Sashe 12
Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Daga Paris Charles de Gaulle Airport ne Rayyan ya ɗauko mahaifinsa Haroon Kareem, convoy ɗin motoci masu tsada suna gaba da baya suna tsare su cikin tsari mai kyau, motar Rolls-Royce Cullinan na tafiya cikin nutsuwa a kan titin da ke cike da hasken yamma, birnin Paris na walƙiya a gefensu kamar wani zane mai rai, Haroon ya jingina da kujera yana kallon ɗansa da wani irin farin ciki da gamsuwa, “My love… I think it’s time,” ya faɗa cikin nutsuwa, Rayyan ya ɗan juya kai ya kalle shi da murmushi mai sauƙi, “Time for what, Dad?” Haroon ya ɗan yi dariya “Time for you to get married…” Rayyan ya girgiza kai a hankali yana ɗan murmushi, “Dad… I’m not seeing anyone…” Haroon ya ɗaga gira cikin wasa, “Ba wai dole sai ka ga wata ba, we can find you someone…” ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara, “Your mom even said no at first when I mentioned Hanan… ‘yar gidan abokina…” Rayyan ya yi ɗan murmushi mai cike da nutsuwa, “Then talk to Mom, Dad… idan ta amince… I’ll accept,” kalmar ta fito da sauƙi amma tana ɗauke da girmamawa mai girma, Haroon ya ɗan kalli ɗansa da idanu masu cike da alfahari, ya shafa kansa a hankali “Allah ya yi maka albarka, my son… I’m proud of the man you’ve become…” Rayyan ya ɗan sunkuyar da kai cikin ladabi, motar ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa har suka isa katafaren gidan su na Neuilly-sur-Seine, ma’aikata suna jere suna gaishe su, amma Rayyan bai tsaya ba, ya wuce kai tsaye zuwa cikin ɗakinsa, ya cire suit dinsa cikin nutsuwa, ya shiga bathroom, ruwan shower mai ɗumi ya sauka a jikinsa yana kawar da gajiya da tunanin da ya taru a kansa, bayan ya fito ya ɗauki wayarsa ya kira Mom, “Mom… I’ll sleep early tonight… don’t worry if you don’t see me,” Fatima ta amsa cikin kulawa, “Are you okay?” “I’m fine…” ya faɗa cikin laushi, “Just tired,” ta ce “Alright… but I’ll check on you,” ya yi murmushi kaɗan, “I know…” ya ajiye wayar, ya kwanta a gadonsa mai faɗi, amma kamar yadda ta saba… Fatima ba ta yarda da kalmarsa kawai ba, ta leƙo ɗakin sau ɗaya… sau biyu… sau uku… tana kallonsa cikin kulawa, har ta matso kusa da shi ta taɓa goshinsa a hankali, “You’re not sick, right?” ya buɗe idanunsa kaɗan yana murmushi, “I’m fine Mom…” ta gyara duvet dinsa ta rufe shi sosai, sannan ta fita cikin nutsuwa.
A ƙasa kuwa… Nayla ta sauko daga saman bene cikin nutsuwa, tana sanye da doguwar riga mai sauƙi amma mai kyau, “Daddy…” ta kira da wani irin ɗan shagwaɓa mai laushi, Haroon ya juya yana murmushi “My princess…” ta ƙaraso kusa da shi ta riƙe hannunsa, “It’s been five days… I didn’t see you… even video call you didn’t pick…” ta ɗan turo baki kamar ƙaramar yarinya, Haroon ya ɗan riƙe hannunta yana lallashi, “I’m sorry Nayla… work was crazy…” ya ɗan sumbaci goshinta “How’s school?” ta yi ɗan murmushi, “We’re almost done… just a few more weeks,” ya ce “That’s good…” ta juya ta kalli Fatima, “Mom… can I go to Uncle Usman’s house tomorrow? Please don’t tell Yaya… he’ll say no… and Amnah invited me…” Fatima ta ɗan yi murmushi tana kallon ta, “Ask your brother first… idan ya yarda, then it’s fine,” Nayla ta yi ɗan tsaki cikin wasa, “Okay Mom…” ta juya tana cewa “Goodnight…” ta haura sama, saboda ita ba ta jinkirin bacci, tana son ta kwanta da wuri saboda lectures.
A falon kuwa Haroon ya juya ya kalli Fatima, “About Hanan…” ya fara magana cikin nutsuwa, Fatima ta ɗaga kai, “No… Haroon, I’m not comfortable…” ya ɗan yi murmushi “Haba Fatima… Rayyan is grown now… he needs a wife… a family…” Fatima ta sauke numfashi, “Ina tsoron ya samu mace mara tarbiyya…” kalmar ta fito daga zuciya, Haroon ya ce cikin natsuwa, “Then investigate… ki bincika… idan ta dace… we move forward,” Fatima ta ɗaga kai a hankali, “Alright… I’ll look into it…”
A cikin ɗakin Rayyan kuwa… ya tashi daga kwanciyar da ya yi, ba saboda bacci ya ƙoshi ba… sai saboda wani mafarki da ya tashe shi, ya zauna a gefen gado yana sauke numfashi a hankali, zuciyarsa na bugawa da sauri, ya shafa fuskarsa, “Ya Allah…” ya furta a hankali, ya miƙe ya sake shiga bathroom, ya wanke jikinsa da ruwan sanyi wannan karon, yana ƙoƙarin dawo da kansa cikin nutsuwa, ya fito ya sa kaya masu sauƙi, ya tsaya a gaban madubi yana kallon kansa, akwai wani abu da yake ji a jikinsa… wani irin restlessness da ba ya son shi, da ba ya yarda da shi, yana jin kamar jikinsa yana buƙatar wani abu da zuciyarsa ke ƙin yarda da shi, ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, yana tuna kalamansa da ya faɗa wa Amir, “Control is a choice…” ya buɗe idanunsa a hankali, ya ɗan yi murmushi mai rauni, “I have to be stronger…” ya koma kan gadon.
ZK2026
08081005693
07040402435.
ZUCIYA DA ƘUNA
By Billy S. Fari & Nana Hadiza
@nanadiso10 | Arewabook
PAGE 8.