane toh" Allah yabaka lafiya yace' Ameen Cikin tausayi *SAJEEDAH* tace' sannu Baba,

yace yauwa *SAJEEDATU* Sajeedu yana can gurin teredar KO?..
tace, "eh baba "aikayan tiredar duksun kare saidan kadan yarage, yace bakomai Allah zaya rufa mana asiri.

******
DA misalin karfe shida na yamma
"Ahankali take tafiya yau ita kadai ce' batareda Sajeed ba tana sanye da uniform Na islamiyya, tafe take tana tunani yadda rayuwa tafara canjawa "agaresu'

musamman ciwon baba dayake ta kara tsananta gashi "abicin da *"SEERAJ* yakawo masu duk yakare hakanan kayan tiredan shima duk yakare, kudin kuma sun siyi magani "amma ciwo sai gaba yake,

Saiganin Mutum kawai tayi "a gabanta dasauri tadaga Kai ta kalleshi jitayi gabanta yafadi ganin irin Kallon dayake yimata, fuska "ayamutse yace kinganeni?..

"Ahankali tadaga kai domin kuwa bazata "alamar "eh domin kuwa bazata taba mantawa da shiba, tsaki yaja mtswwwww Sannan yace natsaneki idanu *SAJEEDAH* yazaro Cikin tsoro tace?...

Aha

Muje zuwa

A

💘Zuciyata ce💘

Tareda Alkalamin

✍🏽

💘Lufhat ce💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

💘ZUCIYATA CE💘

_Based on true life Story_
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

2⃣0⃣

WRITTEN BY

💘©AMEENA UMAR FARUQ💘
OR
💘MEENAT💘

_*Page din nakuna ne kuyi da yadda ku keso dashi, Aunty Na Hadiza Bamalli*_
_*MySweetheart*_ _*Sadiya*_
_*yar fillo tawa*_
_*FateenJos*_
_*Ummu Sadiq*_
_*Kaida duk wani masoyinZUCIYATA CE.*_
________________________

*_®PEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*

✍🏽

"Don ALLAH Alh karufa Mani asiri kamar yadda Allah yarufa maka, wlh Babana bayada Lafiya nadogara da Allah nadogara da kudin nan saboda samu siya masa magani ne, don girman ALLAH karka hana Mani kudin nan takarashi dasaki wani irin kuka maiba tausayi.

taki Mtswwwww Alh yaja tareda cewa "aifa saikiyi nikam nagama magana kuma, ya kalli Anas yace Oya tafi inda zaka yawuce Sannan shima yawuce, jiki Hajiya sanyi dajin abunda Alh yafada domin tasan halin shisarai idan yace' toh" fayace kenan, itakam wani lokaci Mamaki yake bata yadda yake nuna rashin "adalci DA tausayi acikin Lamarin shi.

_*Hmm Allah sarki rayuwa kenan, narasa meyasa wasu mutane sukeda sankansu dayawa, (bi'ma'na son ZUCIYA kenan ) wai saikaga kirikiri yayansu suna "aikata badai-dai ba, me makon su tsawata masu"sununa masu cewa "abun'nanfa dasukeyi ba'abune mai kyauba, amma a ah saisukiyin haka saima kaga suna goyon bayan yayan'nasu wani lokaci ma sainaga "anrufe Wanda akaiwa laifin dafada toh" wannan wani irin rashin Adalci ne haka?*.._

"Ahankali tadaga *SAJEEDAH* dake tafaman kuka tace Don kiyi hakuri ni kudi dake hannun Na duk baifi dubu daya ba, Bari Na daukomaki dai-dai lokacin da Abba yashiga cikin sanyi murya yace' Hajiya Lafiya meya faru naga tana kuka?.. Nan dai tafada masa duk Abunda yafaru,

Kai ya girgiza Cikin takaici halayyar DA dan'uwansa yakeyi marasa kyau, hannun yasa aciki "aljihun wandonsa yaciro walat dinsa tareda zaro kudi yan dubu-dubu guda biyu ya mikawa, *SAJEEDAH* tareda cewa kiyi hakuri nima banida kudi takarba tareda yin godiya, Hajiya mataje tadauko mata dubu daya takawo mata tareda cewa don kiyi hakuri kinji?..

Cikin kuka tace Hajiya nagode Allah yasa kamaku Da Alkhairi hijab dinta dake rataye saman igiya tadauka tasa Sannan tayiwa Hajiya Sallama tafita. tana Cikin tafiya kawai sai gani tayi ansha gabanta, da sauri tadaga Kai gabanta yafadi saka makon ganin Anas.

Cikin rawar murya tace Don Allah kayi hakuri kar kaketa Mani mutuncina, Murmushi mugunta yayi tareda cewa "Ayya yarinya marinafa kikayi, tace toh "aikarama yace ban ramaba yarinya yanzu dai zanrama.

