← Book details Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 17

Sashe 10

Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A cikin harabar Sorbonne University, rayuwa na tafiya cikin sauri kamar yadda aka saba, students suna zirga-zirga, wasu suna dariya, wasu suna cikin damuwa, amma a tsakiyar wannan cunkoso akwai wata presence da take jan hankali ba tare da ƙoƙari ba Nayla Haroon, a hankali take tafiya a cikin corridor, takunta na fita da nutsuwa da confidence, ba gaggawa, ba tsoro, kamar wacce ta saba da kallo da kulawa daga mutane, hijab ɗinta mai tsabta ya zauna da kyau a kanta, kayan jikinta simple ne amma suna da class mai nauyi, duk wanda ya san quality zai gane cewa ba kayan kasuwa bane kawai, akwai tsari, akwai style, akwai ɗan alfarma a ciki, fuskar ta tana da wani irin haske, ba wai kwalliya mai yawa ba, amma natural beauty da ke fitowa da kanta, idanuwanta masu zurfi suna ɗauke da wani irin ɗan tsiwa da confidence, lips ɗinta suna ɗan motsi kamar tana riƙe da murmushi a ɓoye, ba raini gare ta ba, amma akwai wani irin girman kai mai kyau irin wanda ba ya cutarwa, amma yana nuna cewa ta san darajar kanta. “Hey Nayla…” wasu students suka kira suna wucewa, ta ɗan juya kai tana murmushi kaɗan “Hi…” ba ta tsaya hira mai tsawo ba, domin ba ta daga cikin masu son hayaniya, tana da nata circle, kuma ba ta yarda da kowa cikin sauƙi ba, Amina na biye da ita tana ta magana “Honestly you’re too calm… if it was me I would be shouting that lecturer didn’t come!” Nayla ta ɗan yi murmushi tana girgiza kai “You talk too much…” ta faɗa cikin wasa, suka zauna a bench kusa da glass wall da ke kallon harabar makarantar, rana na haskawa a waje, hasken ya sauka a fuskar Nayla yana ƙara fito da kyawunta cikin nutsuwa. Ta ɗan ja numfashi ta jingina baya, idonta ya ɗan lumshe, kamar tana tunani, Amina ta lura da hakan “What’s wrong?” Nayla ta buɗe idanunta a hankali “Nothing… just tired…” amma a zahiri akwai wani abu da ke cikin zuciyarta, wani irin yanayi da ba ta iya bayyana shi ba, kamar tana neman wani abu… ko wata rayuwa da ba ta samu ba tukuna. A cikin wannan lokaci, wayarta ta yi ƙara, ta ɗauka, screen ya nuna Yaya, ta ɗan murmusa kafin ta ɗaga “Yes…” ta faɗa cikin laushi, daga can ya tambaye ta ko ta isa, ta amsa “Yes I’m in school…” ya ce mata ta kula da kanta, ta ɗan yi dariya “I’m not a kid…” ya katse ta “Behave yourself…” ta ɗan turo baki “Okay…” ta katse, ta sauke wayar tana murmushi kaɗan. Amina ta kalleta da ɗan mamaki “Your brother is too serious…” Nayla ta ɗan ɗaga gira “You don’t know him…” ta faɗa cikin wata murya mai nuna cewa akwai wani abu daban a tsakanin su, ba wai kawai yaya ba… akwai wani irin kusanci da fahimta, amma kuma akwai wani layi da ba ya wucewa. Ta miƙe tsaye a hankali “Let’s go… since lecture is cancelled, I’m not wasting my day here.” suka fara tafiya, yayin da take tafiya, wasu idanu suna binta, wasu suna kallonta.

ZK2026
08081005693
07040402435.
ZUCIYA DA ƘUNA

By Billy S. Fari & Nana Hadiza
@nanadiso10 | Arewabook

PAGE 7.

