Sashe 7
Yaudara Da Cin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
{ *A short and interesting true life story*}
*NA*
*UMMU BASHEER*
*REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart
of reader's
#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*DEDICATED TO RAHMAT MUHAMMAD RUFA'I NALELE*
*PAGE* *30*~*35*
*Wannan shafin sadaukarwa ne gare ku matan aure masu ire-iren wannan matsalolin, Allah ya k'ara muku hak'uri, Allah ya kare ku daga fad'awa halaka, Allah ya sa mazajen ku su gane gaskiya, su kula da ku kamar yanda Kuke da buk'ata, Allah ya kare mu daga sharin shaid'an gaba ki d'ayan mu, Allah ya kare mu daga fad'awa halaka irin ta HAFSAT, Ameen*
*'Yan Mata masu fama da irin matsalar AZEEZA, Allah ya sa mahaifin ku su gane gaskiya, Allah ya kare ku daga fad'awa halaka da sharin shaid'an, Allah ya baku mazaje na gari, Ameen*
*Wani* irin rik'o yayi mata Wanda baza ta iya k'wace kanta ba, yayi dubara ya k'wace kwalban, sannan ya tura ta da k'arfi ta fad'i k'asa, cikin zafi yace"Kina hauka ne wato ni zaki buga ma ko? To ni nafi k'arfin ki, Kuma aure ne bazan aure ki ba ni 'yar gidan mutunci Zan aura yarinya mai tarbiyya"
Cikin zafi da d'aga murya tace" Ni zaka YAUDARA SA'EED? Kar ka manta Kai ne sanadiyar lalacewa na Kai ne ka fara b'ata min rayuwa Kuma yanzu shine zaka yaudare ni to wallahi bazan yarda ba"
Yace"to sai kiyi abin da zakiyi, aure ne dai bazan aure ki ba, Kuma ai ba ni na lalata ki ba da had'in kanki akayi komai ba raping din ki nayi ba, Kuma duk abin da kikeyi Ina sane nasan ba da ni kad'ai kike huld'a ba kina da wasu samareen ko a tunanin ki ban sani bane?"
Zuciyar ta na wani irin zafi tace" SA'EED wannan wani irin YAUDARA DA CIN AMANA ne? Ashe dama can ba so na kake ba to wallahi sai na koya ma hankali, sai na tozarta ka cikin jama'a, sai nasa duniya tayi tirr da halin ka, idan Kai YAUDARA DA CIN AMANA kake ma 'yan mata to wallahi ni baza ka yaudare ni ba, nafi k'arfin ka Kuma kayi k'adan in gyale ka haka, I will get my revenge, sai na d'au fansa" fuuu ta bar parlour'n tare da shiga mota ta ja a guje, zuciyar ta na tafasa wato ita SA'EED zai YAUDARA yaci AMANAR ta baza ta tab'a yarda ba, sai yayi nadamar sanin ta a rayuwa.
SA'EED ko bai kawo komai a ran shi ba yasan dai barazana take mai shi Kuma ba zai ji tsoron ta ba, ko takan maganar ta bai bi ba ya cigaba da harkar gaban shi.
A yau ne ABRAR zai dawo sai shirin tarban shi matan shi keyi, Around 8:00pm ya iso garin Abuja, direct gurin HAFSAT ya sauka sai da yayi wanka yaci abinci sannan ya nufa side d'in JAWAHIR.
Tana kwance kan kujera duk ta k'osa ta ga ABRAR, kamar a mafarki taji anyi mata wani irin kyakyawar runguma, a d'an tsorace ta d'ago kan ta, murmushi yayi yace"miss you wifey, kinji tsoro Koh?"
Cikin wasa ta ture shi tace"ai dole in tsorata banji shigowan ka ba fa"
Murmushi yayi tare da Kai bakin shi kan nata ya fara kissing, da k'yar ta iya k'wace kan ta tace"ai ka tsaya mu gaisa ko?"
Cikin dariya yace" to wannan ma ai gaisuwa ne"
K'ara rungume ta yayi, Nan yaji kamar ya d'an takura ja yayi da baya Yana mamakin meye ya shiga tsakanin su, shafa cikin ta yayi Yana mamaki yace"ke meye ne wannan"
Dariya tayi ganin yanda yayi maganar sai tace"baby'n ka ne"
A rud'e da mamaki yace" kina nufin ciki kike da shi kuma har ya girma ban sani ba?"
Dariya tayi tare da sanar da shi komai ai ko ba k'aramin farin ciki marar missaltuwa yayi ba, ganin zai Zama Baba, Nan yayi ta ma Allah godiya yana mata albarka Dan ta gama ma komai a rayuwa, kamar kar ya tafi ya bar ta a wannan Daren amma ba yanda zaiyi dole yaje gurin HAFSAT Dan Yana son nuna a dalci a tsakanin su.
