← Book details Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Nayla basu dawo ba sai after magrib Rayyan yaje da kansa ya dauko su, dama yayi waya da ita yace su jirasa zai zo ya ɗauke su, tafe suke Suhayla sai labari take zuba masa kamar yadda suka saba yi masa aduk lokacin da suke tare, sai dai wannan karon banda Nayla bata ce komai ba tunda ya ɗauko su, ba tare daya kalleta ba yana driving “Nayla what's happening?" Juyowa tayi ta kallesa jiki a sanyaya, a yau kaɗai, acikin awannin da basu gaza biyar zuwa shida ba ta faɗa soyayyar wanda bata taɓa gani ba sai yau, soyayya mai zafi da tunda tayi ido biyu dashi sai nukurkusar zuciyarta take yi, gashi takasa fadawa ko da Amnah ce balle ta samu sassauci abinda take ji, ji take yi kamar tai karfin halin sanar da yayan nata sai dai bata san taya zata fara yi masa bayani ba, ɗauke kanta tayi tana kallon gefen fito jin ya sake jefo mata tambayar "nothing Yaya.” "Are you sure?" “Up course." Jin ta tabbatar masa da haka sai kawai ya share zancen, a wani mall ya tsaya ya shiga dasu, abubuwan duk da yasan suna bukata a matsayinsu na mata yasa suka ɗauko Mom kuma ya siyo mata turarukka sanin yadda take masifar son ƙamshi, dama duk wata yakan ɗaukesu ya kai, ko kuma yaje da kansa ya siyo masu, tun suna yara shi ke maye masu gurbin Dad idan baya ƙasar har ma idan yana nan wajen kula dasu ga duk abubuwan daya san zasu buƙata ba tare da gajiyawa ba saboda yana kallon hakan a matsayin dolensa, a ransa yana ji bai da kamarsu kamar yadda basu da kamarsa, shiyasa ya dauki alwashin zame masu Yaya mahaifi wajen basu kariya da kuma kulawa ga dukkanin abinda zasu buƙata.
Bayan sun gama suka nufi gida Nayla jiki tamkar an yimata duka kai tsaye ta wuce ɗakinta, Allah ne sheda matsuwa tayi su iso gida dan duk wanda ta gani sai taga yana mata gizo da wanda ta gani gidan su Amnah, hatta Ya Rayyan ɗin da suna magana da Suhayla taga yayi dariya sai taga tamkar shi ɗinne lokacin da yake yiwa Ikramah dariya “Ya Allah! Wanene shi?" Nayla ta faɗa kan gadonta tana faɗa tare da rufe idanuwa.

_(Tofah! Nayla ta ɗebo mai zafi zafi💃)_

MONDAY MORNING

Kamar yadda Dady ya faɗa haka ta kasance, tun kafin ya sanar da Alhaji Nuhu Shattima ƙudurinsa na don haɗa yar wajensa da tsaronsa Rayyan yana kiransa akan zancen taron yake sanar dashi bazai samu damar halarta wajen taron ba saboda tafiya Egypt ta kamasa zai kai mahaifiyarsa a dubi idanuwanta da take fama dasu suna yimata ciwo, amma ya sanar dashi zai sa Hanan ta wakilcesa wajen ya tabbatar duk abinda ake buƙata daga ta ɓangarensa zata bayar yadda Yakamata, murmushi Dady yai, a zuciyarsa yana cewa faɗuwa tazo dai-dai da zama, a zahiri kuwa cewa yai babu Matsala bayan ya jajanta masa tare da cewa ya bayar masa da Hajiya idan sun dawo zasu zo dubata shi da iyalinsa, a cikin daren ya kira Rayyan ya sheda masa yana da wani taro da zai halarta yana so shima yake ya wakilcesa a wajen wannan taron, ya bashi duk wasu documents daya kamata, ya yi masa bayanin duk wani abu da za'a gabatar saboda kusan shine jagoran taron, sosai Rayyan ya fahimci bayani sa har yana sake bashi shawarwarin abunda ya dace a wasu wuraren, Dady ya ji daɗi hakan dan haka yace yaje duk abinda ya kamata a gabatar, idan ya dawo daga baya zasu tatfauna matsayar da aka cimma wajen taron da manyan yan kasuwan.

Karfe 8:30am
Chapter 16 · 0% Book details