← Book details Yaudara Da Cin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 8

Sashe 8

Yaudara Da Cin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

{ *A short and interesting true life story*}
*NA*
*UMMU BASHEER*
*REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart
of reader's
#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*DEDICATED TO RAHMAT MUHAMMAD RUFA'I NALELE*
*PAGE* *35*~*40*

*Shafin k'arshe*
*THE END*
*Wani* irin kuka ABRAR yakeyi cikin tsananin tashin hankali, da gaske matar shi HAFSAT ta rasu, zuwa yayi gaban gawan HAFSAT Yana hawaye, tare da yin Mata addu'a, SA'EED ko police sun tasa shi gaba an sa shi a mota, Nan wasu police sukayi bincike, da k'yar ABRAR ya d'auki wayan shi ya Kira Baba ya sanar da shi, ba tare da b'ata lokaci ba ya iso shida mahaifin HAFSAT, k'warai da gaske sunji zafin mutuwar HAFSAT ba k'adan ba, lokacin da mutane suka ji cewan SA'EED ya kashe matar abokin shi, sunyi ta tsine mai albarka, JAWAHIR da taji ta girgiza, haka tayi ta kuka, domin ita dai babu wani abu da ya tab'a had'a su da HAFSAT dole tayi kuka, Maman HAFSAT tayi kuka sosai dan tayi rashin 'yar ta.
Anyi ma HAFSAT jana'iza inda aka Kai ta gidan ta na gaskiya,(Allahu Akbar, kullu nafsin za'ikatul maut, dukan Mai rai sai ya d'and'dani mutuwa, Allah kasa muyi mutuwar shahada, Allah ka yafe Mana zunuban mu, Ameen).
ABRAR mutuwar matar shi HAFSAT ya girgiza shi, bai tab'a tunanin aminin shi Wanda ya yarda da shi zai yaudare shi ba, Wannan wani irin *YAUDARA DA CIN AMANA* ne, Nan ya tuno cewa Yana meeting sai Kiran shi HAFSAT takeyi, ashe ba rabon su sake magana ne a duniya, tabbas shine sanadiyar shigan HAFSAT wannan hali na masha'a da suke aikatawa da SA'EED domin da ya kula da ita da tun farko hakan bai faru ba, yayi nadama sosai, Nan ya tuna da text message d'in da tayi mai ana saura awa kusan biyu ta r
asu, ga abin da tace.
*Assalamu Alaikum*
*Ya mijina tabbas na aikata maka babban laifi Wanda bansan ta Ina Zan fara rok'on gafarar ka ba, ka yafemin ka gafarce ni, tabbas nayi kuskure da na biye ma shaid'an, na biye ma son zuciya, gashi yanzu ina nadama ,Ina son ka gafarce ni, Ina son muyi sabuwar rayuwa mai cike da dad'i, Ina son ka miji na ka yafemin abin da na aikata ma, a yanzu haka na fita ba tare da izinin ka ba amma ka yafemin, wannan shine na k'arshe,I LOVE YOU*.
*Your wife HAFSAT*
Wani irin kuka ya fashe da shi, Yana girgiza kai, Ina ma ace mafarki yakeyi.
B'angaren SA'EED ko an kulle shi inda aka tsanan ta bincike sosai Kuma bincike ya nuna shine yayi kisan Dan babu wani alamar da za'ace ba shi bane, iyayen shi da suka ji sunyi bak'in ciki sosai da abin da SA'EED ya aikata.
An samu wani da yasan AZEEZA lokacin da tayi accident, har hospital ya kaita Yana zuwa doctor yace ai ta rasu, Nan mutumin ya Kira Daddy'n ta ya fad'a mai, Nan da nan sai ga iyayen ta sun zo, hankali su ya tashi sosai, haka Mommy tayi ta kuka, yayin da Daddy yake nadama, Dan yasan duk abin da ya faru shine sanadi, gashi yanzu AZEEZA ta rasu ta bar su, karatun ma da yace sai tayi bai ga amfanin shi ba haka sukayi ta kuka sannan suka tafi da ita gida, da k'yar aka samu mutane akayi mata salla aka Kai ta gidan ta na gaskiya.