Da k'yar yayi kwanaki biyu gurin HAFSAT ya dawo gurin JAWAHIR cikin murna har sai da HAFSAT ta gane, Kuma ya sanar da ita cewa JAWAHIR nada ciki, habawa ba k'aramin zafi taji ba tayi kishi sosai haka tayi ta kukan bak'in ciki.
ABRAR ya sanar da iyayen shi cewa ya dawo Nigeria kenan ba zai k'ara yin tafiye-tafiyen Nan ba gaba d'aya aikin shi ya dawo Nigeria, ai kuwa sunyi farin ciki sosai, lokacin da SA'EED yaji yayi bak'in ciki dan ba haka ya so ba, Dan ya katse musu Jin dad'in su ne shi da HAFSAT.
Haka rayuwa yaci gaba da tafiya, yayin da ABRAR yake kula da JAWAHIR sosai saboda cikin ta yanzu haka cikin watan shi takwas, gashi cikin na bata wahala sosai.
B'angaren HAFSAT da SA'EED kuwa basu fasa aikata masha'a ba Dan har yanzu suna had'uwa a hotel su hole, Amma da yake ABRAR ba Mai kula bane duk bai tab'a ganewa ba, Dan a yanzu haka ma aiki yake sosai Kuma ba Wai ya cika kula da matan shi bane, Yana dai kula da JAWAHIR saboda cikin shi da take d'auke da shi.
A hankali a hankali abubuwa ya fara canza ma ABRAR dan yanzu Yana k'okari gurin ganin ya gyara tsakanin shi da matan shi, dan Yana k'okari gurin basu hak'okin su da ya rataya akan shi, ganin Yana canzawa ne yasa HAFSAT Jin nadamar abin da take aikatawa, gaskiya lokaci yayi da zata daina aikata masha'a, ta dawo hanya mai kyau, ta zauna da mijin ta da kishiyar ta cikin k'aunar juna, ita ma ta samu ciki ta haifa nata yaran, sosai take son ganin wannan rayuwar da zata fara, a hankali ta fara guje ma SA'EED, ko yazo gidan bata kula shi, bata Kuma d'aukar wayan shi, ta yanke zuwa hotel, shi ko k'aramin tashin hankali ya shiga ba sai tambayar ta yake ko lafiya, Nan take sanar da shi gaskiya su daina wannan abin da sukeyi ita dai tayi nadama, ya rabu da ita kawai shima yaje yayi aure ya daina aikata haka, yayi mamakin maganar ta, Kuma shi dai Yana Jin dad'in harka da ita baya son su rabu.
*Mene ne labarin AZEEZA?*
Bayan barin ta gidan SA'EED gidan su ta nufa, haka tayi kwana biyu tana kuka cikin k'unci, tayi ALK'AWARI baza ta tab'a barin SA'EED ba, lokacin da Daddy yayi Mata magana akan auren cewa tayi ta fasa bazata yi ba domin shine silar duk wani abu da ya same ta, haka yayi ta fad'a yace dole tayi aure, Nan yasa mata ranar aure da 'dan aminin shi, biki saura sati d'aya ta gudu ta bar gidan su inda ta tare can wani gidan 'dan iska suna aikata masha'a (Wa'izzubila), haka dole aka fasa auren, iyayen ta na cikin bak'in cikin ta.
AZEEZA ba wai rayuwar farin ciki takeyi ba burin ta kawai taga tayi maganin *YAUDARA DA CIN AMANA* irin na SA'EED, ranar ta raka wani saurayin ta hotel kawai sai ta ga SA'EED da HAFSAT, ba k'aramin mamaki tayi ba Dan tasan HAFSAT tunda lokacin bikin ta ma taje, Nan ta fara bincike akan su, meye ne ke had'a su a hotel, a haka tana bincike har ta gano abin da suke aikatawa, ba k'aramin farin ciki tayi ba domin tsuntsu daga sama gasashe ta samu, Wato SA'EED na yaudaran aminin shi ABRAR ta hanyar yin aikata masha'a da matar shi HAFSAT, ai ko sai ta tona mai asiri.
AZEEZA ke Kiran ABRAR da different sim card tana gaya mai cewa ya bincika matar shi HAFSAT da aminin shi SA'EED, tun yana ganin maganar shirme har ya fara yarda domin ya fara lura da wasu alamomi hakan yasa hankalin shi ya tashi sosai, amma bai tabattar da zargin shi ba yafi so ya kama su red handed, gashi AZEEZA tak'i bayana mai kan ta.
HAFSAT abin duniya yayi mata yawa domin tana son rabuwa da SA'EED amma yayi ta damun ta da Kira.
Wata rana
HAFSAT na kwance kan bed sai tunanin duniya takeyi, ga wani irin nadama da takeji, SA'EED ne ya Kira ta a waya yana rok'on ta tayi hak'uri ta zo su had'u a hotel, da farko tak'i yarda sai Kuma ta shirya zata je ba Dan yin komai ba sai dan tace ya rabu da ita, d'aukar wayan ta tayi tana ta kiran ABRAR amma bai d'auka ba Dan a lokacin yana cikin meeting ne, can take yanke shawaran yin mai text message, sannan ta nufa hotel d'in.
