Sashe 2
Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washe garin safiyar Paris ta waye cikin wani yanayi mai ɗan sanyi da shiru mai nauyi a unguwar Neuilly-sur-Seine, gidan dangin Haroon Kareem ya cika fal da mutane masu zuwa gaisuwa, motoci suna jere a waje, ana shiga ana fita ba ƙaƙƙautawa, kowa da fuskarsa ɗauke da tausayi da jimami, kowa na magana da murya a ƙasa kamar ana tsoron a ƙara tada wani sabon ciwo, a tsakiyar wannan taron ne jaririn da bai wuce kwana biyu da haihuwa ba ya zama abin kallon kowa, mutane na kallonsa da tausayi, wasu na girgiza kai suna cewa “Subhanallah… yaro ƙarami haka ya rasa iyayensa” wasu kuma na share hawaye suna furta “Allah ya raya shi cikin alkhairi” amma duk da wannan taron da wannan hayaniya mai sanyi, akwai wani abu da ya fi ɗaukar hankali Fatima, wacce tun jiya bata samu nutsuwa ba ko da minti ɗaya, idanunta sun kumbura, kanta na mata ciwo, zuciyarta cike take da wani irin tsoro da ba ta iya bayyana shi ba, haroon ya yi ƙoƙarin janyo ta su koma gida domin ta huta amma cikin kuka ta ce “No… I’m not going anywhere… ni da baby zamu kwana anan” ya kalleta cikin natsuwa ya san hakan zai faru, tun daga daren jiya ya riga ya yanke shawara a ransa cewa wannan yaron nasa ne har abada, ba zai bari wani ya shiga tsakani ba, ba zai bari wani ya ɗauke shi ba, saboda haka bai ƙara mata gardama ba sai dai ya ɗan shafa kanta a hankali yana cewa “It’s okay… I understand” dare ya shige, aka siyo madarar jarirai domin a ba shi amma abin mamaki yaron ya ƙi karɓa, yana ta kuka, ihu yana ƙara, kamar yana neman wani abu da ya ɓace masa, hankalin kowa ya tashi, wasu na ƙoƙarin ɗaukar shi, wasu na girgiza kai, amma babu wanda ya iya kwantar da shi, Fatima kuwa ta rungume shi kamar zuciyarta zata fita, ta ƙi bacci, ta ƙi zama, tana tafiya da shi a hannu tana lallashinsa “please baby… please calm down… I’m here…” amma yaron bai daina ba, sai da safe ya waye cikin wannan hali, a cikin wannan taron ne Zeynab, ƙanwarsu Haroon amma ba uwa ɗaya ba, Mahaifin su ne ɗaya. ta tsaya tana kallon Fatima da yaron, sannan cikin ɗan ɗaga murya ta ce “Sis… banda abunki fa, ina ke ina raino? You’ve never had a baby before…” kalmarta ta fito da ɗan zafi, wanda ya sa wasu suka juya suna kallonta, kafin Fatima ta ce wani abu, kakarsu Haroon Dada tsohuwa mai hikima da nutsuwa ta ɗago kai daga inda take zaune tana cewa “Zeynab… ki kiyaye bakinki, idan ba za ki godewa Fatima ba, to kar ki ƙara mata ciwo” Zeynab ta yi murmushi mai ɗauke da raini tana cewa “Grandy… you know me now, ai ni zan kula da yaron nan, ko ba haka ba?” kalmar ta faɗi da sauƙi amma ta sauka da nauyi a zuciyar Fatima, gabanta ya faɗi, zuciyarta ta ɗan buga, amma ta yi shiru, ta ƙara rungume yaron kawai, ta miƙe ta nufi babban falon gidan inda mata ke zaune, mahaifiyar matar Umar ce ke zaune tana karɓar gaisuwa, tana kuka lokaci-lokaci, Fatima ta ƙarasa kusa da ita, ta zauna, matar ta ɗago ta kalleta cikin tausayi “Sannu Fatima… Allah ya saka miki da alkhairi” wasu matan suka fara magana a gefe “Allah mai iko… ashe ita ce zata raini yaron” wata ta ce “To ai ba ta taɓa haihuwa ba…” wata kuma ta ce “Dada ce ta fi dacewa da shi” kafin hayaniyar ta ƙaru, mahaifiyar matar Umar ta ɗaga murya cikin ƙarfi “Ku daina magana haka Babu wanda ya cancanci zama uwarsa sama da Fatima” shiru ya sauka na ɗan lokaci, amma wata tsohuwa a gefe ta sake cewa “Haba… yaro fa yana buƙatar wanda ya san raino…” kalmomin suna shiga kunnen Fatima kamar allura, amma bata ce komai