← Book details Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 17

Sashe 14

Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

suka shiga gidan Uncle Usman tana ƙwalawa Amnah kira, Amnah tafito da gudu suka rungume juna “Ke yar air na ɗauka baza ki zo ba fa da ban ganki ba jiya." Amnah ta faɗa suna riƙe da hannun juna ita da Nayla, Suhayla kuwa can gefe ta nufa inda ta hango su Mahbub da Ikramah ana yi masu lesson dan sune sa'anninta musamman Mahbub da suke matukar shiri dashi, dariya Nayla tayi “Bari kawai Amnah kin san Yayanmu ba lafiya jiya aka sallamosa daga asibiti shiyasa baki ganni ba." “Hmm ai na ɗauka ma shiya hanaki zuwa tunda baya son zumunci kuma yana hanaku.” " Laaa.. wallahi kin masa sharri ba haka bane." Nayla ta faɗa tana kallon gun da akewa su Mahbub lesson jin wata murya data tafiyar mata da hankali na dukan dodon kunnenta, idanuwanta ne suka sauka akan Uncle Sajid dake yiwa Ikramah faɗa kan rashin maida hankali, a ɗaya ɓangaren kuma yana taya yan uwanta yi mata dariya yadda yai mata wani question ta kasa amsawa. Lumshe idanuwa Nayla tayi ta sake buɗe su akansa, lokaci ɗaya taji wani abu mai ƙarfi ya dira a zuciyarta akansa, wani yanayi da bata taɓa tsintar kanta aciki ba ya ziyarceta, ƙaƙƙarfan wani irin sinadari taji kai tsaye na tasowa daga cikin idanuwanta mai kama da wutar lantarki yana neman isar da wani saƙo ga mutumen da bata taɓa gani ba, bai santa ba itama bata san shi ba, gaba-daya ta rikice ta kasa tsayar da natsuwarta sai juyowa take yi tana kallonsa. “Ke Nayla lafiya kike?" Muryar Aunty Zeynab data zo gidan zata tafi suka kusan cin karo ta faɗa fuska a ɗaure, da sauri ta dawo hayyacinta daga duniyar data tafi ta wucin gadi, sai dai har yau maganaɗisun dake kokarin janta wajen sanin ko waye wancan mutumen data gani bai saketa ba, "Wlh Amnah na rikice.” "Da akai uwar me? Ko rashin ganin girman mutane ne da kika gado wajen uwarki zaki nuna mun, har ina miki magana kina cewa kin rikice." Aunty Zeynab ta faɗa a ɗan hasale cikin ɓacin rai, maganar ta daki zuciyar Amnah, ta ji rashin jin daɗin kalaman a zuciyarta, amma bata ce komai ba, a yanzu ba lokaci ne da take fahimtar komai ba saboda zuciyarta ta tafi wani gun, gaida ita tayi tana bata hakuri, tsaki zeynab ta ja tana ci gaba da masifa da faffaɗar maganganu marasa daɗi akan Mom, Nayla na kin zafinsu amma ta saurara saboda ba yadda zata yi, haka Aunty Zeynab ta ƙarasa masifa ta tafi tana jin haushin Nayla ɗin, taso ta tanka mata ta nada mata shegen duka a gidan, so take ta rage zafin mahaifiyarta dake zuciyarta na tsawon shekaru amma ta rasa ta wace hanya zata iya yin hakan, Nayla nada hankali, duk yadda aka zagesu a cikin family ko aka ci zarafin Mahaifiyarsu, zata ji zafin har tana ji kamar ta rama amma bazata taɓa zuwa ta sanar da ita ba, takan sha damuwar ita kaɗai wasu lokutan saboda bata son su ci gaba da musgunawa mahaifiyarta idan har taje ta faɗa wani abun ya faru. Zeynab ko dama a hasale take da Mahaifiyarsu Amnah ke sanar da ita rashin lafiyar Rayyan da Uncle Usman ke sanar da ita ɗazu daba kowa ya ji ba, kasa hakuri tayi har ta isa gida akan hanya ta kira Mom tayi mata tas “bamu san kin fimu son Rayyan ba sai kin cire jininmu dake jikinsa kin musanya da naki jinin, waya sani ma ko ke kike neman ajalinsa kike so ya mutu ku gade dukiyarsa shi yasa kikai kane-kane kika hana kowa ya raɓesa, ai wallahi kin ji haushi kuma indai Rayyan ne sai mun nuna miki mun fiki karfi akansa dan zai dawo hannunmu dole, wawiya mai raba zumunci kin dai ji kunya saboda you're after his money.” Mom na zaune a falo ne tana kallo Zeynab ta kira wayar ta ɗauka, duk abinda take faɗa Rayyan na jiyota daga cikin wayar, shigowarsa kenan falon yazo ya zauna akusa da mom ɗin, sosai ransa yai mugun ɓaci da kalaman ƙaunar mahaifin nasa, idanuwansa suka kaɗa sukai jajir, zuciyarsa tayi zafi tamkar ana tafasata da sauri ya miƙe ya wuce ɗakinsa, ba'a jima ba ya sauko cikin shiri riƙe da makullin motarsa ya nufi kofar fita, bayansa Mom da zuciyarta ke lulluɓe da kunci tabi tana kiran sunansa cike da son dakatar dashi, sai dai ko data isa harabar gidan har ya tada motar da karfi ya fizgeta yabar gidan “Ya Salam." Ta faɗa tare da komawa ciki ta dauki wayarta tana kiransa, amma sai taji karar wayar ya barta anan falo…
Chapter 14 · 0% Book details