Kotun ya cika mak'il da mutane, kowa sai ya tsine ma SA'EED suna tirr da irin hali irin na shi, yasha zagin duniya sosai, kowa na cewa saboda Yana aikata masha'a da matar abokin shi to tayi nadama tace su rabu shi Kuma yak'i yarda ya rabu da ita shine daga k'arshe ya kashe ta, cewan mutane kenan.
Gaba d'aya SA'EED ya canza ya rame yayi bak'i yayi muni, gashi duk duniya babu Wanda zai yarda cewa ba shine yayi kisan ba, sai lokacin yake tuna maganar da AZEEZA tayi mai na cewa sai ta tona mai asiri ta sa yayi nadamar abin da ya aikata Mata, gashi yanzu maganar ta ya tabatta, Dan abin da ta fad'a ya faru, Nan alk'ali ya yanke ma SA'EED hukuncin kissa, Nan duk mutane suka Fara magana kowa na fad'in hakan yayi dai-dai, wasu na fad'in sun tausaya Mai.
ABRAR ne ya kalle SA'EED lokacin an fito waje za'a sa shi a mota, yace"SA'EED ko zaka iya fad'a min abin da na aikata maka a rayuwa da zaka min irin wannan sakayar ? Wannan wani irin *YAUDARA DA CIN AMANA* ne? Meye ban yi maka na alkhairi ba da zakayi min haka, meyasa zaka kashe min Mata ta? Ka YAUDARE ni ka CI AMANA na, bazan yafe maka ba, ka cutar da ni" ya fashe da kuka, baban shi ne ya rik'e shi zasu shiga mota.
Da sauri cikin nadama SA'EED yace" A'a kar kace haka, na rok'e ka da ka gafarce ni, tabbas nayi kuskure, Kuma na San ko da Zan shekara Ina fad'a muku ba ni na kashe ta ba baza ku yarda ba, Dan Allah ku yafemin, nasan na Yaudare ka naci AMANAR aminan taka amma ka yafemin ko na samu Rahma, Kuma babu abin da ya shiga tsakani na da HAFSAT, hasalima ta rasu muna masu yafe ma juna da nadama, kuma HAFSAT ta na son ka, ni dai na shiga tsakanin ku na rok'e ka gafara" ya fashe da kuka mai cike da nadama.
ABRAR cikin dauriya yace" Na yafe maka, ka nema yafiya gurin Allah" kawai ya shiga mota suka bar gurin, yayin da akayi gaba da SA'EED dan aiwatar da hukuncin da aka yanke mai.
*************************
*Five years later*
Wasu Kyakyawan yara na gani su biyu suna wasa, can sai ga wata kyakyawar mata, JAWAHIR kenan, ta fito tare da ba yaran juices a cups tana murmushi, ABRAR ne ya fito Yana cewa"Mommy ni Ina nawa juice d'in?"
Dariya sukayi gaba d'aya, tare da mik'a mai, Yana karb'a ya rungume ta yace"Ina ma Allah godiya da ya azurta ni da matar irin ki da Kuma Yara na HANIF da HAFSAT, Allah ya raya Mana su"
"Ameen"Tace
Yace"Allah ya raba mu da *YAUDARA DA CIN AMANA*"
Tace"Ameen ya Allah miji na" ta rungume shi.
*Alhamdulillah*
*Anan na kawo k'arshen litafina Wanda ya faru ne da gaske, sai dai na tsara labarin ne, kuma ina Jan hankalin mutane da su d'auki DARASI a wannan litafin domin mutane dayawa na fuskan irin wannan matsalolin, to Allah ya yaye Mana Allah yasa mu fi k'arfin zuciyar mu Ameen*
*Allah ya yafemin duk wani kuskure da nayi ba tare da sani na ba, Ameen*
*Ku biyo ni a sabon novel na Mai suna AKAN K'ANWA TA, Yana Nan zuwa Nan ba da jimawa ba*
*Massoyan litafai na Ina godiya da k'aunar ku gare ni Allah ya bar zumunci da k'aunar junan mu Ameen*
*TAKU CE UMMU BASHEER MAI K'AUNAR KU*
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
e3c0fd3443274f88b58d5d96110b1dc8
Chapter 8 · 0% Book details