ba, ta yi shiru kamar yadda take yi, sai ƙarar wayarta ya katse komai, ta duba, saƙo daga Haroon “Come upstairs… Aslam room” ta miƙe a hankali, jikinta ba ƙarfi, idanunta sun yi nauyi, zuciyarta cike take da damuwa, tana tafiya har ta isa matakala, kafin ta hau sai ga Zeynab ta biyo ta “Fatima… yakamata ki sauko da yaron nan, people want to see him… kin ɗauke shi kamar naki ne” kalmar ta sake soka mata zuciya, cikin ƙarfin hali ta ce “To…” ta miƙa yaron ba tare da ta kalle ta ba, ta juya ta haura sama, hawaye na zuba a idonta, zuciyarta na raɗaɗi, tana shiga ɗakin da aka nuna mata, ta tarar da Haroon zaune a kan kujera, jikin sa ɗan sanyi, fuskar sa ta nuna gajiya, bai faɗa mata ba cewa an yi masa allura saboda zazzabi, ya san idan ta sani hankalinta zai ƙara tashi, da ta gan shi, sai ta garzaya ta rungume shi, kuka ya ƙwace mata “Ils ne veulent pas me donner le bébé… Zeynab keeps talking… Haroon please… he’s my baby… I love him… I will take care of him… please…” ta riƙa magana cikin harshen Faransanci tana kuka kamar zata fadi, Haroon ya riƙe ta a hankali yana shafa bayanta “Fatima… please… calm down… kina son ki ƙara tashin hankali ne?” ya ɗan ɗaga kanta ya kalle ta cikin ido “Listen to me… yaron nan naki ne… nobody will take him from you… ke ce uwarsa… and you will even choose his name… he has no mother now… you are his mother… do you understand?” ta kalleshi cikin mamaki, idanunta cike da hawaye “Da gaske?” ya ɗaga mata kai “Yes… I promise” sai a lokacin ta ɗan sauke numfashi, zuciyarta ta ɗan samu natsuwa, daga nan ta lura da jikin sa “Are you sick?” ya yi murmushi mai laushi “I’m fine…” amma ba gaskiya ba ne, duk da haka farin cikin da ya shiga zuciyarta ya sa ta manta da komai, har ta yi sujudin godiya a gefen gadon “Alhamdulillah…” Haroon ya kalle ta da tausayi, yana jin yadda take jin wannan yaro kamar nata, a daidai lokacin Aslam ya shigo da abinci, ya ajiye yana cewa “You need to eat bro…” sannan wasu ‘yan uwa suka shigo suna masa gaisuwa “Ya jiki?” “How are you holding up?” Uncle Usman ya zauna kusa da shi yana cewa “Na san dole ka ji zafi… you were very close to Umar” Haroon ya sauke kai, kalmar ta taɓa masa zuciya, kafin yanayin ya koma kuka, Aslam ya yi sauri ya ce “Doctor said no stress please…” Fatima ta miƙe a hankali ta bar ɗakin, ta sauko ta koma kusa da Dada, wacce take son ta sosai, Dada ta ja ta kusa da ita “Zo nan…” ta zuba mata abinci da kanta “Sai kin ci…” Fatima tana cin abincin a hankali, Dada ta ɗago ta kalli Zeynab “Zeynab… ga uwarsa nan… ki kawo mata yaronta” Zeynab ta ji haushi sosai amma bata da wani zaɓi, ta miƙa yaron ba tare da so ba, Fatima ta karɓa da sauri kamar wanda aka ƙwace mata wani abu mai muhimmanci, ta rungume shi “My baby…” ta miƙe da shi ta nufi kitchen “Let me prepare his milk…” duk mutanen da ke wurin suna kallonta, wasu suna jin tausayinta, wasu suna jin mamakin yadda ta haɗu da yaron cikin sauri haka, ta shirya madarar cikin nutsuwa, ta dawo ta zauna, ta fara ba shi a hankali, abin mamaki… yaron ya fara sha, ya yi shiru, kamar ya gane hannun da ke riƙe da shi, kamar ya sami abin da yake nema tun jiya, Fatima ta kalle shi hawaye na sauka amma wannan karon na farin ciki ne “See… he knows me…” bayan ɗan lokaci, bacci ya ɗauke shi, bacci mai nauyi wanda bai samu jiya ba, ita ma ta jingina da kujera, jikinta ya yi sanyi, idonta ya lumshe, kamar karon farko tun jiya da ta samu natsuwa, Dada ta ɗan gyara mata mayafi, mutane suna ci gaba da shigowa suna gaisuwa har zuwa dare,