Tana zuwa hotel d'in ta nufa bedroom d'in da SA'EED yake, Yana ganin ta ya mik'e tsaye cikin farin ciki zai rungume ta, da sauri ta dakatar da shi, tace"Wai meye kake nufi ne? Na gaya maka gaskiya ni nayi nadamar abin da muke aikatawa yanzu ma na zo ne in sanar da Kai Dan Allah Ina rok'on ka, ka fita daga rayuwa ta, Dan Allah ka barni in zauna da miji na kamar yanda muke a da please ina rok'on ka"
Jikin shi a sanyaye yace"na so ace kin yarda mun cigaba da harka amma tunda kince haka ni na hak'ura Zan bar ki kici gaba da Rayuwar ki kamar yanda kike so"
Taji dad'in maganar shi, dan haka tace zata tafi sai yace A'a ta bari taci abinci, haka akayi kuwa sai da taci abinci sannan tayi sha'awan yin wanka tunda garin ana zafi gashi gurin k'arfe 2:00pm ne, Nan yace taje tayi wanka.
Toilet ta shiga tayi wanka sannan ta fito d'aure da towel, tana fitowa shima ya shiga Dan yayi wankan.
AZEEZA ce ta shigo bedroom d'in cikin tsananin zafi da kishi da yake k'ofar a bud'e yake, cikin mamaki HAFSAT ta kalle ta domin ta tuno da fuskar ta ai wannan budurwan SA'EED ne, cikin mamaki tace" baiwar Allah lafiya Kika shigo babu sallama?"
Cikin zafi da kishi mai tsananin gaske ta nufa HAFSAT gadan-gadan ta tsaya a gaban ta tare da zaro wani wuk'a sai shek'i yakeyi.
Cikin razana HAFSAT ta zaro ido kafin tayi magana AZEEZA ta dage iya k'arfin ta da rashin imani ta caka mata wuk'an a cikin ta, tsoro ne ya kamata ta da gudu ta bar bedroom d'in ta nufa Wanda ke facing d'in shi dan dama Nan ta kama, tana shiga ta kule cikin tsoro da razana ta Kira police ta fad'a musu suyi sauri su zo hotel wani ya kashe wata Mata, Nan tayi musu kwatance sannan jikin ta na rawa ta Kira ABRAR.
Cikin rawar murya tace"ka zo yanzu abin da nake gaya ma ne ga abokin ka Nan ya kashe maka Mata!"
Dum gaban shi ya fad'i jikin shi ya d'auki rawa lokaci d'aya zufa ya wanke mai fuska,!
Nan ta fad'a mai sunan hotel d'in da number'n room d'in da sauri sannan ta fita ta bar hotel d'in, da gudu ta fad'a, mota.
Lokacin da AZEEZA ta caka mata wuk'an wani irin ihu ta saki mai k'ara, ta fad'i k'asa, cikin rud'ewa SA'EED dake toilet ya fito, ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba ganin HAFSAT kwance cikin jini ga wuk'a a cikin ta, da sauri ya k'arasa gurin Yana cewa"HAFSAT me ya faru kiyi min magana waya caka Miki wuk'a, Wayyo Allah na ki tashi HAFSAT kiyi min magana"
Innalillahi wa'ina illaihir-raji'un, dai-dai lokacin ne Allah yayi ma HAFSAT rasuwa,!
Zuwan ABRAR yayi dai-dai da zuwan police a tare suka shiga hotel d'in, ya riga su gaba Yana zuwa ya nufa k'ofar bedroom d'in, a dai-dai lokacin ne cikin rud'ewa da razana SA'EED ya cire mata wuk'an a cikin ta.
D'agowan da zaiyi sukayi two eyes da aminin shi ABRAR da yayi mutuwar tsaye, police na zuwa suka ga abin da ya faru, wani police ne ya nufa SA'EED tare da cewa"You are under arrest" ya sa mai hand cuff.
Sakin Baki SA'EED yayi cikin mamaki yace"Bani na kashe ta ba"
Wani irin durk'usawa k'asa ABRAR yayi tare da sakin kuka mai k'arfi, Yana sallati.
AZEEZA tana cikin mota tana tunanin abin da ta aikata Wanda ko a mafarki bata yi tunanin yin kisa ba, jikin ta rawa yakeyi sosai, ba tare da ta sani ba wata k'atowar mota tabi ta kan ta.
Da gudu mutane suka nufa motar ta Dan taimakon ta, sai dai ina ko shurawa batayi ba ta rasu.
Innalillahi wa'ina illaihir-raji'un
*Innalillahi wa'ina illaihir-raji'un, mutuwar HAFSAT ta girgiza ni, na tausaya mata sosai na Kuma tausaya ma ABRAR*
*TAKU CE UMMU BASHEER*
[07/01 1:54 pm] Sis Ummu Bashir:
*YAUDARA DA CIN AMANA*