Daga fitowarsa daga École Internationale Privée de Paris, bai tsaya ko’ina ba, motarsa kirar Rolls-Royce Cullinan Black Badge mai launin baki mai sheƙi ta tsaya a gaban katafaren ginin kamfaninsa mai suna RH GLOBAL HOLDINGS, wani gini mai hawa da yawa da aka yi da gilashi mai kyalli wanda ke nuna ƙarfin iko da kuɗi, guards biyu suna tsaye a ƙofar suna gaishe shi da girmamawa “Good afternoon, sir” bai tsaya ba, ya sauko daga motar cikin nutsuwa, suit dinsa na Italian tailored navy blue ya zauna jikinsa kamar an zuba masa, agogon Patek Philippe a hannunsa yana ƙara masa kima, tafiyarsa cike da authority, ma’aikata suna tsaye a gefe suna masa “Welcome sir” wasu suna sunkuyar da kai, wasu na murmushi amma babu wanda ya kuskura ya yi masa magana fiye da kima, kai tsaye ya nufi executive meeting hall, ba tare da ɓata lokaci ba aka fara meeting, projectors sun haskaka, screens sun nuna figures da charts, ya tsaya a tsakiyar table mai tsawo yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, muryarsa ta fito da nutsuwa amma cike da iko “Let’s get straight to the point…” CFO ya fara gabatar da rahoto kan sabon investment a Dubai real estate expansion, figures sun kai billions, amma Rayyan bai nuna mamaki ba, ya saurara cikin nutsuwa, sannan ya ce “The numbers are good… but I want higher returns… restructure the deal” kowa ya yi shiru yana rubutu, wani director ya yi ƙoƙarin ƙara bayani, Rayyan ya ɗaga hannu a hankali “I don’t want explanations… I want results” kalmar ta tsaya a zuciyarsu, aka ci gaba da meeting, aka tattauna kan agricultural export business dinsa da ke France countryside gonar da Fatima ta gada wacce ya juya zuwa babban kasuwanci, ya ce “We expand production by 40% this season… invest in modern equipment… no compromise on quality” awa ɗaya cif meeting ya ɗauka, amma a cikin wannan awa ɗaya, an yanke hukuncin miliyoyi, an tsara makomar kamfani, sannan ya juya ya fita ba tare da ya tsaya hira ba, ma’aikata suna bin bayansa suna masa gaisuwa, yana amsawa da ɗan ɗaga kai kawai, presence dinsa kaɗai ya isa ya cika wurin da iko.
Yana shiga cikin private executive office dinsa wani ɗaki mai faɗi, gilashi a ko’ina, view na birnin Paris daga sama, desk ɗinsa mai tsari da leather chair mai alfarma, ya zauna cikin nutsuwa yana buɗe laptop dinsa, a waje kuwa Noor personal assistant dinsa ta gan shi, zuciyarta ta buga, murmushi ya bayyana a fuskarta, ba ta ɓoye yadda take jin sa ba, a duniyarta babu wanda take so kamar shi, amma soyayyarta shiru ce, ta ɗauki file ta nufi ƙofar, ta yi knocking a hankali, “Come in” ya amsa ba tare da ya ɗago kai ba, ta shigo cikin ladabi tana tafiya a hankali, “Good afternoon, sir” ta ajiye file a gabansa, har yanzu bai kalle ta ba, “Please review this contract… it needs your signature” ta faɗa cikin nutsuwa, ya ɗauki file ɗin ya fara dubawa, ba tare da wani extra magana ba ya sa hannu, ta tsaya na ɗan lokaci kamar tana son ya ƙara magana, “Do you need anything else, sir?” ya amsa a takaice “No, thank you” kalmar ta rufe komai, ta juya ta fita a hankali, zuciyarta na cike da wani irin abu da ba ta iya fassara ba, tana fita ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, ta jingina da bango na ɗan lokaci kafin ta dawo cikin nutsuwa.
A cikin office dinsa kuwa, Rayyan ya jingina da kujera, ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, numfashinsa ya ɗan sauya, wani irin tashin hankali yadda gabansa ya mike, ba abu bane na jiki kawai, wani irin pressure ne na rayuwa, na nauyin da ke kansa, ya buɗe idanunsa a hankali yana shafa fuskarsa “Focus…” ya furta a hankali, ya dawo kan aikinsa, amma yau ba kamar kullum ba, hankalinsa ya ɗan watse, ya ɗauki wayarsa ya kira Mom.
“Hello Mom…” muryarsa ta sauya nan take, ta koma laushi.“Rayyan… are you okay?” Fatima ta tambaya cikin kulawa.
“I’m fine… just checking on you.” “Have you eaten?” ta tambaya kamar kullum. Ya ɗan yi murmushi “Not yet.” “Please don’t skip meals… you work too much.” “I will… don’t worry.” Ta yi masa addu’a cikin nutsuwa “Allah ya tsare ka… ya sa albarka a aikinka…”
“Thank you Mom…” ya amsa da girmamawa.
Sun yi sallama. Nan take ya kira Dad.
Chapter 10 · 0% Book details