Sashe 5
Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Fatima ta amsa tana jin wani farin ciki na lulluɓe mata zuciya, ta ɗago kanta tana kallonsa da idanuwanta masu nuna tsantsar farincikin da take ciki, irin annurin da fuskarta ke fitarwa yasa Haroon tana kokarin buɗe baki tayi masa godiya ya ɗora yatsansa akan laɓɓanta da akullum yake jinsu tamkar auduga saboda taushinsu yana ƙare mata kallo cikin idanuwa, tasan me yake nufi dan haka bata ce komai ba sai ɗan zamewa da tai a hankali ta sake matsowa kusa dashi sosai ta shige jikinsa haɗe da ɗora kanta a saman faffaɗan ƙirjinsa, Haroon tamkar jiraye yake da hakan yasa hannayensa biyu ya rungumeta tsam yana kallon jaririn da har lokacin take rungume da shi ta kasa ajewa tamkar wacce za'a kwacewa shi. “A duk lokacin da nake tare da ke, duniya tana zama tamkar gida na lafiya da soyayya Fatima, nafaɗa maki gaskiya?” Fatima ta ɗaga masa kai ba tare data ce komai ba saboda yadda take sauraren bugun zuciyarsa da suka haɗe da kalaman dake fitowa daga bakinsa suka tashi wasu baituka tamkar waƙa suka saukar mata da natsuwa a zuciya, wata duniya take jinta ta daban gajimare na yawo da ita, ji tai ya ɗago fuskarta ya sumbaci bakinta “You're my comfort zone Princesse.” Murmushi ya ƙwace mata da sauri ta sake shigar da kanta cikin faffaɗan ƙirjin nasa cike da jin daɗi da farin ciki, mutsumutsun data soma jin jaririn nayi da ƙananun kuka ya sata saurin janye jikinta, ta sauka kan gadon ta miƙe ta ɗorasa a saman kafadarta tana ɗan bubbuga bayansa haɗe da kaiwa da komowa a tsakiyar ɗakin alamun lallashi, shi kuma Haroon ya ɗan yi baya kaɗan ya kwanta ya ɗora kansa a jikin pillow dake jikin kan gadon yana kallonta, sosai tayi masa kyau da zama uwa shi kan shi sai yake jinsa tamkar wani sabon mutum da aka sake halittawa a duniyar wuɗan dake amsa sunan iyaye. Fatima tafi minti ashirin tana abu ɗaya kafin ta samu jaririn ya koma baccin da yai ta ƙananun kuka, tare suka sauke ajiyar zuciya ita da shi jin ya yi bacci, Haroon ya taso ya miƙa mata hannu alamun zai karɓi jaririn, tamkar ƙwai haka suka lallaɓa tare suka ajiye sa a tsakiyar gadon, Fatima takai hannu ta rage ƙarfin gudun A.C ɗakin sannan ta ɗan zame tana ƙokarin kwantawa, riƙota Haroon yai ta juyo tana kallon shi, lumshe ido yai ya buɗe su akanta, baki ya buɗe zai yi magana tai saurin rufe masa bakin tana zaro masa idanuwa mai mai jin tsoron wani abu dake shirin faruwa da ita, da ido yai mata alamar tambaya Meye? ta marairaice fuska tana kallon jaririn, ya fahimci me take nufi, tsakiyar tafin hannun nata data rufe bakinsa dashi ya ɗan ciza ba tare data ankare ba da sauri ta sake masa bakin tana yarfi da hannun, ta cikin kunnenta ya rada mata magana “Tunda kin gama da ɗanki kizo ki shimfiɗeni bacci nake ji nima ko na saka miki rigima." Harara ta maka masa da wasa tana ɗan haɗe fuska, ya langaɓe kai irin yadda yara keyi shima, Fatima ta buɗe masa hannayenta tamkar mai yi masa oyoyo a hankali Haroon yazo ya shige hukunta yana sauke ajiyar zuciya, a haka ta jashi suka kwanta Haroon na sake jinta cikin ransa tamkar jini da anta, jikinta ya sake shigewa ita kuma ta shiga tofa masa addu'a rabin tunaninta kuma ya tafi wata duniyar. A haka ta samu shima Haroon ɗin yai bacci ta miƙe da kyar tana sake gyarawa jaririn kwanciyarsa sannan ta shige toilet ta yo wanka ta ɗoro alwala ganin kusan karfe biyu har da wani abu na dare yayi, tana fitowa tayi yan abubuwan data saba yi na kula da jikinta don macece ita mai son gyaran jiki da kulawa da kanta yadda yakamata, shiyasa idan ka ganta baza ka taɓa yadda tayi shekarun da take dasu ba. Kamar dai kullum Fatima sallah ta tayar tana miƙawa Allah kukanta, duk da yau adduoin nata sun sha banban dana kullum, a yanzu ba haihuwa kaɗai take buƙata ba ta fahimci har ƙwarin guiwar reno tana buƙata dan bawa maraɗa kunya.