"Ina kudin da su brother "Abba suka baki cikin tsoro tace' gasu tareda mika masa, hannun shi yamika zaikarba saiyana kokarin hadawa da hannun ta, "aida sauri tasaki kudin kasa tareda Da budawa a 360, tsaki yaja mtsww tareda cewa kin kuru yarinya da yau kinga ne bakida wayo kudin yadauka tareda juyawa yatafi.

Saida tayi nisa Sosai Sannan ta tsaya tana maida numfashi, tareda cewa Allah ya'isa mugu Azzalumi macuci kawai kuma sai Allah yabi mani hakkina, sai kuma tafashe dakuka mai ban tausayi tunani take yanzu shikenan duk lokacin da tabata tanayi masu "aiki tayi " don tasamu kudin dazasu siyawa baba magani yanzu yatashi abanza kenan?.., Allah ya'isa tasake furtawa hakan taita tafiya tana kuka har ta'isa gida.

Da Sallama tashiga gida direct gurin Baba tanufa tsugun'nawa tayi tareda cewa sannu Baba ya jiki?, yace' yau kindawo? tace "eh har ta tashi tamike, yace zonan *SAJEEDATU* tace toh" tareda tsugun'nawa "ahankali yace matso sosai,

"Ahankali takara gushi kusada shi Sosai idanu yakurawa fuskarta tareda Kai hannun shi saman kumatunta, inda shatin hannun Ana's yafito rudurudu Cikin sanyi murya yace' *SAJEEDATU* wanene yai wannan Aiki haka baisan cewa fuska gurine mai "DARAJA" ba?. amma shine ya mareki harsai da shatin hannun shi yafito "afuskarki.

Kuka tafashe dashi "aranta kuwa tanaji dole tafada masa gaskiya domin boyewar batada "amfani, wama yasani ko rashin fada masane alhakin shi yakamasu , a hankali yasake cewa *SAJEEDATU* wane yamarar Mani ke?.. Cikin kuka take fada masa duk "abunda yafaru.

Shuru yayi can kuma sai shima yafashe da kuka Wanda yasa hankali *SAJEEDAH* yatashi tareda Na Inna dake zaune kusa dasu, Cikin kuka yace oh Allah inada rayuwata wani yafaracin zarafin zuri'ata akan takare mutuncin ta, Oh ni Abubakar toh" inaga banida rayuwa?...

"Oh Allah kasani cewa nimarayane banida Uwa banida Uban yan'uwana sunkini, batareda nayi musu komai ba Ya UBANGIJI hakan yana nufin banida kowa bani komai sai KAI RABBIL'IZZATI, sai ko" zuri'ar daka bani,

Ya UBANGIJI kazamo gatana kakareni kakaremani zuri'ata KO" bayan baraina kajibanci lamuransu, Allah karkawa mutum ko Aljan damar cutamasu haka Baba yaita Addu'a mai ratsa *ZUCIYA*, yanayi yana hawaye suma *SAJEEDAH* da Inna sunayi suna fadin Ameen haka Sajeed yazo ya'iskesu shima yabi kayi, hakanan sukai tayin kuka babu mai lallashinsu saida sukayi mai isarsu' Sannan sukai shuru.

"Ahankali Baba yakalli Inna tareda cewa Saratu meyasa zakiyi Mani haka?.. Cikin kuka tace toh" Baban Sajeedu sokake mubarka Cikin wannan halin kullum ciwo sai Kara gaba yakeyi, yace toh idan ba ku barniba ya zakuyi dani kune zaku yaye Mani "Abunda Allah yadora mani?...

tace "a ah yace toh tunda baza ku'iyaba kubari ALLAH da yadora mani yayaye mani, ninasan wannan ciwon jarabawace "ina kuma rokon Allah yabani ikon cinyewa sukace' Ameen.

_*Ikon ALLAH wai duk wannan halin dasu SAJEEDAH suke Ciki Alh Siddi dashi DA iyalinsa, suci me kyau susha me kyau sukuma kwana a me kyau, Anya Alh Siddi makocin kwarai ne kuwa?..wai "ace kanada makoci ka kwana daya biyu sati daya sati biyu Kai har watan'ni baka ganshi ba, "amma kodai kace Bari dai nagani wannan mutumin ko Lafiya kwana biyu ban ganshi ba "amma bakayi haka ba toh" dama haka makotata yake? Kai Allah kaimana tsari DA makoci irin Alh Siddi Ameen*.._

****💘💘💘💘***
*JORDAN*
Firgigi yafarka daga firgitaccen mafarkin dayakeyi kwana biyu nan salati yakeyi, ga sanyi a c amma kuma saifam share gumi yake "ahankali yafurta meyasa nake ganiki kina kuka kullum saina ganki cikin barcina kina kuka, saidai kukan ki nayau yafi Na kullum Why! Why!! Why!!! *MY JEEEDAH* meyasa kike kuka?.. hakan yana nufin wani "Abu mara dadi yana damunki KO?..
Chapter 16 · 0% Book details